Sashe 29
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Takawa yafara yi saida ya ɗan gotata kaɗan sannan yace"zamu tafi kamar yanda kike so zan miki biyayya amatsayin ki na mahaifiya ta kuma da bin umarnin ki, dan haka zan tafi kuma bazan ƙara dawowa ba kamar yanda kikace ba kyaso kiƙara ganina ni kuma nayi alƙawarin bazan sake dawowa inda kike ba, kuma koda kin gane gaskiya kar ki nemeni tunda a loƙacin da na tsugunna agabanki ina baki haƙuri baki saurareni ba kuma kinƙi ki saurari bayanina, idonki ya rufe duk uwar da zatayi shekara da shekaru bata fahimci abun ɗanta zai iya aikatawa ba da abun da bazai iya aikatawa ba, to kuma waye zai iya fahimtar ka...,
"Kaga ba neman jin ta bakin ka nake ba ka fice min daganan wacce irin fahimta ce kuma zanyi bayan nagama fahimtar komai da ido na, ai ba wani bayani da yarage wanda banjiba, Sameer kafita zan ƙara maimaita maka bana son inƙara ganin ka, taƙarasa maganar cikin ƙunar rai idon ta kuma yana kan hannun su, riƙe hannun ta da yayi shi yaƙara haddasa mata ɓacin rai fiye da na farko, dan tana ganin yagama rainata,
Sam baiƙara ce mata komai ba ko juyowa baiƙara yi ba yaja hannun Sumayya suka fice daga ɗakin,
Sumayya nayi masa magana tana jan hannuta daga riƙon da yayi mata, amma yaƙi saki haka ta haƙura taci gaba da binsa amma idon ta na kansa ahaka suke tafiya har suka fito daga part ɗin,
Duk abun da takeyi yana sane da ita har kallon sa datake yana jinta amma ko sauɗaya bai juya ya kalle ta ba saboda bayaso tasan halin da yake ciki dan har ƙwalla saida ya zubar loƙacin da zai fito daga ciki, shiyasa bayaso su haɗa ido,
*Hamza*
Bayan sun gama maganar da Azeema daman akan batun abun da mahaifiyar sa tayi musu ne yasa shi yazo dan yaƙara bata haƙuri, nuna masa tayi iya ba komai, komai ya wuce iya Yakamata ma tayi masa godiya akan taimakon da yabawa mahaifin ta,
nandai suka sasanta tsakanin su har suka ɗan fara hira sai kuma yakawo mata maganar son da yake mata zata amince dashi ko kuma ya haƙura dan shi wallahi sonta yake tun ranar da yafara ganin ta kuma har yanzu son ta yana nan bai ragu ba saima ƙaruwa da yayi,
Nan madai yaɗauka zaisha wahala sai kuma yaga ta ƙara nuna masa ba wata matsala atake agun ta amshi tayin sa, domin itama yayi mata da farko bata sonshi amma daga baya da ta fara sanin halayen sa na gari da kuma irin taimakon da yayiwa mahaifin ta sai taji ya kwanta mata saboda ba halin su ɗaya da mahaifiyar saba, kuma badan shiba da tuni ankashe mahaifin ta dan haka irin taimakon da yaringa yi masa shikaɗai ya isa yasa ta amshi tayin soyayyar sa, kodan ta faran tama sa shima duba da yanayin da ya tsinci kansa baida kowa a halin yanzu,
daga nan sukayi sallama ko wanne su ransa fesss musamman Hamza da yake jinsa kamar awata sabuwar duniyar ta daban daɗi kwa ji yake kamar ya zuba ruwa aƙasa ya sha, bayan rabuwar su har wani tsalle tsalle yake yana tafiya ya taho part ɗin fulani dan so yake yaje yabawa Sam labari duk da basa haka dashi amma dai farin cikin sa na yau na dabanne bazai barsa aransa ba shi kaɗai sai ya samu wanda zaigayawa ya taya sa farin ciki,
