← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 100

Sashe 59

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      Mintuna 15 a tsakani aka bud’e kofar d’akin , cikin Sauri Abla ta d’ago da kanta , shima ya canza shiga da alama wanka yayi . A bakin ‘kofa ya tsaya tare da folding hannun sa waje d’aya yana binta da wani irin kallo da shi kad’ai yasan ma’anar sa . Cikin Sauri Abla ta sunkuyar da kanta ganin irin kallan da yake binta dashi. Cikin takunsa na kullum ya soma takawa cikin falour zuwa kan sofa d’in d’akin, bai ce komai ba har lokacin da ya zauna kusan tsawan mintuna biyu , Abla da take wasa da ‘yan ya tsunta a hankali ta furta “ Ina kwana ?” Kamar me koyar magana , shiru yayi mata batare da ya amsa ba a karo na biyu Abla ta ‘kara furta “ina kwana ?”, hannun sa d’aya ya mi’ka mata alamar tazo batare da ya furta ko uffan ba, tunanin yadda zatajen take ganin yadda ya mi’ka mata hannunsa , bata motsa daga inda take ba har lokacin sai d’an d’ago da fuskarta da tayi kad’an kamar me jiran ‘karin bayani “ come here “ ya fad’a ahankali yana ‘kara mi’ko mata hannun sa , ganin face d’insa kamar ba da wasa ba yasa ta taso jiki a sanyaye zuwa inda yake duk da bata ‘karasa ba ta tsaya, tunda ta soma tafiya yake kallan movement d’in tafiyar ta ganin ta tsaye ne yasa ya d’ago da kansa “ zafi?” Ya furta a hankali , kanta Abla ta jinjina masa itama Batare da tace komai ba . Mi’kewa yayi zuwa inda take tare da kawa hannunta “ it’s okay , zai dai na kinji ? Kanta Abla ta jinjina tana pouting lips d’inta kad’an , ‘karamun murmushi ya saki tare da d’aukar ta kamar Baby ya fita daga cikin d’akin , “ Ban san Yaushe kika koyi shagwa’ba da yawa ba haka “ cikin Sauri Abla ta mayar da bakinta , har zuwa inda yake san suje, a hankali ya ajjeta akan kujerar dinning , ga abinci kala kala dake kai , d’an zaro idanuwanta Abla tayi kad’an ganin yadda aka çıka kan dinning d’in da abincin cika “ what do you want to eat ?”, ‘kamshin cow leg da taji duk da bata da grantee d’in shine amma haka ta furta “ cow leg”, bai ce komai ba ya bud’e Warmer d’in tare da saving d’inta cikin wani unique bowl bayan had’ad’d’an breakfast d’in da yayi serving , a kujerar kusa da ita ya zauna kafin ya kama hannunta yana mayar da ita kan cinyarsa , cow leg d’in ya d’ebo zai kai bakinta Abla ta d’an sunkuyar da kanta ‘kasa jin yadda abunda ya zo mata a banbara kwai “ öpen your mouth “ ba musu Abla ta bud’e bakin ya saka mata , sosai taji dad’in sa shiyasa da ya ‘kara saka mata ta sha abunta , kamar wata Baby haka yayi feeding har lokacin tana kancinyarsa ,sai da ya tabbatar ta ‘koshi tukunna ya rabu da ita. Hannu yayi mata alamar saura turn d‘inşa , zatayi masa musu ya girgixa mata kai , babu yadda ta iya haka ta bashi a bakin idanuwansa gabaki d’aya akan ta . Suna gamawa Abla ta mi’ke a hankali da har azumi ciwan ta bai warke ba , kayan kan dinning d’in ta so kwashewa ya ri’ke hannun ta “Don’t touch anything , let’s go some where “ ya fad’a yana ri’ke mata hannu zuwa wani ‘kofa , cikin wajan sosai yayi kyar sabida babu komai a cikin sai wasu kujeru masu laushi kamar na shan iska daga inda suke suna iya hango abunda yake waje . Akan kujerar suka zauna Abla na cinyarsa ya zagaye Hannayensa guda biya akan stomach d’inta , shiru gabaki d’ayan su sukai kamar babu mai magana a cikin su kafin ta tsinkayi muryarsa cikin dodon kunnanta “ What’s your Biggest dream of yours ?” Kai tsaye Abla ta furta “ My parent, inaso nagansu ko sau d’aya ne “ d’an shiri Big Boss yayi ganin voice d’inta yana ‘ko’karin canzawa “ Şai kuma me? “ Abla kamar mai tunani  sai kuma ta furta “ Inaso na taimaki maraya Sabida nima nasan wahalar da suke sha “  and ? Cewar Big Boss , turo bakinta Abla tayi kad’an kafin ta furta “ Inaso nayi karatun Medicine “, a hankali ba tare da ya bari taji ba ya furta “ Dream “ gabaki d’aya kansa ya d’ago a bayanta yana lumshe “ Ba kyacin abinci sosai , your tummy is so flat ko sai nayi ajiya xai tashi?” Abla bata fahimci maganar saba shiysa tayi shiru, ‘kara kwanciya yayi a bayanta suna kallan yanayin gari daga inda suke a zaune . 

