← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 103

Sashe 63

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana gama sakawa ya zuge mata zif ɗin, sannan ya janye ta daga gurin ya ɗauko wani miyafi da ya shiga da kayan, Saida yanzu ya ɗago ya kalle ta, ita kuma idon ta yana ƙasa bata yarda sun haɗa ido dashi ba,

Mamaki baigama kashe Ameesha ba saida taga ya ɗaga ɗankwalin ya ɗaura mata akai amma ɗaurin ba zauna ba kuma tana jinsa bawani ɗaurin arziƙi yayi mata ba cukukuye shi kawai yayi ya haɗa da gashin ta dake ɗaure,

Ƙara ɗaga mayafin yayi da kansa ya yafa mata shi, maimakon ya saka mata aka faɗa sai ya yafa mata shi akai,

Duk wannan abun da yake ko kallon inda yake ma batayi ba bare ta tanka masa, dan gani take kamar baya cikin hayyacin sa ko kuma ya fara shaye shaye ne yasa yake mata haka, dan asanin da tayi masa dai tasan hakannan bazai taɓa yi mata haka ba shine da kansa zai saka mata kaya, gaskiya dai da alamar tambaya a wannan sabon lamarin nasa indai kuma ba wani aljani ne ga shiga jikin saba....,

Hannu yasa ya goge mata fuskar ta, saida yaga ta dawo daidai babu komai akanta ƙura mata ido yayi yana sake ganin tsantsan kamannin ta da Abban ta sak babu inda ta barshi, abu ɗaya zata nuna masa shine haske ta ɗan fishi haske,

tsarguwa tayi da kallon da yake mata hakan yasata ɗagowa dan ganin me yake, tana ɗagowa suka haɗa ido sai kawai ya ɗaga mata gira,ita kuma tayi saurin mayar da idon ta ƙasa tana me ƙara mamakin sa, tunanin take anya ma kuwa shine,

kamo hannuwan ta yayi gaba ɗaya yasaka cikin nasa ya riƙe gam yana kallon fuskar ta yanda tayi wani kicin kicin sai kace mai shirin daukar mataki akan abun da yake mata, share wannan tunanin yayi cikin sanyin murya yace "kidaina wannan haɗe haɗen ran kuma kar kiƙara kuka yau ba ranar baƙin ciki bace yau ranar farin ciki ce musamman agare ki, nasan duk yanda zanji farin ciki bazai taɓa kaiwa irin naki ba, nasan zakiyi mamakin abun da nayi miki to ba komai bane yasa nayi miki illa tsantsar farin cikin da nake ciki, na daɗe banyi farin ciki ba irin na yau, shiyasa bana son duk wani abu na ɓacin rai ya biyo baya, dan haka saki fuskar ki yanzun nan kinji ni, muje kiga wani abu.....,

Sai yanzu ta samu damar ɗagowa ta kalle sa cike da alamar neman ƙarin bayanin maganar da yayi masa dan bata fahimci inda zancen sa ya dosa ba,

Jinjina mata kai, saboda ya fahimci kallon tambayar da take masa, bai bata amsa ba sai kawai yaja hannun ta ya fara tafiya da ita,

Itama bata ce masa komai ba, ta shiga binsa abaya, cike da mutuwar jiki danji tayi gaba É—aya jikin ta yayi mata wani iri,

Ahaka suka fito daga ɗakin suka shigo falo da taga dai fita zasuyi suna zuwa bakin ƙofa ta tsaya kamar zatayi kuka tace "bansaka takalmi ba fa,

kallon ta yayi ta gefe sai yace "ina takalmin?

Tace "É—aki.