Dan haka ya taho da murnar sa, amma tundaga nesa ya hango sa zasu shiga mota da sauri ya nufi inda suke sai kuma yayi saurin dakatawa da tunanin ko wani wajen zasu idan sun dawo yabasa labari yanzu bari yaje ko shi kaÉ—ai yayi nishaÉ—in sa kan anjima ya kirata dan har exchanging É—in Number sukayi tabashi tata yace zai kirata......,
Sam na fita momma taji ƙafarta tayi mata wani irin nauyi take taji jikin ta nashirin daina ɗaukan ta da sauri ta lallaɓo ta fito daga ciki guri ta samu ta zauna akan kujerar falon fulani, tana zama taji zuciyar ta ta karye miƙewa tayi taje jikin window tana hango su yanda suke tafiya kana gani kasan ba lafiya atattare dasu, kallo ɗaya zakayi musu ka fahimci hakan, tana ganin su har ya buɗe motar ya sakata ya rufe sannan ya zagayo ya shiga shima ya tayar da motar yabar gurin tun tana hango sa har ya ɓace ma ganin ta, ta daina hango motar sa,
Sakin labulen tayi tana ja da baya da baya, maganganun sane suka fara dawo mata arai, to mai yasa bata tsaya ta saurare sa ba, kukane ya kuɓuce mata tayi saurin saka hannun ta, ta toshe bakin ta, tana sakin wani kukan mai sauti, idan ta tuna wai ita da kanta ta kori ɗanta to mai yake damun kanta mai yasa bata fara tunani ba mai yasa tayi saurin yanke hukunci,
_dan girman Allah momma ki tsaya ki saurare ni, ni bahaka nake ba ba halina bane ke kanki shaida ce da ace halina ne da tuntuni kin daɗe da sani shekarata nawa amma baki taɓa ganin da mace ba, wallahi ko hannun wata macen bantaɓa riƙewa ba bayan ita itama kuma da dalili bawai hakan nan ba ki tsaya inyi miki bayani kar kiyi saurin yanke min hukun cikin fushi, momma dan Allah_
Tuna wannan maganar tasa ba ƙaramin ƙara sata danasni tayi ba gashi tun ba aje ko ina ba tayi nadamar abun da tayi, gashi tasan shi da taurin kai yanzu ko tace yadawo bazai dawo ba koda zai dawo bazai dawo nan kusa ba, yanzu mai zatacewa mahaifin sa mai zatacewa ƴan gidan ga duk wanda ya tambaye ta, zatace ta koresane saboda takamasa da mace aɗaki ko kuma mai sosai kuka yaci ƙarfin ta, ita kaɗai a falo ta rasama wane irin tunani zatayi ta samowa kanta mafita,
Tana cikin wannan halin taji anturo ƙofar falon da sauri ta miƙe tsaye tare da saurin goge hawayen ta,
Hamza da ya shigo da saurin sa da murmushi ɗauke akan fuskar, loƙaci ɗaya kuma murmushin ya ɗauke tare da yin turus yana kallon momma da tayi saurin kawar da kanta, ganin shine ya shigo,
Yana ƙoƙarin yi mata magana ya buɗi bakin sa kenan kawai ta ɗaga masa hannu, sannan tabi ta gefen sa ta fice a halin da take ciki yanzu babu wanda zata iya magana dashi,
Binta yayi da kallo har ta gama ficewa yana mai tambayar kansa abun dake faruwa, abun ba ƙaramin mamaki yabasa ba,
Can falon ya wuce yana shiga yayi karo da kwanukan abinci, ganin hakan yabasa amsar dukka nin tambayoyin sa dafe kansa yayi yana cewa kashhhh ya a kai haka ta faru yarfar da hannu sa yayi yana mejin taƙaicin fitar da yayi da bai fita ba da hakan bata faruba, yanzu ya zaiyi ta ina zai fara neman sa yaji mai yafaru gashi baida number sa,
