← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 103

Sashe 60

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yauwa to wallahi karku yarda dashi shine mutumin da ya ɗauke wannan mutumin da muka kawo muku, tunjiya yakama mu yanzu haka muna wani waje a ƙulle shine yasa akayi mana duka har saida muka faɗi inda kuke, loƙacin ma da kuka dawo daga masallaci muna tare dashi da yagankune yace duk muɓuya kada wanda ya fito,

Saida kuka shiga mutanen sa suka ƙara kamomu suka kawo mu wani wajen daban yanzu haka muna nan angarƙamemu a ɗaki wayarnan ma basu san tana jikina ba,

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, Inna lillahi wa'inna ilaihi ÆŠan ladi, waye wannan mutumin shikenan ai yanzu haka duk ma abun da zai musu ya musu dan suntafi kano tare a motar sama suka tafi,

Shima Dan Ladi cike da damuwa yashiga yin sallati, yace yanzu dai yanda za'ayi ka kirasu kagaya musu tunkan suyi nisa, dan wallahi mutumin nan bashida imani ko kaɗan babu abun da bazai iya yi musu ba bakaga yanda yasa akay......, bamm yaji anturo kofa hakan yasa yayi saurin sauke wayar zai ɓoye amma ina anriga angansa da sauri suka ƙwace wayar suka shiga dukan sa dan sunji wata maganar tasa saboda suna kallon sa ta CCTV camera dake ɗakin,

Dan haka tuni suka hau dukansa É—aya kuma yace "bari insanar da Oga...... yafaÉ—a yana zaro wayar sa tare da barin É—akin......

"Hello, hello ÆŠan ladi ÆŠan ladi kana jina yanzu kuna ina? kana jina, yana ta magana baima san ankashe ba, saida yazaro wayar yagan ta akashe, kiran number tasa yakuma yi sai yaji anÉ—aga.,.

Ana ɗagawa yace "Hello kasan unguwar da kuke yanzu kaga yamin zan turo a fito daku ni yanzu zankira su kafin inbi bayan su nasan zan cinmasu dan basu daɗe da tafiya ba, maimakon yaji muryar Ɗan ladi sai kawai yaji ankwashe da dariya tare da cewa muna wajen gidan uwarka ka, ana faɗar haka kuma yaji ƙit ankashe wayar,

Ayuba ji yake kamar yayi hauka gefen titin yasamu yayi parking, tare da saurin lalubo number Dadyn Bossay, saboda bashi da ta su gaba É—ayan su,

saidai kuma sau uku yana kira ba'a ɗaga ba, da yaga ma ɓatawa kansa loƙaci kawai ya yanke shawarar gwanda ma yabi bayan nasu tun kan loƙaci yaƙara ƙurewa yanzu dai yasan duk inda suke yanzu basu fita daga garin Gombe ba idan yayi sauri zai iya kamosu....

A 360 ya kwashi motar shima ya ɗauki hanya yana gudun kuma yana ƙara gwada kiran layin Dadyn Bossay har yanzu kuma ba'aɗaga ba, gudu yake sosai kamar zai tashi sama haka yake jan motar nan,

yana daf zai fita daga garin wata ƙatuwar mota ta tunkaro sa gashi a ɓarin hannun sa take gurin sa take tunkaro wa gadan gadan kuma ta cike hanya amma duk da haka sai yayi ƙoƙari ya daina gudun yabi gefen ta zai sauka daga kan titin, amma ina kafin yakai ga sauka motar har ta ƙaraso kusa dashi tare da dakar gaban motar sa take yafara juyawa aka ƙara buga masa ya motar ta wuntsila can gefen titin, masu babar motar kuma sukayi tafiyar su, suka barsa agun........

***********************

Gudu suke shararawa suma kamar akan titi dan ba ƙaramin gudu Dadyn Rasheeda yake yi ba, sai gashi tafiyar da zasuyi wajen awa biyar ko shida amma baifi suyi awa huɗu ba,

Suna cikin tafiyar kuwa dan ina tunanin ma sun kusa shigowa kano saboda ko awa ɗaya ba lalle su ƙara ba,

kawai basu san ta inda mota ta fito ba sai gani sukayi kawai tasha gaban su sai kuma wasu ta bayan su, dan haka da sauri Dadyn Rasheeda yaja burki ya tsaya,

mutane ne zabga zabga suka fara fitowa daga cikin motacin fusko kin su duk a É—aure, sunkai wajen su goma sha biyar haka suka zagaye motar, da sauri Dadyn Rasheeda ya buÉ—e motar ya fito Abban Ameesha ma cike da tsoro da fargaban abun da zai faru ya fito dan yagane mutanen masu gadin sane irin kayan da suke sakawa kenan kuma daman kullum ahaka yake ganin su, shiyasa yayi saurin fitowa dan yasan ma shi suka biyo,

Bossay zai buɗe ya fito shima Hamza yayi saurin riƙeshi yace "ɗau ko wayar ka, kafin su ankare kayi sauri ka turawa Dadyn ka message kagaya musu kawai wasu mutane sun tare mu a akan hanya a biyo tracking ɗin mu, dan waɗannan mutane baza su barmu ba, kayi sauri ni kuma bari in gayawa su Sam duk wanda ya riga gani sai azo a taimakawa bawan Allahn dan bana son wani abun yasame shi, duk wannan zancen yayi sane cikin sauri ƴan sakanni tare da fara rubuawa, shi Bossay harma yagama rubuta nasa ya tura, kuma saida sukayi sharing ɗin message ɗin ga wasu ta yanda za abasu taimakon gaggawa,

