← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 103

Sashe 98

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai kuma ce mata komai ba, ya rungumo jikin sa, suna jiyo bugawar zuciyoyin su, ahaka bacci ya É—auke ta shikam saida ya daÉ—e sannan baccin ya É—auke sa,

               *******************

  ___A daren jiya cikin gidan nan ƙalilan ne suka rintsa dan yawancin su a tsayae suka kwana yanda suka ga rana haka suka ga dare har waye war gari,

Koda gari ya waye inda aka tsaya nan aka ɗora da neman Ameesha, dan wasu har sun fara saddaƙarwa ma ta ɓata, ga ɗaurin aure da za a gabatar yau wajen ƙarfe sha ɗaya zuwa shabiyu  za"a ɗaura , dan har anfara tunanin ko aɗaga auren amma manyan sukace ai bazai yiyu ba saboda wasu ƴan nesan kawai a ɗaura, da ɗaurswar da rashin ɗaurawar ai bazai sa aganta ko kar aganta ba,

Tsoron su ma kuma nan ma Maman ta anjima za'a sallamo su, zasu dawo gida,

Sha É—aya da rabi aka fara hallara a masallaci dan karfi sha biyu daidai za'a É—aura, mutane da dama sun haÉ—u a babban masallacin dake haÉ—e da masarautar,

Mutane har bakin layin, nan kaka gabatar da É—aurin Æ´an matan da samarin,

Daga nan cikin fadar ta ƙara cika da mutane, wasu na murnar ɗaura aure wasu na baƙin cikin rashin ganin Ameesha,

Ƙarfe wajen uku, Su Abban Ameesha suka dawo, nanna aka shiga murnar samun ƙaruwar da a kayi, amma koda wasa babu wanda yayi gigin sanar dasu halin da ake ciki, suma kuma basu tambaya ba saboda sun san hidimar biki ake, ba kowa zasu gani ba bare kuma ita da take layin amaren suma,

Kan kace me magana ta zagaye ko ina da samun ƙaruwar da akayi wasu suna ta mamaki ta yanda akai hakan ta faru dan wasu duk basu santa da cikin ba, wasu kuma suna cewa murna biyu ga ƙaruwa ga kuma biki, sai kuma wani baƙin cikin dake guda na rashin ganin wata,  wasu acewar su anrasa wata kuma ansamu ƙaruwar wata,

Magana dai tun ana ɓoye musu har ta fito fili, sukaji,

Shigowar Abban Ameesha falon kenan yaji ana zancen, Maman Ameesha saboda tsabar shiga wani halin ai ko magana ma bata iya yi ba,

Shima sanar dashi abun dake faruwa a kayi,

Guri yasamu ya zauna yana ƙara jajanta maganar tasu wai anrasa Ameesha wannan wace irin magana ce,

ÆŠan numfasawa yayi sannan yace "Amma kun kira Meer kuwa basa tare,
Dadda ce ta basa amsa cikin tsananin damuwa, tace shi da baya ƙasar ma taya za'ai su kasance tare, kuma ankira sa wayoyin sa duk akashe,

Abban Ameesha yace "a'a ɗazu kuwa da zan fita ai nagan sa, yana shigowa cikin nan mun haɗu a hanya, baide ganni ba ni naga shigowar sa, dande ina sauri ne shiyasa har na wuce bantsaya mun gaisa ba, gaskiya ku ƙara tuntubar sa, waye kuwa zai ɗauke ta acikin gidan nan, ko acan baya ba aɗauke ta ba bare kuma yanzu da komai yayi lafiya,

Duk a kusan tare suka sauke numfashi, Maama tace to Alahamdulillah ai zancen kenan ma indai kaga shigowar sa to suna ma tare, bari kaga aje part É—in sa aduba idan yana nan sai a tambaye sa, in kuma bata can sai asan abun yi shima asanar dashi halin da ake ciki....,

Abuu yace "Anya kuwa shi kagani yace fa baya ƙasar nan, kuma inzai dawo ai da yasanar damu koh?