Kuma daga ganin fuskar momma babu walwala akwai babbar matsala bare yaje yayi mata bayani, dan yasandai fushin nata bazai wuce na ganin su da tayi ba, to mai haddasa zubewar abu kodai wani abu tagani sunayi, da sauri ya girgiza kai a fili yace "kai a'a maima zasuyi babu abun da zasuyi wataƙil dai kawai ganinta aciki ya haddasa wannan matsalar, amma dai bari ya jira dawowar sa yaji mai ya faru, can cikin ɗaki ya wuce kawai zuciyar sa duk ba daɗi ji yake gaba ɗaya laifin sane, sai gashi shi da ya taho da murna amma saiga murnar ta koma ciki babu damar yin ta......,
*Amsh&Azm*
"Wai ke tun ɗazu kin ishi mutane da surutu kuma nace ki faɗan mai yace Miki amma kinƙi kuma kin dameni da zancen sa kodai soyayya kuke ne naga tunda muka dawo kin kasa haɗa nutsuwar ki guri guda, duk Ameesha ce mai wanann maganar,
"hmmm yarinya ce ke kibari duk sanda kika girma nagaya miki ni matsamin in kwanta sai nafi jin daÉ—i a kwance,
Ameesha tace "wallahi bazan matsa ba duk girman gurin nan bai ishe kiba,
Azeema tace "idan kika kwantar da hankalin ki ma daga yaune ba ƙara ganina zakiyi ba akusa dake,,
Atake Ameesha ta canza fuska tana turo baki wai dan Allah da gaske kike baza kibar tafiyar nan ba idan kinje gidan mai zakiyi muna zaman zaman mu kuma sai kice zaki tafi, Allah besty bana so, dan Allah kar ki tafi kibar bestyn ki idan kika tafi ina zan dafa,
Azeema na dariya, tace "Allah kwa sai naje saidai zan iya yi miki alƙawari sati ɗaya zanyi kuma shima da sharaɗi ki tabbatar ina dawowa zamu fara zuwa makaranta dan nagaji da zaman gidan nan, danma yanzu Allah ya taimake Ni yanzu nasamu na rage loƙaci bakamar daba,
Ameesha da bata fahimci zancen taba shiyasa bata bi takan taba, sai kawai tace "a'a gaskiya sati É—aya yayi yawa ina laifin ma kiyi kwana biyu amma sati besty yayi yawa, Allah idan kukayi kwana biyu ayau zuwa gobe zanyi wa yaya maganar ko maama duk yanda sukace zakijini,
Azeema ta harare ta tace "a ina zanjikin ke da baki da ko calculator bare waya,
Ameesha zata bata amsa kenan sautin ƙarar wayar Azeema ya katse mata maganar da take shirin yi,
Murmushi Azeema ta saki tare da É—aga wayar ta kwanta sannan taja bargo ta rufe har kanta,
Duk nacin Ameesha dan tajiyo abun da take cewa amma takasa babu abun da take ji dole ta haƙura, tana mai mamakin canzawar Azeema haka, itama abin rufar tayi kwanciyar ta bata ma daɗe da kwanciyar ba bacci yayi gaba da ita, Azeema kama anacan ana soyewa da Hamza acikin waya saikace sunyi wajen shekara biyu atare daga ɗan haɗuwa, har sun saba sosai......,
*Sam*
tunda suka fito bai tankawa Sumayya ba duk da haƙurin da take basa,
Maimakon taga yakaita gida sai kwai taga ya nufi wata hanayar daban zuba masa ido tayi kawai har suka ƙarasa hospital ɗin sa, tayi tunanin ko wani abun zai ɗauka shiyasa bata ce mata komai ba, suka fito a tare suka shiga ciki can office ɗin sa ya kaita, tana zama yaƙara fitowa ba daɗewa yaƙara komawa ciki,
Samun guri yayi ya zauna tare da zabga tagumi,