← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 103

Sashe 86

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ameesha ce ta tashi daga kusa da Dadda ta koma kusa dashi tare da kamo hannun sa tace "Abba na kana tare da damuwa gata nan a idon ka, ɗazu ba haka kake ba, dan Allah koma me yake damun ka kayi haƙuri kaji,

kallon ta kawai yake maganar da tayi sai duk gaba ɗaya ta ƙara karyar masa da zuciya, rungume ta kawai yayi yana me jin zuciyar sa gaba ɗaya a cunkushe, cike da sanyin murya, yace "Dole in shiga damuwa baby ina cikin kewar mahaifayar kine shiyasa kika ganni cikin damuwa, duk sanda na tuna haka nake kasancewa, naso naƙara ganin ta araye akaro na biyu, amma gashi ta tafi ta barni, ya ƙarasa maganar tare da jin ƙwalla ta cika masa ido,

Hannu yasa yayi saurin share ta, itama kukan take kawai fili ne bai fito ba, amma fuskar ta har ta gama jiƙewa da hawaye, Saida ya ɗagota ya gani da sauri ya shiga goge mata yana so ya rarrashe ta amma yana jin idan ya buɗi baki da niyar yin magana shima zai iya sakin kukan dan yanda yake jin zuciyar sa tana daf da tsinkewa,

A hankali ta shiga takawa ta zuro ƙafar ta cikin falon tare da ƙara zuro ɗayar halin da take ciki yasa ko sallama bata, yi ba baba ne ya shigo shima amma shi da sallamar sa, ya shigo hakan yasa sauran ɗagowa suna kallon inda suka ji  sallamar,

Dadda ce ta miƙe tsaye da sauri har ta neman faɗuwa, halin da ta tsinci kanta ya hanata, magana kawai hannu ta ɗaga ta fara nuna su, sai motsi take da baki tanaso tayi magana, al'ajabi da bazata sun hanata furta komai,

Abban Ameesha kuma da Ameesha ya rungume ta hakan yasa basu ji sallamar da a kayi ba, hankalin su yana kan na juna.

Ita kam tunda ta shigo idon ta ya sauka akan su bata ganin fuskar sa da kyau shiyasa ta tsayar da idon dan gano abun da idanuwana ta suka gane mata,  idan idanunwan ta basu yi mata ƙarya ba kamar Noory ɗin ta take gani agun, shiyasa bata ma kalli inda Dadda take ba,

Jitayi kamar anajan ta hakan yasa ta shiga takawa zuwa gare shi, bata tsaya ba saida taje gaban sa, cikin wata irin murya me sanyi da nutsuwa tayi ta a hankali, tace...

NOORY....!

Jin muryar yayi kamar saukar aradu a cikin zuciyar sa saura kaɗan ya zauce jin muryar, a sukwane ya ɗago kansa tundaga kan ƙafar ta yafara kalla har ya kawo kallon ga kan fuskar ta, wata iriyar zabura yayi yana ja da baya, cike da zaro ido da tsoro, baisan loƙacin da ya janye Ameesha gefe ba, ya miƙe tsaye,

Bakin sane ya shiga rawa wajen son ya kira sunan ta, amma sai mamar mamar da baki yake yakasa faÉ—a, ai tunkan yace wani abuma, ta faÉ—a kansa ta rungume sa, tana fashewa da wani irin kuka wanda ita kanta batasan dalilin saba,

shikam mamaki da shiga É—imuwa ya hanasa yarda dan gani yake kamar gizo ne shi kaÉ—ai yake kallon abun dake faruwa,

Tana kuna ta kuma kiran sa, Sai yanzu yasamu damar ɗaga hannun sa a hankali ya ɗora duka hannu wansa akan ta, ganin bata ɓace bane yasa yafara tunanin to kode ba gizo bane,

Yana rungume ta suka sauke ajiyar zuciya a tare har cikin zuciyar sa saida yaje wani sanyi,

Shima cikin sanyin muryar yace "Norry, MY DEEYA!

Ɗagota yayi daga jikin sa, ido cikin ido suka zubawa junan su idanu sunayiwa juna kallon ƙurilla dan kowa ji yake kamar a mafarki,

Tattaro maganar sa yayi yace "Norry kece da gaske ko gizon da kika saba yi min ne,  Dan Allah kar ki kuma tafiya kibar Ni kitsaya ko a hakane ko ni kaɗai ne idan ka kallon ki, Please my Deeya kar ki tafi please......, yana faɗar haka yakuma jawota jikin sa ya rungume ta, shima yana sakin kukan,

Cikin kukan tace "Norry nice ba gizo bane, nuna gani nake kamar gizo kake nin, Norry a kace min ka mutu, ni daman nasan bazaka taɓa tafiya ka barni ba, dan Allah ka tsaya muci gaba da rayuwar mu kar ka ƙara yin nesa, dani nima ina tare da kai babu inda zan ƙara zuwa inbar ka,

Jikin sa har yana karkarwa wajen ɗagoya ya ƙara ganin ta da kyau jin tana magana hakan yasa yafara tabbatar wa kansa da ba gizo bane gaskiya ne,

fuskar ta ya kamo a tafi kan hannun sa ya shiga goge mata hawaye yana girgiza kai yace "nima haka aka ce min, kullum da tunanin nake kwan nake wuni komai baya min daɗi aduniyar nan, babban burina bai wuce ace nasanya ki a idona ba, ina taƙaici da baƙin ci aduk ranar da na wayi gari na wuni nakai dare ban sanya ki cikin idona ba, hakan ba ƙaramin ɓatan rai take ba, nima zuciyata bata taɓa bani kin tafi ba, ni nasan zaki dawo gare ni mu cigaba da rayuwar mu tare da Babyn mu,