Ganin yayi ɓata masa loƙaci zatayi idan ta koma sai kawai yaɗaga hannun ta da ya riƙe ya ɗaga ya ɗora a kafaɗar sa, ya ɗan ranƙwafa yasaka ɗayan hannun kawai yayi sama da ita ya saɓeta kamar ƴar baby ya buɗe ƙofa,

Cikin zaro manyan idanun ta bakin ta har yana karkarwa tace "sauke ni sauke ni tana faɗa tana ciccilla ƙafafu,

Ko kallon baiyi ba bare tayi tunanin zai sauke ta,

Tunda suka fito ma'aikata suke kallon su cike da burgewa kowa na mamakin sa,

Ta inda ya biyo ta nan yabi yanda su Bossay baza su gansa ba, suna zuwa bakin gurin ta nemi ta sakar masa kuka akan dole sai ya sauke ta, ita kar ya shiga da ita gaban mutane a haka,
Haɗe rai yayi yace "ke ina miki wasa ko wallahi kikayi kuka sai kinga yanda zanyi dake sai na baki mamaki wallahi, tsit tayi bata ƙara ce masa komai ba,

Haka ya tura ƙofar ya shiga da ita cikin fadar, ai suna shiga kamar jiran shigowar su ake kowa ya zuba musu idanun wasu kamar zasu faɗo musamman su Abu, dan atunanin su ko hakan shine maganar da yasa ya tara su agun, dan har taƙaici yafara kama wasu...,

Ɗauke kai yayi kamar baisan ma'anar kallon da suke ba, Saida yazo tsakiyar gurin sannan ya dire ta, wata kujera da ya hango can baya, ya ɗauko ya ajiye ta sannan yakamata ya zaunar da ita ya ƙara gyara mata mayafin ta, yana kallon yanda su Papa suka zuba masa ido, yasan daman za'ayi haka, kallon su ta gefen ido kamar irin baisan da suba dake ya ƙware a iya shege saikawai yasa hannu ya shafo fuskar ta, sannan yace "kar kitashi daga nan gurin yanzu zan dawo,

Ɗagowa yayi idon sa suka sauka akan Abu sai kawai ya ɗaga masa gira dan ya ƙara ƙullar dashi kuma yaƙi cewa kowa komai ya juya ya fita daga cikin fadar,

Yana fita sai kawai gurin ya kauraye da surutu kowa da abun da yake faÉ—a wasu suna cewa ya raina musu hankali ya tarasu agu kuma yazo yanayin wasu abubuwan da suka kasa gane inda ya dosa,

Ameesha kam kunyar duniya da taƙaicin sababin abubuwan da Meer yake mata ta kasa koda da ƙwaƙƙwaran motsi duk maganar ma da ake mata takasa ɗagowa tayi magana,

Suna cikin hayya niyar nan saiga Meer ya ƙara shigowa tare da Bossay da Hamza da baban Rasheeda, guri Meer ya nuna musu suka zauna,

Duk da shigowar su bata sa mutanen sunyi shiru ba saida Meer ya ɗaga murya yace kowa ya saurarara da ƙyar sukayi shiru amma Papa yana yiwa Meer magana da cewar sun gaji basa son rainin hankali ya sa sun taru sama da wajen awa ɗaya ya shanyasu suna faman jiran sa,

Maimakon Meer yabasa haƙuri sai kawai yace "ai sai nagama jan aji zan sanar da koma meye kai nama fasa sai anbani tuƙuici ko kuma in fasa faɗa,

ÆŠan dariya Papa yayi yace to shikenan faÉ—i komai kake so dan mungaji da zama,

Ɗan taɓe baki Meer yayi yace wannan kyautar mutum ɗaya ne zaiyi ta so nake ta fito daga gun sarki in ba haka ba kuma na fasa,

Harara Abuu ya wurga masa daga inda yake saboda yasan yana fushi dashi baya kulasa shine zaiyi masa wannan abun agaban mutane,

Shikenan kagani Papa hara ta yayi to anfasa kowa sai ya tashi indai bazaiyi magana ba to nima na fasa cewa komai,

Papa ne ya kalli Abuu cike da tsokana yace "to kaji ango yana magana kabashi ƙyauta kar kayi mana asara kan ran ya isa haka tunda kaga haka Ni masan ba'a banza ba,

