← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 100

Sashe 27

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

    Tana shiga kitchen ta soma tunanin abunda zata dafa so simple ganin lokaci na tafiya , gashi yamma tayi , potatoes ta d’auka Daidai Wanda ta san zai isheta ta soma filling d’insa , cikin sauri jennifer ta shigo kitchen d’in “ Mah ki barshi zanyi aikin” girgixa mata kai Abla tayi “ No Jenny ki barshi , ba abu bane me wahala karki damu kanki “,  amma akwai abunda kike bu’kata ne ?” Cewar jenny, shiri Abla tayi na ‘yan sakanni kafun ta furta “ yes jenny alayyahu nake bu’kata idan za’a sameshi , da Sauri Jenny ta furta “okay ma tana barin kitchen d’in, cikin ‘kan’kanin lokaci Abla ta gama filling potatoes d’innan ga su onions gabaki d’aya data yanka, duk abunda take bu’kata ya fito dashi musamman kifin da ta gyara . Jenny bata dad’ewa ta dawo da zogalan. Cikin ‘kan’kanin lokaci Abla ta fara girkin ta cike da kwarewa , daddad’an ‘kamshin abincin na tashi duk da bawani abu take yi me wahala ba , ko mintuna 30 batayi ba ta kammala had’a had’ad’d’an Irish potatoe porridge d’inta da yaji alayyahu da kifi , cikin wani unique medium warmer ta zubashi kafin ta d’ebo fruits shima da kanta ta had’a masa lapiyayyan smoothie , cikin d’an ’kamar silver din abu kuma ta saka mashi ice block kad’an, sai data tabbatar ta gama had’a tray d’in ta dauka da kanta Jenny zata karba ta hana ta tayi fitowar ta , tana zuwa ‘kofar d’akin shi kuma sai ta kasa shiga , Tuna’nın yadda zatayi masa da abincin ta fara har ta d’an tsugunna zata ajje sai taga rashin dacewar hakan , addua ta fara Allah yasa baya cikin d’akin, sannan ta bud’e a hankali kamar me sand’a, daga inda take bata hango kowa ba shiyasa ta shiga cikin sand’a, ganin baya cikin ne yasa tayi ajiyar zuciya tayi saurin ‘karasawa kan center d’in datasan akai zai iya cin abincin , tana ajjewa ta mi’ke zata juya a Daidai lokacin da shikuma ya bud’e kofa, da wani irin mugun speed Abla ta juya masa baya Sabida batayi tsammanin ganin saba ,  kamshin turaransa ne ya cika mata hanci, cikin sauri zatayi hanyar fita ya ri’ko mata ‘kugu “ ina zaki?” Motsi ta soma yi da bakin ta tana sanyin magana , da ‘kyar ta iya furta “ zanje d’aki ne ”, hannun ta ya ri’ke har kan sofa d’in d’akin, shigar ‘kananan kaya blue d’in da yayi ba ‘karamun yi masa kyau yayi ba musamman yadda kullum gashin kansa yake ‘kyalli sabida gyaran da ya Samu , da hannu ya nuna mata abincin da ta ajje, ba musu taje ta d’auko masa , zata kuma juyawa ya furta “ Haka aka koya miki ? Idan zaki bawa miji abinci?” Tsuke fuskarta Abla tayi ta’ki tanka masa , tana gani yana ‘ko’karin mi’kewa ta ‘karaso tare da serving d’insa abincin da tunda ta bud’e ya d’an lumshe idanuwansa , “ Okay now a bani “ Abla batasan lokacin da ta zuba masa wani kallo ba tare da d’auke kanta zata gudu “ idan kika ‘kara one step , you will surely regret it , bakyajin magana ko ?dont let me loose my patience over you “, kamar zatayi kuka ta furta “ zan….zan ga su Yaya Little ne..” kallan da ya je fa mata ne yasa ta had’iye ragowar maganar tata. Dan dole ta soma bashi abincin a baki, sosai ya ci abincin dan ba’karamun dad’i yayi masa “ I like the food “, cewar Big Boss duk da ba sosai yayi magana ba amma sarai taji abunda yace shiyasa ta d’an tsuke fuskarta, “ wad’an da kike neman basanan sai ki bari idan sun dawo sai ki tattara ki kowa Wajan nasu “, da Sauri Abla ta kalle sa ganin yadda ya mayar da kallansa zuwa phone d’insa . Bata san dalili ba sai jin kwalla tayi ta tarar mata a idanuwa , mi’kewa tayi zatabar d’akin ya dawo da ita tare da d’orata kan cin yar sa “ Rigimar ki tayi yawa , ni da kaiko wa laifin banyi kuka ba shine ke kike sanyi ,” d’an sunkuyar da kanta Abla tayi ba tare da ta kallesa ba , gabaki d’aya hannayensa ya saka yayi hugging flat tummy d’inta tare da d’ora kanta akan kafad’unsa , shafar jikin yayi kad’an kafun ya furta “ Anya mutum zai iya rayuwa a flat tummy ?” Abla bata gane me yake nufi ba shiyasa ta soma mutsu mutsu zata kwace ya ‘kara Hugging d’inta “ it’s okay ! Just cool down, fushin ya isa haka, I want to feel your warm, stay still “.

********
A part d’insu Hajiya sa’adatu kuwa , iya sha’ka sun sha’ka abunda akayi wa ‘ya’yan su , babu abunda ya fi tsaya musu arai kamar yanke gashin ‘ya’yansu da akai ga uban aikin wahala da sukayi kamar sun samu bayi , Hajiya karima tun da ta shigo part d’in ta kasa zaune ta kasa tsaye gabaki d’aya ta kasa zama “ Hajiya sa’adatu dole mu d’auki mummunan mataki, idan ba Haka ba yaran nan sai ya mulke mu gabaki d’aya dashi da waccan shegiyar yarinyar da bazan ta’ba bari ta samu kwanciyar hankali ba , lalle basusan wacece Hajiya karima ba , sun ta’bo dala ba gammo gabaki d’aya sai nayi maganin su , harda munafikin kubansu da ya bi bayan wannan abun”.tsuke fuska Hajiya sa’adatu tayi kamar wacce take cikin tsananin ‘bacin rai amma a cikin zuciyar ta kuwa wani irin shegen murmushi take “ kiyi duk abunda zakiyi, zan zuba miki idanuwane kiyi mun komai kafun na mayar da aikina kanki dan bana yadda da mutum biyu, banza shashasha , kar nake kallan ki “, amma a fili sai wani dogon tsaki taja , “ Hmmm Hajiya karima ki bari , dan sai na d’auki mugun mataki akan yarinyar can sai ta san da wa take ja , yanxu ba gobe ba zansa a fara yi mata aiki dan ba makawa sai na kawar da ita hankalina zai kwanta , shegen munafukin babansu ma sai nayi duk hanyar da zanbi naga bai amince da wannan Auran ba “ d’an ajiyar zuciya Hajira karima ta saki cikin zuciyar ta kuwa wani dad’i ne ya kamata gani take kamar dama ce ta samu babba da sa’adatu zatayi mata aiki tana kammala wa kuma zata saka ‘ya’yanta su auri Big Boss bayan sun saka Abla ta koma ‘kas’kantacciyar baiwa, kowa da kalar muguntar da yake ‘kullawa d’an uwanshi , amma a zahiri mutum sai yayi Tuna’nın kansu d’aya sabida yadda kullum suke a tare .
Chapter 27 · 0% Book details