Sashe 20
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Mom ma ta ɗora da cewa naga alamar yaron nan baida hankali fa, yakamata kayi wani abun yanzu dai munsamu mun tsira ba tayanda zaiyi ya shigo nan amma dai kasan yanda zakayi damu dan nasan ba barin gidan nan zaiyi ba, tana gama faɗar haka Rasheeda ta ɗora dacewa...
"Dady wai allurar mai kasa akayi mishi gashi nan yakoma kamar mahaukaci Dady ka cuceni maiyasa zaka saka ayi masa alluarar da zata cutar dashi yanzu ga abun da ka jawo mana nan duk da nasan halin sa amma da bakayi masa haka ba da ba abun da zaisa ya koma haka gaba É—aya ya canza kamanni ya koma kamar wani dod......,
Tsawa Dady yadaka mata yace "ya isheki haka dame kikeso inji da kukan ki ko da maganganun ki ko kuma da halin da muke ciki, idan zaki iya fita ki ɗauko wayar tana can falo kije ki ɗauko idan kuma ba haka ba kada wanda ya ƙara min magana anan, ya faɗa cikin ɓacin rai da borin kunyar abun dake faruwa dashi agaban ƴarsa ga kumatunsa duk shatin hannun Meer ga gefen bakin sa har ya ɗan kunbura saboda bugewar da yayi da jikin kujerar,
Mom da taga abun ba mai ƙarewa bane bata bi takansu ba, ta ɗauki wayar ta da sauri ta lalubo wata number ta danna mata kira ana ɗagawa tace "mustapha kana ina ne, banji mai akace mata daga can ba, tace to kabar ko mai kake kazo gida ba lafiya, kataho da ƴan sanda, akwai matsala, da sauri Dady ta ƙwace wayar daga hannun ta yace ke mahaukaciyar inace zaki kira mana ƴan sanda cikin gidan nan, angaya miki shiɗin ƙaramin mutum ne idan aka tambayi dalilin zuwan sa nan ɗin kina da hujjar da zaki kare mune kina abun faɗa musu, wannan shashan cine, yana gama faɗa mata haka yakara wayar a kunnen sa yace kar kasake ka kira wasu ƴan sanda, kajini koh! yafaɗa tare da kase wayar,
Ya wurga mata ita ajiki, yana dafe kansa yana furzar da iska ta bakin sa, yana tunanin ta yanda zai sama musu mafita wannan yaron yabar gidan batare da ga taɓa lafiyar su ba, duk da yana tunanin mai yake faruwa a falo har yanzu bai biyo suba, Allah yasadai ya fita tunanin hakan yasakashi zuwa wajen window yaga ko ba motar sa da suka shigo da bata nan, amma yana keƙawa sai yaga wayam babu motar, wani irin sanyi yaji aransa, cike da farin ciki ya juyo yana kallon su yace "Alahamdulillah ya tafi wallahi ya tafi amma Allah ya taimake mu daman nasan tunda muka rufe ƙofar nan bazai iya shigowa ba sai hankalin ku ta kwanta ya tafi, yana faɗa musu yana buɗe ƙofar ɗakin fita yayi dan ya tabbatar wa da kansa, tagani da idon sa, lallaɓawa yayi ya fara leƙawa yaga basa ciki har sauran mutane, amma duk da haka bai yarda ba saida ya fito har waje daga nesa ya tambayi mai gadi shin mai ya buɗewa musu ƙofa ne sun fita yace masa eh yanzu suka fita, sosai yaƙara jin daɗi aransa sannan ya koma cikin gidan......,
   ***************************     Â
Loƙacin da aka fito da su Ameesha tafiya kawai suke basu san inda suka dosa ba, dan tun suna hira har suka dawo yin shiru suka fara gajiya da hirar dan a ƙalla sunkai kusan awa ɗaya suna tafiya, Amra sarki surutu itace tacewa drivern wai ina zai kaisu shiru yayi mata baice mata komai ba dan Meer yana sa yace masa komai zasu tambaye sa kar yace komai kawai yaci gaba da tafiya har sai yace masa ya dawo gida sannan zai juyo ya dawo gida daman ba saƙon da zasu karɓo kawai yayi tarkone da fitar tasu shiyasa ya aikasu kuma gashi anzo an ɓata masa komai,
Bayan Meer ya fita daga gidan wayar sa ya ɗauka da yaganta inda ya barta basu ɗauki komai ba, daddingin number tasu yafara bi yana ganin inda location yake nuna masa, gudu kawai yake kamar zai tashi sama dan yana tunanin ma wataƙil wani abun ya samesu ga, ga inda alamar take nuna masa kafin yaje gurin wajen tazarar kilo mita hamsin ce kafin ya tadda inda suke,
Ƙure gudun sa yayi har ƙarshe Allah ma yasoshi babu mutane da yawa akan titi dan haka yasamu damar gudu yanda yake so yana ganin mota tundaga nesa zai fara danna horn abasa guri yana zuwa ya wuce,
Sudai suna baya suna addu'ar kalmar shahada dan sun riga sun saddaƙar da kashe su yake shirin yi kawai dan wannan gudun ya wuce na hankali.......,
Aɓangaren Meer kam yana sane ya taho dasu dan zaiyi amfanine dasu wajen binciken sa na gaba shiyasa ya taho dasu, dan ya riga a buga alamar tambaya akan Dady saboda yana zargin wani abu akansa saboda haka ne ma ya rabu dasu bai mishi komai zai dawo wajen sa daga baya,
Batare da ya kalle su ba kuma bai daina gudun da yake ba yace dasu zamu je wani guri daku duk abun da kuka ga ya dace kuyi zamuyi magana daku zuwa gobe idan kun ban haÉ—in kai zaku tsira idan kuma kuka bijire min kunsan sauran,
Da sauri har suna haÉ—a baki wajen cewa "in Allah ya yarda komai kace muyi maka zamuyi indai zaka barmu da ranmu koma wani kake so mukashe maka wallahi zamuyi,
Banza yayi dasu saidai ya girgiza kai kawai yaci gaba da tafiya aransa yana jin daÉ—i yasan daman bazai sha wahala dasu a shiyasa yake son haÉ—a kai dasu...........,
  *Su Ameesha*
______Suna cikin tafiya wata motar tazo tasha gaban su, gaba É—ayan su a tsorace suke kallon motar har driver É—in saida ya tsorata saboda shikansa baisan da zuwan motar ba,
Suna cikin haka nacikin motar suka buÉ—e suka fito, wajen tasu suka matso cikin tsawa sukace duk su firfito daga cikin motar har driver É—in suka fito,
Ameesha ta rirriÆ™e Azeema cike da tsoro Æ™walla har tafara cika mata ido, tace "kinga abun da nake gaya miki ko wallahi sune Saida nace masa kar mu tafi mu kaÉ—ai amma yaÆ™i ji, Cikin Æ™asa Æ™asa da murya Azeema tace ke wai meye haka baza ki nutsu ba, Â
Amra da Hamra suma suna riƙe da hannun su duk sun tsatstsaya suna kallon mutanen da suka ce su fito,
gadan gadan mutanen sukayo kansu kamar zasu dake su sai kawai sukayi kan Ameesha ɗaya daga cikin sune ya damƙo hannun sa a hannu ta sannan ya juya ya kalli sauran yace "wannan ce ko?
