← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 100

Sashe 83

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*************
Kwalbace a hannun Harry sai faman kwankwad’awa cikinta take yi , tana yi tana surutai barkatai “ wai ni ce yau zan samu abu na rasa Ni Harry ? Toh wallahi hakan bazai ta’ba faruwa va “ ina sanka , ina sanka , ina sanka , kuma dole sai na aure ka ko zanyi yawo tsirara ne , sai ka zama miji na , ke kuma shegiyar yarinyar nan sai na la’antaki, sai na la’antaki kamar yadda kike ‘ko’karin rabani da farin ciki na , sai na tarwatsa rayuwar ki , sai na Mayar dake ‘kas’kantacciyar mutum “,ta fad’a da ‘karfi tana wurgi da kwalbar hannun ta , lokaci d’aya kwalbar ta fashe . Wani kwalbar ta ‘kara bud’e tana kwankwad’ar abunda yake ciki, sai da tayi takilll tukunna ta zube a ‘kasan tana munshari.

***********

Tana idar da Sallah M.Sarah ta kawo mata wani abu cikin medium size d’in designer me shegen kyau sai spoon da yake kan ‘karamin tray d’in “ Madam gashi Hajiya Mamy tace na kawo miki “ murmushi Abla ta saki tana amsar tray d’in “ Nagode sosai “, cewar Abla , itama murmushi M.Sarah ta saki kafun ta bar d’akin, Abla bata bud’e abunda aka kawo mata ba a acewarta şai anjima sabida kar bakinta yayi d’aci, tana ‘ko’karin zama akan gadon wayarta ta soma haske , cikin Sauri ta d’auki wayar “ Sun shine “, shine sunan da ya fito a screen d’in wayar me had’e da luv the kiss a wajan.