Ummy ce ta karɓe sa da cewa "kaima sai kace baka san halin sa ba wannan ai cike daga cikin aikin sa, ba ƙaramin aikin sa bane yin hakan, ko kamanta loƙacin da yazo makarantar su, loƙacin ma ai cewa yayi baya ƙasar kuma ya akai yazo gurin, ni aganina kawai aje a duba, daga nan sai a yanke hukun ci danni wallahi jikina bai bani yarinyar nan ta ɓaga ba, duk yanda akayi suna tare ko kuma yasan inda take,

Gaba É—ayan su na'am sukayi da suna taren dan haka sai kawai Ummy tace bari taje ta duba,

Ita kaÉ—ai suka bari ta tafi part É—in sukuma suka zauna kowa na fatan Allah yasa dai suna can É—in......

  Ummy na zuwa part ɗin taga motar sa, nan ta ƙara tabbatar wa da yadawo ɗin bakin ƙofar taje ta shiga bubbugawa amma shiru ba a buɗe ba, ci gaba tayi da bugun ƙofar,

__Daga  can ciki kuwa Meer yana jin bugun dan loƙacin ya fito yana kitchen ya haɗa musu abun da zasu ci, ashe harda su girki ya kowa,

Tunda suka kwanta basu suka tashi ba sai wajen ƙarfe biyu, dan haka suna tashi wanka suka ƙara yi daga nan suka ɗan taɓa alalunbon su a banɗakin sannan suka fito suka shirya sukayi sallar Az'har daga nan kuma shine suka fito daga ɗakin yace shi zaiyi girkin da kansa, dan haka ya mayar da ita ɗaki yace ta zauna ta huta kar ta fito saidai taga girki kawai, har tsokanar sa tayi tace "Allah yasa dai yanzu kuma ba shinkafa zaka watsaba ka tsamota bata dahu ba kamar yanda kayi dankalin rannan, yana dariya ya fice daga ɗakin yace da kenan yarinya loƙacin ma iyawa ne banyi ba yanzu kam saidai ma in koya miki,

"Allah ya kiyaye, bandade cika baki,  Ameesha tagaya masa,

Shi kuma kawai yace mata to shikenan zaki gani, yana faɗar haka ya fita ya barta aɗakin ƙara kwanciyar ta tayi......

Yana gama girkinne ya juyo musu jalouf ɗin taliya da dankalin turawa, yayi musu, sai ƙamshi kuwa take ta faman yi, yazo daidai falo yaji ana buga ƙofar ko kallon gurin beyi ba yayi wucewar sa ɗaki, Saida ya shiga ya ajiye musu, sannan ya samu guri ya zauna,

Ameesha dake kwance taji ƙamshin ga bugar mata hanci, tashi tayi zaune, zatayi magana kenan taji an ƙara buga ƙofar, kallon sa tayi tace kamar nocking fa akeyi,

Ba tare da ya kalle ta ba, yace "Eh naji tunkan na shigo banson takura koma waye idan yagaji zai tafi,

"Amma dai yakamata ai kaje kaga ko waye, idan kuma kirane me mahimmanci fa, wataƙil ma su Abuu ne, kai wai tsaya ma ni sai yanzu abun ya faɗo min,  dan Allah su Dadda sun san inda nake,

ÆŠan juyowa yayi ya kalle ta kaÉ—an sannan yace "basu san ma na dawo ba bare su san inda kike,

Da sauri ta sauko daga kan gadon ta dawo inda yake tace "dan Allah wai da gaske, amma meyasa zakayi min haka kasan wane irin hali zasu shiga idan suka neme ni suka rasa, wane tunani kake so suyi, gaskiya kaje ka duba, ko kuma ni intafi, wannan abun ai ba daidai bane,

Tunda tafara maganar yake binta da kallo, saida tayi shiru sannan yace "to yanzu faÉ—a kike min kokuwa me,

