← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 103

Sashe 62

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin su tafi gida saida Meer yasa suka siyawa Abban Ameesha kaya masu kyau manyan kaya, sannan sukaje wani Hotel ɗin yasa yayi wanka ya canza kayan jikin sa yasa shi agaba ya kuma cin abinci mai rai da lafiya, sannan yace ya kwanta ya huta sai zuwa dare zasu tafi gida shide Abban Ameesha ba haka yaso ba saida ya haɗasa da Allah ma shi bazai iya bacci ba su tafi kawai ya matsu yaga sauran, amma shima Meer ɗin ya hanasa tafiya, dan acewar sa yafiso yaje musu cikin ƙoshin lafiya yanda bazasu tashi hankalin su ba musamman ƴar sa, da ta matsu ta gansa bai kamata ta gansa cikin wani hali ba hankalin ta zai tashi da yawa, (tofa kunji ni da wanga mutum meye damuwarsa da ita bayan cin zalinta da yake")

Babu yanda Abban Ameesha ya iya dole ya haƙura ya kwanta cike da jin daɗin kulawar da Meer yabasa a iya yau,(hmmm bari dai inyi shiru da nace kodai neman fada ake ne Ale Meer na sirikan taka agun siriki) ba shiri kuwa bacci me daɗi ya ɗibesa,

bai tashiba sai bayan sallar magriba sannan ya tashi bayan duk suka haɗu sukayi sallah dan ko masallaci basu je ba, da suka idar Meer yaƙara bashi wasu manyan kayan masu mugun kyau ya saka yasake cin abinci saida ya tabbatar da komai need need sannan suka baro Hotel ɗin,

Dadyn Rasheeda fa jini fara É—urar ruwa dan ganin yanda Meer yake nunawa bawan Allahn nan kulawa da so, yasan idan yagane da saka hannun sa, kashin sa ya bushe dan yasan halin sa sarai baiyi gadon mutunci ba, duk wanda ya shiga hannun sa zai É—anÉ—ana kuÉ—ar sa, dan haka ya fara tunanin guduwa tunda wuri amma yasan idan ya gudu ayau za'a iya zargin sa shiyasa kawai yayi ta wannan zaman a Hotel badan son ransa ba, saidan ba yanda zaiyi,

Meer tun suna hanya yace "a haɗa zama a fada kowa da kowa ya hallara akwai zama gagarumi da za'ayi yana kan hanya yanzu zasu ƙaraso da wani muhimmin abu, anyi anyi yafaɗa yace shide ayi masa wannan alfarma kafin ya ƙaraso dole, Abu da Papa suka amince masa,

Nan danan suka sa aka fara haÉ—a kan muta ne acikin fada,

Ba jimawa motar su meer ta iso cikin masarautar, adaidai wajen fada Meer yasa akayi parking ɗin motar, loƙacin kowa ya hallara acikin fadar zuwansa kawai ake jira,

Meer ne ya fara fitowa sannan yace subari sai yace su fito zai shiga ciki yagani kowa yana ciki.....

Yana shiga cikin fadar kowa ya zuba masa ido mutanen ciki ya shiga bi da kallo ɗaya bayan ɗaya amma har hagama baigan taba, dan haka saikawai yace afuwa ina dawowa kowa ya ƙara shiryawa wanda bai wanke ido ba ya wanke wanda kuma ya wanke ya ƙara wankewa yanda zaifi gani da ƙyau, yana kaiwa nan ya juya ya fita yabar su da surutu....,

Koda ya fita bai yi musu magana ba hasalima ba su gansa ba, saboda bata gaban su yabiyo ba,

Can part ɗin ya nufa yana shiga direct ɗakin da yake kyautata zaton nanne ɗakin da take kwana nan ya nufa yana zuwa kuma ya tura ƙofar,

Yana saka ƙafar sa ita kuma tana sako tata daga banɗaki jikin ta ɗaure da towel iya gwiwa, dake ƙarar tata ƙofar baisa taji tasa ba dan haka bata san ma da shigowar saba, ta ƙarasa fitowa daga ciki,

gaba wardrobe É—in ta taje dake sauri take tagama shiryawa ta fita cikin fada saboda farko cewa tayi bazata ba sai kuma daga baya kawai taji tana son zuwa gashi rabonta da wanka tun jiya shiyasa ta shiga tayi yanzu da niyar tana fitowa sai taje taga uwar da zaiyiwa mutane da yasa aka haÉ—asu,

Sanin ita laɗai ce babu kowa a part ɗin bare kuma ɗakin sai kawai ta saki towel ɗin ya faɗi ƙasa yanda zata fi saurin shiryawa...,

Pant ta ɗauka ta fara sakawa sannan ta ɗauko bra tana zurota ta baya zata fara saka maɓallan ta sai ta suɓuce ta faɗi ta bayan ta saboda saurin da take cike da sakin tsaki ta juyowa a fusace ta tsugunna takai hannun ta zata ɗauka kenan sai taga bra ɗin akan ƙafar mutum a razane ta ɗago dan batama ɗauki bra ɗin ba,