      ✨✨✨✨

  ‘Karfe uku da mintuna Wasu manyan motoci suka danno kai gidan His Excellency gabaki d’aya yan sandan gıdan sunsan su wanene a ciki, a Daidai wani part da ya’ke kusa da part d’in Didii motocin nan sukai packing , ana ‘ko’karin bud’e motar su Didi suka fito daga cikin gidan fuskokinsu d’auke da fara’a . Gabaki d’aya yan gidan sun fito hardasu Harry , Nanni ce Kawai babu sai su Little da His Excellency da su Bobo da basusan abunda yake faruwa ba . Fanan ma tana kusa da Mamy cikin shigar doguwar rigar a baya. ‘Kafar d’aya daga cikin motocin aka bud’e , wani kyakkyawan guy ne chocolate colour ya fito daga cikin motar  sanye da ash suit sai sumar gashin kansa da itama ta sha gyara sosai , ba laifi kyakkyawa ne guy d’in shima, d’ayan side d’in kafar wata macece ta fito kafin gangan jikinta shima ya bayyana, kyakkyawar yarinyace da taci a donta cikin material fuskarta d’auke da lallausan murmushi akai, batace komai ba sai ‘kofar baya da ta saka hannu fa bud’e , wani hannu ne da yaji kwala kwala akai ya soma fitowa , Ba kowa bace face Hajiyar America, uwa ga gabaki d’aya familyn Mai Dala, mace mai kamar zama ga dattako dukda rashin lapiyar da take fama dashi, tana fitowa gabaki d’aya Suka ‘kara nutsuwa san Hajiyar America bata san wargi idanuwanta gabaki d’aya cikin wani ba’kin glass yake bata ce komai ba ta soma taku budurwar macen na binta a baya ga wata mata da ashekaru bazata wuce 45 ba itama da ta fito daga cikin motar. Hajiya America kai tsaye kusa sa Didi ta karasa tana rungumarta “ Amincin Allah ya tabbata a gare ki yar uwa “ murmushi Diidi ta saki tana furta “ kema haka yar uwa”, yan gidan suna ‘ko’karin magana wata mota ta shigo cikin gidan ba’ki, a Daidai lokacin da Fanan ta shiga cikin gidan Adaidai lokacin sukai parking a kusa da motocin su Hajiyar madina , ‘kofar motar da aka bud’e ne gabaki d’aya ya sa yan gidan suka mayar da kallansu zuwa wajan. Daga d’ayan side d’in aka bud’e ’kofar motar aka fito ba kowa bane face Baby da Eshaal da fuskarsu ke d’auke da fara’a kwance akan fuskokinsu. ‘Dan dafe kirji Momy Baby tayi kafun ta furta “ Me kuke yi anan ? “ cikin d’an d’aga murya…

IBTISSAM
      ( A heart touching story of love and destiny)

Story & written 
      By
Mss Lee   

                    09134652921

    TALLA!! TALLA!!! TALLAH !!!!!!!