Maama itama cike da farin ciki dan ta fahimci mutumin nata yana cikin farin ciki dan bata taɓa ganin sa cikin irin wannan yanayin ba dan haka tasan tabbas ba ƙaramin abu bane yasa shi haka, ga yanda taga yayiwa Ameesha hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata, ba ita kaɗai ba duk sauran ma haka,

Shima Abuu ta ciki na cikine amma fal yake da farin ciki musamman da yaga ya nuna yana so yayi masa magana, dan a iya rayuwar sa, Meer bai taɓa yi masa laifi ba ya nemi su shirya ko yaba sa haƙuri saidai idan ya gaji dan kansa ya sauko ya ci gaba da yi masa magana amma shi ko akwalar rigar sa, shiyasa da yaji ya sako dashi sai hakan ya faranta masa rai sosai,

"Ni wacce kyauta zan baka bayan wacce na baka ga tanan agaban ka ai babu kyautar da ta fita, kuma nasan ita kafi buƙata, dan haka malam babu wata kyauta kuma wallahi baka isa ka ɓata mana loƙaci a banza ba, sai ka faɗa ko kuma a matsayina na sarki inda ayi maka hukunci me tsauri,

Wayyo abun mamaki yau ga Meer yayi murmushin gefen baki, bani kaɗai ba kowa dake cikin fadar saida yayi mamaki, dan babu wanda yataɓa ganin hakan sai yau,

Abun da Abuu ya faɗa ba ƙaramin nishaɗi yasa Meer ba, girgiza kai yayi yace "da kuwa anyi yaƙi na biyu dan bazan bar kowa da raiba har shi sarkin, danni nine gaba da kowa bawani sai ni daga Ni kuma sai UNCLE ɗina sannan wasu su biyo baya kafin ayi maganar wani sarki,

"UNCLE É—ina Abuu ya maimaita sunan yana kallon sa,

Saurin canza maganar Meer yayi kafin ma wani yayi tunanin me yake nufi da yace UNCLE dan yasan ba kowa zai kawo me hakan yake nufi ba,

Abuu zaiyi magana Meer yace "kaga kowa yayi shiru na kunyi sa'a kunci darajar me daraja, da bazan faÉ—a ba,

Yana kaiwa nan bai jira amsar kowa ba ya juya ya bar fadar, yana fita yadawo ɗan leƙowa yayi yace kowa ya shirya?

Gwaggo duk ta ƙosa taji meye tace kai wannan yaro baka da kirki wallahi sai kace wasu sa'annin ka ka ajiye anan kakewa mutane yawo da hankali, ni wallahi da tuni nayi bacci kai uku da nasan wannan shirmen zakayi mana da banzo ba wallahi bansan ka da wannan halin ba, haba ya kake haka ne.....,

Hararar ta kawai Meer yayi baice mata komai ba,

Saidaga baya yace "kuyi haƙuri yanzu wannan ne na ƙarshe wallahi daga shi bazan ƙara cewa komai ba, kowa idon sa zai gaya masa,

Dan Allah kowa ya rufe idon sa zan shigo da abun, kuma banda maƙe ido kowa ya rufe yayi tsakani da Allah idan ma ka baka rufe ba baza ka gani ba,

"Papa yace "kai wai yaushe ka zama hakane dan Allah duk ka canza kamar bakai ba me ya canza ka haka loƙaci guda,

"Kaidai kawai kayi abun da nace zaka ga abun da ya canza ni kaima zai canzaka,

Daga nan ya kuma roƙon su da Allah haka kuwa sukayi masa yanda yake so, kowa ya rufe idon sa,

Daman Abban Ameesha yana bayan sa ya ruƙo hannun sa, shiyasa bai shigo gaba ɗayan sa ba ya leƙo,

Jawo sa yayi suka shigo ciki, saida ya kawo sa gaban Ameesha suka tsaya sannan yace "kowa zai iya buÉ—e idon sa yanzu,
Chapter 63 · 0% Book details