Haɗe rai tayi tace ni bawai haka nake nufi ba, abun da ya dace na faɗa maka, tashi tayi daga inda take ta ɗauki hijabin ta, tace ni kaga wallahi fita zanyi wayasan yanzu a wane halin suke, ni bansani ba amma wallahi da tun ajiya sai asanyanda za'ayi ko zaka kashe ni bazan yarda in kwana ba, batare da sanin suba, sai faman kunfar baki take dan ranta ya ɓaci, tasan dole yanzu ana cikin wani hali ana neman ta,

Harta fara tafiya yayi saurin shan gabanta, gefen ta tabi zata wuce ya ƙara tare ta, shima kansa saida ta faɗa ɗin yaga hakan kamar be dace ba, dan dole su neme ta kuma idan ba'agan ta ba, hankalin su zai tashi sosai, zasuyi tunanin wani abunne yasame ta,

"Kasan Allah bazan ƙara zama ba anan idan kaga na zauna to sai na tabbatar da suna cikin kwanciyar hankali,

"To nani kiyi haƙuri kibari idan kika ci abincin sai mufita tare, amma dai yanzu kiyi haƙuri ki zauna kinji,

Maƙe kafaɗa tayi ta ƙara raɓawa ta gefen sa zata wuce, yayi saurin riƙo ta, yace "wallahi da gaske nake, in baki yarda bama ki tsaya ki gani yanzu zan kirasu awaya ingaya musu, idan kuma mun gama cin abinci sai muje, nayi miki alƙawari,

HarÉ—e hannun ta tayi, tana kallon sa, tace "promise?

"Yes I promise...,

Sai loƙacin ta yarda ta koma kuma duk da haka bata saki fuskar taba kamar da,

A bincin har yafara hucewa, zama tayi agaban abincin shima ya zauna, fork ya ɗauko ya ɗibo abincin ya kai bakin ta, ƙin karɓa tayi dai kawai ta kai hannun ta ga karɓi cokalin ta shiga ci da kanta, tana kai laumar farko, taji bakin ta ɗau abincin yayi zanƙwai kamar kunnen ka yacire, amma haushin shi da yake ji ya hana ta ta nunawa koda a fuska saima ya mutsa fuska da take.....

Kallon ta yake yana so yaji me zatace game da test É—in abincin, amma sai yaga tana ya mutsa fuska,

Ɗan leƙen fuskata ya kuma yi tare da cewa, 'ya dai ba daɗi ne naga kina ya mutsa fuska,

Ɗan ɗaga kai tayi batare da tace komai ba ta ciga ba da cin abincin tana jin daɗin sa amma duk da haka, taƙi bari ta nuna a fuska,

Wani ƙalulun abu yaji yazo masa wuya, jin tace ba daɗi gashi tana ya mutsa fuska, wani tunanin ya yafara yi to kodai da gaske ne, ba daɗin saboda shi baici ba yaji,

Ƙwace cokalin yayi daga hannun ta, sannan ya ɗiba yaci dan yaji ko dagaske ne babu daɗin, yana ci sai yaji da daɗi, ɗagowa yayi yana kallon ta yace kika ce, ba daɗi,

Itama kallon nasa tayi sannan tace,  "ai haka naji da yayi ai da bazan faɗa ba,

"Allah saidai kiƙi faɗar gaskiya amma ke kanki kinsan yayi daɗi,

"A gurin ka ba amma ni ko kaɗan beyi min ba inace ne kawai saboda yunwa, kaga ni nama ƙoshi, "ta ƙarasa maganar tana ture abincin gefe,

Kallon ta yayi sai yace "shikenan baki son fita kenan,

"Na ƙoshi ne kaga naci da yawa, Please kar muyi haka dakai, ka kirasu ka sanar dasu,

"Tom naji zan kira amma ki daure ki ƙara ci,

Bata ce masa komai ta jawo abincin gaban ta, daman bata ƙoshi ba,

Shi kuma sai ya tashi yaje ya É—auko wayar sa ya dawo wajen ya zauna akusa da ita ta gefe,
Chapter 98 · 0% Book details