ÆŠan baya taja da sauri cike da jin daÉ—in tace Babyn mu, tace "Babyn mu fa kace kana nufin itama tana raye bata mutu ba,

Murmushi ne ya kuɓuce masa ganin yanda tayi tana tambayar, jinjina mata kai yayi, sannan ya juya ya kalli inda Ameesha take, tana gefen su amma ko lura da ita basuyi ba hankalin su yana kan na juna,

Da hannu yayi mata nuni da inda take yace "ga Ameeshan ki,

mayar da kallon ta tayi ga kan Ameesha, tabbas kallo É—aya tayi mata ta gane hakan dan ga kamanni Norry É—in tanan a fuskar ta, wani irin daÉ—i da farin ciki wanda tafi na farko shi taji ya ziyarci zuciyar ta,

BuÉ—a mata hannu tayi alamun tazo gare ta,

Hakan da tayi sai ya tunawa Ameesha loƙacin da mahaifin ta yadawo shima haka yayi mata,

Takawa ta fara yi hankali dan itama jikin ta duk a mace yake ga fuskar ta da tagama wankewa da hawaye, tana zuwa ta faÉ—a jikin ta suka rungume juna suna,

Kallon inda Abban Ameesha yake tayi sai shima tayi masa alamun da ya taho yazo,

Zuwa yayi ya haÉ—asu gaba É—ayan su ya rungume su Ameesha na tsakiyar su, sun daÉ—e a haka kafin suka saki juna kowa yana farin ciki da kuma mamakin yanda hakan ta kasan ce,

(Tsaya wa cigaba da bayyana muku tsatstsan halin da bayin Allahn nan suka kasance aciki ɓata loƙaci ne, andai yi abun da ya samu)

Nan suka ƙara riƙe juna suna shirin cigaba da ƙara wasu maganganun,

Meer ne yayi gyaran murya dan ya fahimci kamar idon su ya makan ce basa ganin kowa a gun, kansu kaÉ—ai suke gani a cikin falon,

"Hmmm nace ba kunmanta da sauran ne?

Baba ne yace "a'a rabu dasu mu ai inajin duk ba ason ganin mu sai mu koma inda muka fito,

Sai loƙacin Abban Ameesha yaga Baba, dan shi har ga Allah bai kula dashi ba sai yanzu, kunya ce ta kamasa, ƙasa yayi da kansa yaje gurin Baba ya tsugunna har ƙasa yace "Ayi haƙuri Baba, ban kula bane, ashe duk tare kuke,

Baba ina kuka shiga tsawon loƙacin nan, duk munyi tunanin kun mutu ashe kuna raye,

Kamosa Baba yayi ya miƙar yace muna raye Babu abun da yasame mu, fatan munsame ku lafiya, nima banyi tunanin kana raye ba,

Dadda ba gefe sai faman zubar da ƙwalla take, loƙacin da Abban Ameesha ya tafi gurin Baba, ita kuma Ameesha sai taja maman ta zuwa gurin Dadda dan itama sai yanzu taga Daddar, farin cikin tane ya ƙaru da ta ƙara ganin mahaifiyar tata, anan ma sai da suka sake yin kuka duk wanda yagansu cikin halin da suka kasan ce sai ya tausaya musu,  dan abunne banma san yanda zan kwatanta muku, abunne ya zowa kowa unexpected basu taɓa tunanin saba,

Nan aka samu kowa ya zauna sannan aka fara gaggaisawa da su Maama, da Papa, a loƙacin kuma Meer ya fita yaje ya taho da Ummyn sa da sarki Abuuu, suma zuwa sukayi kowa da kalar nasa al'ajabin najin yanda abun ya kasance,

Duk wannan hidundumin da ake Baba da Dadda basuyi magana ba, sakamakon ɗauke kan da Baba yayi ya nuna kamar ma besan da ita agun ba, hakan kwa ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba, suyi shekar da shekaru basa tare amma yazo inda take ya nuna kamar ma besan ta ba, duk da tana ta kallon sa idan suka haɗa ido ma sai ya kuma haɗe rai ya juyar da kansa, abun ya tsaya mata arai duk sai taji takasa sukuni,

Nan suka sake buÉ—e sabon babin hira, tun ana koke koke har aka dawo murnar nuna farin cikin ganin juna,

Abban Ameesha kam ko kunya yabi ya tattare a jikin Norry ɗin sa, ya kamo hannun ta ya riƙe gam kamar ance masa za a kwace masa ita,

Dadda ce ta kasa jurewa, cikin ɗan hasala, tace "wai ni me ake nufi dani ne, malam ko nayi maka wani abunne naga sai wani haɗe rai kake yi sai kace baka san dani ba agun, 

kowa maida hankalin sa yayi kansu, ga mamakin su amma sai sukaga Baba ya kuma haɗe rai tare da ƙara kawar da kansa, suma kuma sai yanzu duk suka fahimci hakan tunda suka zauna basu ga sunyi magana ba, a tsakanin su,

Abban Ameesha ne yace "Baba lafiya me yake faruwa?

Shiru Baba yayi bai basa amsa ba, yana me ƙara jin abun dake ƙasan zuciyar sa na ƙara taso masa,

A gaba suka sakashi, akan ya faɗi dalilin sa amma yaƙi Dadda harda su kuka,

Dadda ce ta miƙe cike da haushi ta goge hawayen, tace "To sai me inbaka kulani, suɗin ma ai da kasani baka kulasu daka sani ma baka dawo yanzu ma zaka iya tafiya ai ba wani yace kazo ba, me yasa ma kadawo,

Miƙewa Baba yayi shima cike da hasala, yace "ai badan ke na dawo ba ko angaya miki duk tsawon loƙacin da muka ɗauka bansan inda kike ba,
Chapter 86 · 0% Book details