    ‘Dan zama Abla tayi a gefen gado ganin kamar vidoe called ne , kamar me tsoran d’aga wa ta amsa kiran wayar ,tare da kulle face d’inta da hannu d’aya , sautin muryar sane ya shigar mata Dodan kunne “ Remove your hand “, hannun Abla ta zare tana d’an d’ago da face d’inta zuwa jikin cameran , yana zaune kan wata farar kujera mai zaman mutum d’aya da alama yayi crossing legs d’in sa sabida irin zaman da yayi “ Sunshine mai kika ci ? Naga kamar kin ‘kara kumatu “, shafa kumatun Abla tayi kafun ta turo masa bakinta “ Ni dai ban ‘kara kumatu ba “, sosai Big Boss yake kallanta kafun ya furta “ ‘kin ‘karafa, har nauyi ma kin ‘kara ki bari şai mu fara training , har kin fara tinbi fa tun banbaki Baby ba “, kallan cikin Abla tayi tana turo masa bakinta “ Ni bani da timbi kai ne maishi “, gira d’aya Big Boss ya d’aga mata “ Really ?” Itama Ablan gira d’aya ta d’aga masa tana kashe masa ido d’aya , yanxu kam murmushi Big Boss ya saki saman la’b’ban sa , “ tell me Menene sirrin ? You look so chubby, Anya babu Baby na a cikin ki kuwa ?” ‘Bata fuska Abla tayi “ Ni babu komai a ciki na kawai ..” sai kuma tayi shiri “ Kawai me ?” Cewar Big Boss , ka fad’a ta ma’kale kamar Baby kafin ta furta “ Uhm’Uhm ni bazan fad’a ba “, d’an lumshe ido Big Boss yayi a kanta yana ‘kara bud’ewa “ Sunshine ki shirya by 8 anjima and don’t asked me anything “, batasan musu dashi shiyasa ta jinjina masa kai, da hannu ya nuna d’an kwalin kanta “ remove it “, hannu Abla ta saka tana zare d’an kwali, lokaci d’aya lallausan gashin kanta ya zubo mata , d’an ‘karamun ajiyar zuciya Big Boss ya saki yadda bazata ji shiba, ido ya kashe mata yana nuna shirt d’in jikinsa “ ki cire rigankiba kwai zafi fa”, d’an sakin baki Abla tayi jin abunda nace “Kinji “ ya ‘kara maimaita wa , fiki fiki Abla tayi masa da ido dan ko bra babu a cikin rigar tata “ Babu zafi fa sanyi nake ji “, shima cikin sanyin murya kamar yadda tayi ya furta “ I will show you something ne fa”.  Yanzu ma d’an zare masa ido Abla tayi tana ‘kasa da kanta “ You can’t do it right ?” Kanta Abla ta girgiza masa alamar ah’ah , Sosai yaga kunya a fuskar ta shima Sabida yaga rigimar tane ya fad’e hakan da a dane da ta kira sa d’an iska sa’banin yanzu “ Okay daman wifey tace zata…” wani irin d’ago da fuskarta da Abla tayi sai da yayi shiru ya kasa ‘karasa abunda zai ce , wani hutar Kishin sa ne yake hangowa a cikin idanuwanta , tun ba yau ba yasan tana kishi, ganin yadda ta ‘bata rai ne yasa ya kalleta sosai “ Are you really jealous of me ?” Idan Wifey ta zo fa ?” Cikin tsuke baki Abla ta furta “ Sai na bubburma mata wu’ka a ciki sannan na bawa Simba na manta ya cinye ,” yanxu kam murmushi da Big Boss yayi mai sauti yayi ganin ta ‘kara ‘bata fuska ne yayi shiru , a shagwa’be Abla ta furta “ Ni babu ruwa na da kai , na fasa nuna makan “ ta fad’a itama cikin rigima tare da nuna masa daidai saitin breast d’inta da ya le’ko kafun yayi magana difff Abla ta kashe kiran tana dafe ‘kirjinta da ya soma d’aga wa ita ba da wani abun tayi ba dan tara mane kawai tayi amma kallan data ga ya mata ne yasa tayi saurin kashe kiran , bata gama Tuna’nın da take ba kiran sa ya ‘kara shigowa shiyasa ta kasa d’aukar kiran , ‘karamun message ne ya shigo wayan nata , tana bud’ewa taga “ I love you Sunshine ..” murmushin jin dad’i Abla ta saki tana ajje wayar , abun da M.Sarah ta bata ta d’auka tana bud’ewa yadda ‘kamshin kwakwa da dabino ya Dakar mata hancı ne yasa ta yi saurin d’ankwan spoon d’aya ta kai baki , batasan Menene ba amma abun yayi mata dad’i sosai , wani spoon d’in ta ‘kara kaiwa bakinta , ganin yadda abun yake da dad’i sosai ne yasa ba shiri ta d’an samu waje ta zauna tana shan kayanta , ko 5 spoon batayi ba aka d’anyi knocking ‘kofar , a Tuna’nın ta M.Sarah ce ko su Eshaal shiyasa ta bud’e d’akin tana fad’in “ come in “ , tana zama kan gadon ta d’auki abunta zata kai baki taji daddad’an ’kamshin