← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 100

Sashe 75

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wasu irin mutane ne zazzaune cikin ‘kayataccen wajan da ya çıka da kayan alatu , ga wasu irin manyan kawu nan dabbobi daban daban musamman yadda aka rataye su tare da ‘kawon su ,  ba ‘karamun kayan alatu a ka zubawa wajan da za’a iya kira da wajan tsafi ba duk da irin kayan duniyar da aka narka a wajan. Sosai maza da matan Wajan sukai layi  cikin ba’ka’ken kayansu da ba’a iya ganin ko ina na jikin su , kamar masu shirin yin sujjada haka suka sunkuyar da kansu . Wani irin sauti da suka soma ji ne yasa ba shiri ko wannan su ya fara magana cikin siddabaru kafun suyi sujjada gabaki d’ayan su suna ‘kara d’agowa , sai da sukai hakan kusan sau uku kafin wani ba’kin haya’ki ya bayyana cikin d’akin wasu irin Sautika marasa dad’in ji suna tashi , ko wannansu sai suka soma juyi cikin kayan jikin kamar ‘kannan shed’an suna girgiza kai, sun d’au dogon lokaci suna abu d’aya kafun sautin ya tashi gabaki d’aya suka tsaya, kamar wasu aljanu suna taku biyu baya ko wannen su kujera ta bayayyana a bayansu a haka suka zauna  kawunan ko wannan su a ‘kasa .

    Cikin  sakannin da basu wuce minti d’aya ba wasu mutane suka bayyana a tsakiyar wajan , da’banın mutanan farko wad’an nan jajayan kayane a jikinsu sai wata sanda da ko wannan su ya ke ri’ke da ita , mutanan wajan suna ganin su ko wannan su ya ‘kara ‘kasa da kansa har saida Suka wuce gabaki  d’ayansu zuwa masaukin su na musamman , da alama süne manyan shuwagabannin Black Spider . 

    Suna zama wasu giant d’in maza ‘karfafa suka dunga shigo musu da cups cups na lemo amma idan mutum ya Lura sosai zaiga ba lemo ne a ciki ba , Jini ne a ciki a haka ko wannan su yake sha kamar sun samu ruwa ko la’akari  da ‘karnin jini ba sa yi da’alama ko d’igon imani basu dashi. 

 Mi’kewa tsaye d’aya daga cikin mutanan da suka shigo yanxu yayi , tare da soma wani irin siddabaru da hannun sa cikin ‘kan’kanin lokaci babban screen d’in wayan ya kunnu, gabaki ko ina na Wajan a na gani a ciki musamman yadda wajan ya rabu kashi kashi ga manya manyan makayan da suka saka kamar na tsaro a wajan ,  wucewa mutumin ya dungayi daidai wani daki me hudun gaske ya tsaya , gabaki d’aya ba’a iya ganin mutanan da suke ciki, waccen ya kalla ta gefensa ce ta ‘bace gabaki d’aya , ba a d’auki cikakken mintuna biyu ba matar ta bayyana a cikin screen d’in a Daidai lokacin da haske ya karad’e cikin d’akin. 

     Babu komai a cikin d’akin gabaki d’aya fanko ne ba’a iya ganin komai sai wasu ankwa dogaye guda biyu, tafiya ta somayi tana bin hanyar da ankwar take har zuwa ‘karshen wajan da ankwar ta ‘kare sai mutum da yake du’ke a wajan gabaki d’aya dogon gashin da yayi futu futu ya rufe fuskar mutumin da yake zaune sabida yadda dogon gashin ya rufesa , ba tausayi ko imani matar ta saka hannunta d’aki Wanda ya ke kwance , da ‘kar ‘karamun ‘kara ya iya fitowa daga bakin mutumin sa hannun da ya fito dashi duk jiki hannun sai faman karkarwa take , ganin tana ‘bata musu lokaci ne yasa matar ta dan’ki dogon gashin nan tana d’ago da fuskar Wanda yake kwance , ko motsi bayayi Sabida azabar galabaita . Fuskar macece ta bayyana ga tsananin wahala da ya gama bayyana a fuskar ta , ko bud’e idanuwanta batayi sosai Sabida yadda take tsayar wa , batare da imani ba matar ta hankad’ata zuwa tsakiyar wajan tana nemowa sauran matar da ta jefo, lokaci d’aya suka soma wata dariya cike da rashin imani . 

    ‘Kara matsowa matar da baza’a iya gane macece ko na namiji dan kusan shiga d’aya ce dasu ta d’ur’kusa tana matse fuskar matar da ta jefo, har yanzu idanuwanta kuma a kulle suke , cikin wata irin murya da baza’a gane macece tayi magana ba ko namiji ya furta “ Mai yasa kike da taurin kai ? Tsawan shekaru ana fama dake , kalkar Amincewa kawai aka ce ki anbata amma kina wahalar da kanki, da tun farko kin amince da mutuwar ‘Ya’yanki kamar yadda aka bu’kata da duk hakan bata faru ba da yanzu kina cikin daula kina juya mülki yadda kike so . 

     Kashe rai ba wani abu bane kamar yankan mage haka yake amma taurin kai irin naki ya sa kına wa Black spider jayayya , wannan shine Karo na ‘karshe da za a baki idan baki amince da kisan ‘ya’yanki da muke bu’kata ba zamu kashe su gabaki d’aya ne  sannan mu kashe ki, babu Wanda zai san da hakan sai mutuwa da ‘ya’yan ki zasuyi cike da tsanar ki , lokaci d’aya mutanan suka soma dariya . 

      Matar da tun d’azu batayi magana bace ta soma ‘ko’karin  mi’kewa zaune amma ta kasa sabida yadda jikinta yake karkarwa , cikin wata irin murya da bata fitowa sosai ta soma ambatan “ Yara na , yara na , yara na ku gafar ceni Ammu tana sanku , ku yafe mun yara na , ina matu’kar kewar ku .  Wata waya aka jefa mata cikin Sauri ta d’auka tana bin Wayar da kallo abun mamaki su Little ne zaune a falour suna hira shi da prince da alama game çıke Sabida yadda gabaki d’aya hankalin su ya karkata waje d’aya , sosai matar ta zuba musu idanuwana , lokacin da idanuwanta ya sauka kan Little da Prince kuka ne me ‘karfi ya ‘kwace mata, cikin sha’kewar murya ta furta “ kuya femun yarana Dan Allah”, suna jin ta ambaci sunan Allah gabaki d’aya suka razana suka mimmi’ke tsaye lokaci d’aya ta dunga jin saukar bulala a jikinta, har saida ta sume sannan aka ‘kara janta gefe akayi wulli da ita . 
Chapter 75 · 0% Book details