Ganin sun rirriƙe Abban Ameesha yasa sukayi saurin fitowa suma, duk wannan bataliyar mutanen kan Abban Ameesha sukayi suna ƙoƙarin jansa amma ya hana kowa dama dake yana da ƙarfi ga kuma zuciyar sa da yazo kusa yagama kaiwa ƙarshe ji yake babu abun da bazai iyaba ga duk wanda ya kuma yunƙurin rabasa da ƴan uwansa iya ka ƙarfin sa yake sawa wajen kaiwa duk wanda yazo zai taɓasa duka,

Su Hamza kuma suna fitowa tuni wasu mutum biyu sukayi ran dasu suka hanasu ƙarasawa inda yake, Dadyn Rasheeda ma riƙe shi akayi,

Sauran kuma duk suka tararwa Abban Ameesha tun yana yi da jiki har jikin sa yafara gajiyawa yadawo kai dukan a hankali daga ƙarshe ma sai ya kasa kawai ya zube awajen ga gajiya ga baƙin ciki sai kawai yasa kuka, cikin kuka yace dan Allah ku kasheni ku huta ku kasheni burin ku ya cika wai me nayi muku me nayi muku kuka zaɓi ƙuntatawa rayuwata, baigama rufe baki suka rufe sa da duka...

Dadyn Rasheeda har da su kuka, yazo kusa da su yana tsugunnawa dan Allah ku rabu dashi me yayi muku idan kuɗi kuke so kufaɗi ko nawane ni zan baku amma ku rabu dashi kada ku cutar na roƙeku kunji dan Allah ku rabu dashi,

Babu wanda ya saurare sa da suka gaji da dukan nasa sai kawai suka fara jansa, zasu sakasu a mota,

Hamza ne ya gama kaiwa ƙarshe shima tuni ya turar da wanda ta riƙeshe yayi kan su yana zuwa ya shiga sauke musu naushi duk wanda ya nausa sai yaja baya dan ba ƙaramin bugu yake kaimu su Bossay ma da yaga haka sai yasamu ƙarfin gwiwa, daidai tsinin gwiwar sa ya saita adaidai wajen alulun wanda ya riƙe shi ya taƙarƙare ya buga masa agabansa take azaba tasa mutumin yasake sa yasaka hannu akai yana tsalle dan yaji zafi ji yayi kamar ransa zai fita,

Nan faɗa ya kauraye tsakanin su kowa nayin iyaka ƙarfinsa, suna ƙoƙarin ɗauke Abban Ameesha, su Bossay kuma na ƙoƙarin hanasu........,
[15/11, 10:53 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                         *_🅿️36_*

___'Nan faɗa ya kauraye tsakanin su kowa nayin iyaka ƙarfinsa, suna ƙoƙarin ɗauke Abban Ameesha, su Bossay kuma na ƙoƙarin hanasu........,

.......haka sukai ta kokawa, zuwa yanzu kuma su Hamza jikin su yafara sanyi duk ƙoƙarin su amma dake sunfisu yawa dole suci galaba akansu.

"babu yanda suka iya suna gani aka aka É—auki Abban Ameesha aka saka amota suma kuma É—aya bayan É—aya duk suka kwashe su suka zubasu amotar gaba É—aya suka tattara su amotar su,.

Dadyn Rasheeda kuma suka sakashi a motar sa, wasu mutum biyu suka shiga É—aya yaja motar É—aya kuma ya zauna a gefe motar suce tafara yin gaba, sannan ta sauran suka bi bayan su,

Wani shu'umin murmushi Dady yake ta saki, kwantar da kansa yayi ajikin kujerar, sannan ya zaro wayar sa yayi danne danne ya dannawa wata number kira, ana ɗaga yasaki dariya yace "angama komai dan ma sunɗan bamu wahala da tuni mun taho tun ɗazu yaran akwai ƙarfi bakiga yanda suka wahalar da kansu ba, Allah ya taimake mu dai  yanzu munci nasarar ƙwamishe su. Kina ina ne yanzu? shiru yayi yana sauraron ansar da ake basa..

"To shikenan muma yanzu zamu shigo cikin garin, amma fa gaskiya bazan ƙara sakaci ba asirina ya tonu dan indai suka gansa kinsan sai asirin mu ya tonu dan haka muna zuwa zansa akashe shi, ni bansan dalilin da yasa kika hana akashe shi, yanzu  gashinan barin sa yana neman yajawo mana matsala,  shiru yayi yana jin maganar da akeyi daga can ɓangaren,

Tsaki yaja sannan yace "wallahi baki isa ba mu zuba mugani ni zaki kawowa maganar banza bari zanzo insame ki, kuma kisa aranaki ina muashigowa garin Kano zai mutu dole ya mutu dan bazan taɓa barin sa yaci gaba da zama ba a duniyar nan, kina gani tunda waɗancan yaran sun gansa kina tunanin zasu shiru da maganar inba ganin gawar sa sukayi ba, baza suyi shiru da bakin su ba, dan haka nagama yanke shawara yauce ranar mutuwar sa. Yana kaiwa nan baima jira amsar taba ya kashe wayar gaba ɗayan tama saboda karma ta kirasa,

sukaci gaba da tafiya yana ta saƙe saƙe kala kala na yanda zai tsara komai yatafar masa yanda yake so,

***********************

Baban Bossay fitowar sa daga wanka kenan yaji ƙarar text ya shigo wayar sa shareta yayi babi takan taba, ya wuce ya cigaba da shirin sa, har yagama kintsawa, ya ɗauki wayar sa, yama manta da jin ƙarar saƙo. Sai kawai ya zurata a aljihu ya fice daga ɗakin,
Chapter 60 · 0% Book details