Ɗaya ya kaɗa masa kai na gefansu kuma yace ai su biyu ne ita da wannan ce, wanda ta riƙe mata hannun yace banda ita ɗaya akace,
Kuka Ameesha tafara yi tana jan hannun Azeema, da su Amra, shi kuma mutumin yafara janta kuka take tana cewa ku taimakamin kar kubari su tafi dani,
ganin haka yasa drivern yayi kansa da niyar ƙwatar ta amma sai sauran suka riƙeshi gam, suma su Hamra cikin kukan suka fara haɗa mutanen nan da Allah su saketa har tsugunnawa sukayi suna roƙon su amma basu kyale taba suka ci gaba da janta, mutumin yana daf da shigar da ita yaji saukar dutse abayan ƙeyarsa, da sauri yasake ta yana dafe gun da yaji zafi sosai har ma jini yafara fita,
Da gudu Azeema ta ƙara zuwa ta wawuro wani ƙaton dutsin da ta ɗaga sa da ƙyar tayi kan sauran zata jefa musu da sauri suka fara ja da baya gudun kar ta sami wani acikin su,
Ameesha ta samu damar barin wajen da gudu ta koma gurin su Amra amma sai wani yaƙara riƙeta zai fara janta,
Kamar mahaukaciya haka ta koma taƙara nufarsu tana zazzare ido tace "wallahi duk wanda yaƙara taɓa ɗaya sai na fasa masa kai,
ba shiri duk suka fara ja da baya ai da gudu Amra ta ƙara zuwa ta ɗauko wasu dutsina da yawa a hannun ta, tafara jifansu dashi, duk baya mota suka fara ɓuya, dan su Hamra ma duk ɗaukan duwatsun sukayi suka fara jifan su dashi,
Ganin sun korasu driver É—in yayi saurin shiga motar yace suyi sauri su shigo su gudu,
Da sauri Azeema tafara tura Ameesha ciki sannan ta tura su Hamra sannan itama ta shiga,
Driver yana shirin tayar da motar kenan yasaka hannun sa gurin muƙullin motar sai yaji babu muƙƙuli ajiki da sauri ya juya yafara dudduba shi aƙasa ko ya faɗa amma bai gansa ba,
Amra tace wai me kake jira dan Allah mutafi gasu nan fa sun fara tahowa wajen mu Ameesha ma ta ɗora da cewa muje mutafi, gaba ɗayan su suka fara ɗaga masa hankali kowanne da abun da yake cewa, shi har ya rikice ma ya rasa ta inda zai fara neman muƙƙulin ga surutun su da yagama burkitashi, idan ya ɗaga kai yaga mutanen sun kusa zuwa wajen su, sai yaƙara shiga tashin hankali,
Cike da tashin hankali ya juyo ya kalle su murya na rawa yace "dan Allah kuyi haƙuri narasa muƙullin motar ko da wanda yagan sa acikin ku,
Gaba ɗayansu suka ƙara tsorata jin muƙulli wai ya ɓata, basu ankara ba suka ji bugun ƙofar su, ta ɓarin da Ameesha take aka buɗe motar, ana buɗewa suka jata suka fitar da ita daga ciki, suna cire ta kuma suka rufe ƙofar gaba ɗayan su suka zagaye motar suka hana sauran fitowa gudan kar suƙara yi musu abun da sukayi musu ɗazu,
Kuka su Hamra suka fara yi suna ƙoƙarin fitowa dan su ƙwace ta amma duk sun daddanne murfin motar sun hanasu fitowa,
Saida suka ga yakaita wajen motar ya buɗe bayan motar yasaka ta, sannan ya dawo wajen su yace ku buɗe musu mu rama abun da sukayi mana dukkannin su sai sun gane kuren su musamman wannan tsinanniyar yarinyar wanda aka fasawa ƙeyane yake wannan maganar,
Buɗesu sukayi zasu fito dasu kokawa suka fara yi dasu, su Azeema suka tubure suka ƙi yarda suyi musu komai kuma suka ƙi fitowa saboda duka suka ringa kai musu suna cizon su suna mintsinin su, sukuma suna famar fito dasu daga ciki amma ba dama,