SHIN KUNSAN WACECE HAJIYA NUSAIBA BR~B ZURU ?❤️

HAJIYA ~ NUSAIBA DR~B ZURU

MAMALAKIYAR ZIMH ISLAMIC AND MEDICINE DAKE RINGH ROAD A KANO NIGERIA
Tazo muku da ingantattu ko sahihan magungunan mata masu inganci, ba’anan kad’ai ta tsaya ba har da na cututtuka da Turarukan wuta , Humra masu shegen ‘kaushi . Abun Alfaharin kuma tana bada sarı cikin sau’ki, sannan kuma suna aikawa duk inda mutum yake afad’in duniyar nan. 

Duk wacce ta siya magungunan Hajiya Nusaiba Dr B zuru, taga be yi mata aiki ba tazo za’a dawo miki da kudin ki . 

KA’DAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKE SIYAR WA

1️⃣ Hadin amarya
2️⃣Hadin mai jego
3️⃣Hadin sabon budurchi
4️⃣Hadin Kaza Yar’Suddan
5️⃣zuma -Tsumi- Tabaje da sauransu
6️⃣Turaren Sandal ruuu& flastic Sandal
7️⃣ Hadin Hawwi domin inganta zafafiyar kauna
8️⃣Hadin bagadad,kahlij,kajiji,gafgaf dasauransu
9️⃣Hadin humra soyaya dole ta matan aure da normal humra

DON SAMUN ‘kARIN BAYANI KU NE META TA WANNAN NUMBER KAMAR HAKA : 
    08133647913 

   KANO NIGERIA 

LOCATION: RING ROAD BAYAN GİDAN MAN NAZARGO.

       SIYAN NAGARI MAIDA KU’DI GIDA

PAID BOOK

BOOK 2 
         S_____ 20

                 NOT EDITED 

    Da sauri Baby da Eshaal da fitowar ta Kenan daga motar ta jiyo saitin inda taji muryar Momy, suma yan gidan gabaki d’aya Ita suka kalla lokaci d’aya. Ganin yadda kowa yake kallanta ne yasa ta d’an yi murmushi mai kama da na ya’ke cikin rarrabewar murya ta furta “ Na manta da zuwan su ne “, cewar ta tana ‘kara sakar wa mutanan gidan murmushin dole . Hajiyar America bata ce mata komai ba suka nufi cikin part d’in ita dasu Didi sai kuma sauran uncles d’in da suka fito. Mamy da Aunty karima ne suka tsaya lokacin da su Baby suke fito da kayansu, Momyn su ma na gefe sai faman sakin murmushin dole take gudun kar a fahimci yanayin da take ciki. 

    Amma ce ta fito daga cikin motar itama , hannunta d’aya d’auke da jakar su Baby, tazo zata tsugunna Mamy tayi saurin yi’ke mata hannu “ Haba ke kuwa  gaisuwa ba taki bace ai , nasan yanxu kun gaji, ku shigo daga ciki “ Momy ji tayi kamar ta sha’ke Mamy jin abunda tace musamman yadda taga ta tar’ o yar aikinta hannu Biyu, kallan Baby da Eshaal dake gaisheta sukai fuskarta d’auke da fara’a “ Yan mata na ku shigo mana ,” ta fad’a tana musu alamar suzo kusa da ita , daga haka suka shiga cikin part d’in Hajiya karima kuma suka shiga cikin falourn tare da su Amma, duk yadda Momy taso take’be da Amma hakan bai faruwa ba sabida suna shiga falourn har Mamy ta nuna musu masaukin da zasu zauna , ga Baby da Eshaal da har yanzu take mamakin zuwan da sukai yau , gabaki d’aya ranta a ‘bace ta wuce masaukinta ganin yadda Hajiya karima ta bawa Amma masauki kamar ba yar aiki ba . 
Chapter 59 · 0% Book details