turaransa a hancinta , da Sauri Abla ta d’ago fuskar ta , shid’in ne kuwa tawaye jikin ‘kofa yayi crossing hannunsa a ‘kirji yana bunta da kallo , da Sauri Abla ta ajje spoon din hannunta tare da ‘boye cup din a bayanta , bakinta har rawa yake tana sanyi magana amma ta kasa , shigowa cikin d’akin yayi yana binta da wani irin kallo da yasata sunkuyar da kanta ‘kasa , Cup din data ‘boye ya d’auka da Sauri Abla ta ware ido zata kwace ya d’aga hannun sama, cikin Sauri Abla ta fara d’age tana san kwace cup din amma ya’ki bata damar haka,hannunta d’aya ya kama zuwa kan bed din tare da kallan cup din, cikin Sauri Abla ta d’auke idanuwanta “ Menene wannan ?”kallan cup din Abla tayi kafun ta furta alawa, kara kallanta Big Boss yayi kafun ya kai spoon din bakinsa Shima , ware ido Abla tayi ganin abun da yayi , ‘kara kai spoon d’in bakinsa yayi a karo na biyu tana sha , zai sha na ukun Abla tayi saurin d’auke cup din “ Kashanye mun abu nafa “, kallan yadda ta turo bakin yayi kafun ya janyota zuwa jikinsa “ Tom a sanmin” ka fad’a Abla ta girgixa masa alamar ah ah , ‘kamshin turarar da tai wanka dashi ne ya cika masa hanci shiyasa ya soma shinshiyar wuyan nata “ Mai kika saka a jikin ki mai ‘kamshi?” Ynzu ba turo bakin Abla tayi kad’an “ Ni babu abunda na saka fa “. Uhm kawai Big Boss yace yana kara rungumota a yanda suke , hannayensa gabaki d’aya yana kan cikinta , a hankali yake shafa cikin kafun ya furta “ Yaushe zan baki Baby Babies a jiya ?”, kusan kwarewa Abla tayi kafun ta furta “ Su wanene Babies d’in?” Fingers d’insa ya nuna mata “ Our Children, ‘Yan biyar xaki har famun tunda dozen uku xamu yi ko?” Tsayawa Kallansa Abla tayi kafun ta d’auke fuskarta gefe, “ Tafff ko d’an biyu bazan haifa ba ballantana 5 wai dozen 5 , to agwagwace ni ko maciji ?” Ta d’auka a zuciya tayi maganar şai da taji murmushi “ No my wife is Sunshine , don’t Worry zaki hanyar mana ai yan 5 d’in ko ? Ko kuma…” bata bari ya ‘karasa ba ta mi’ke zaune “ ko kuma wifey d’inka ko ? Fine “, ta fad'a zata sauka daga kan gadon ya ‘kara ri’kota “ Sunshine , wannan Kishin naki ko? Hmm , nifa kece zaki haifarmun 5 dozen d’ina kinji ? Maman Babies “, ya fad’a tare da kissing wuyanta , narai narai Abla tayi masa da ido kamar zatayi kuka , Şarai yaga yadda ta tsuren shiysa ya ‘kara furta “ ko yanxu zan fara baki ajiyar yan biyu? Anjima na baki d’aya ? Gobe na baki sauran “, hannunta Abla ta saka tare da kulle face d’inta “ Nidai ka bari please “, hannu yasaka ya d’ago da fuskarta “ Oya nunamun abunda kika fara nunamun a waya “ ware idanuwanta Abla tayi jin abinda yace , tana ganin yana ‘ko’karin maida kallansa kan kirjinta tayi saurin saka hannunta biyu tana karewa “Mai Kike ‘boyemun kuma ?”kasa magana Abla tayi Sabida da kunya , zai ru’ko hannunta tayi saurin zille wa tare da sauka daga Bed d’in “ Nidai Banaso “, da hannu Big Boss yayi mata alamar tazo , amma a maimakon ta zo d’in sai ta ri’ke ‘kugu tana masa Gwalo , cike da neman tsokana ta furta “ babu kyau “ bata ‘karasa ba ganin yana ‘ko’karin janyo ta ta haye kan gado zata güdü amma ya cafkota suka fad’a bed din , sai a lokacin Abla tayi masa fiki fiki da ido “ don’t worry , not now Baby “, hannunta biyu Abla ta sa’kala a wuyansa tana shafa dogon ba’kin gashin kansa ,bai ce mata komai ba shima yana jin yadda take ya mutsa masa gashin sa , cikin rad’a rad’a ya furta “ Yaushe zamu ajje yan biyar d’in mu ?” Abla kamar zatayi kuka ta furta “ mutuwa Kenan zanyi har lahira ko ‘ya’yan mage basa kaiwa biyar lokaci d’aya , kamar zaiyi murmushi sai kuma ya danne abunsa “ Amma ke Matar soja ce ai , 5 children at a önce ai zamu iya ko ?”, ‘bata fuska Abla tayi “ nifa ba kaza bace” , shima kamar ydda tayi ya kwaikwaya “ Tom shikenan ni zakara, kema sai ki dawo kazan , kinga har yan 10 xamu haifa ko ?” Shagwa’be face tayi kamar zatayi kuka ya ja hancin ta “ raguwa kawai.”
Chapter 83 · 0% Book details