Tana tozali dashi ta wangame ɗan ƙaramin bakin ta zata kurma wani mahaucin ihu saboda razanar da tayi,,

Sauri yayi ya riƙota ya ɗora hannun sa akan bakin ta ya toshe mata baki tare da haɗeta da jikin wardrobe ɗin ya hanata koda motsi bare kuma ta samu damar yin ihu......,✍️✍️

(Wayyo Allahn mu yau ina zamu saka ranmu angane mana komai😭😭)
[15/11, 10:53 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                         *_🅿️37_*

____
Sauri yayi ya riƙota ya ɗora hannun sa akan bakin ta ya toshe mata baki tare da haɗeta da jikin wardrobe ɗin ya hanata koda motsi bare kuma ta samu damar yin ihu...

........ido yagama raina fata dan ƙafarta ma neman kasa ɗaukar ta take, dan ji tayi gaba ɗaya jikin ta ya ɗauki ɓari, ta shiga karkarwa,

yana jin yanda jikin ta yake shaking sai kawai ƙara riƙeta da kyau, yana bin fuskar ta da kallo ga kuma hannu sa dake kan bakin ta sai mutsul mutsul take dashi tana son ƙwace wa amma ya hanata damar yin hakan,

Ƙafar sa ya miƙa ya jawo bra ɗin da yatsun ƙafar sa ya ɗauko ta, ya ɗago ya riƙe da ɗayan hannun sa da ya rufe mata baki,

yunƙurin ƙara yin magana tayi sai yasa ya tsansa ya ɗannan mata baki, take hawaye suka fara saukowa daman sun cika idon ƙiris suke jira,

Ɗan matsawa yayi kaɗan daga kusa da ita hakan yabata damar saurin tsugunnawa tasa hannuwan ta duka biyu tana rufe ƙirjin ta gashi babu wani abu da zata ja ta rufe jikin, wani irin haushin shine yakama ta ji take kamar ta rufe da duka, aranta take ayyana ashe bayan mugunta harda iskanci inbanda ɗan iska waye zaishigo guri yaga mutum ba kaya kuma ya tsaya yaci gaba da kallon sa,

Ganin bashi da niyar barin wajen yasa ta rufe idon ta tace "dan Allah ka fita tafaɗa tare da sakin kuka dan baƙaramin taƙaicin hakan take ji ba,

Shikam harɗe hannuwan sa ma yayi yana watsa mata wani irin kallo, ga kuma bra ɗin a hannun sa, maganar da tayi ce ta dawo dashi cikin hayyacin sa, shi abun ma kusan dariya yaso yabashi yanda duk tabi ta tsorata kanta sai wani faman karkarwa take tana wani rurrufe ƙirji shi baiga ma abun rufewa dan tunda ya shigo ma shi baiga abun kalla ba kodan idon sa bai sauka akai bane oho, wani tunanin ne ya faɗo masa sai kawai ya canza fuska tare da gyaran murya yace "ke!!!

"Ni dan Allah ka fita wai wannan wane irin iskanc..., Saurin rufe bakin ta tayi tunawa da wanda take magana dashi ba sa'anta bane,

jinjina kai yayi ganin zata wuce gona da iri, aransa yake ta maimaita kalamar wane irin iskanci ne watakon shi take kira da ɗan iska aikwa badan yanayin da yake ciki ba da ya koya mata hankali da wannan kalmar, taci darajar mahaifin ta kawai yanzu yana cikin farin ciki bayason abun da zai ɓata masa rai, amma zaiyi saving ɗin kalmar nan tata,

miƙa mata bra ɗin yayi yace "tashi kisaka, kasa karɓa tayi dan batajin zata iya ɗagowa bare kuma ta karɓi brazia a hannun sa,

"In saka miki kenan?

Da sauri ta girgiza kai amma duk da haka bata É—ago ba,

"Ok oya ungo. Ya faɗa yana ƙara miƙa mata amma taƙi karɓa,

tsugunnawa yayi a gaban ta, suna facinɗin juna, ƙasa ƙasa yace "bazan ƙara yi miki magana ba idan baki sakaba zakisan sauran,

Jin furucin sa yasa tayi sauri zuro hannu zata karɓa sai kawai ya janye tare da riƙo hannun nata, bazato ba tsammani kawai taga ya miƙar da ita tsaye,

"Wayyo na shiga uku tafaɗa tana ƙara rufe ƙirjin ta,

Hmm yace, tare da juyata ta kalli wardrobe ya haÉ—a bayan ta ajikin sa,

Adaidai kunnen ta yace "ki tsaya kar ki ɓatan loƙaci idan kuma kikayi min garda Zan hukunta ki, sannan duk abun da zanyi karkisake kiyi min magana inba ni na baki dama ba kina jina!? Yaƙarsa maganar da ɗan daka mata tsawa...

Itakam tsoro ya hanata magana da sauri ta É—aga masa kai, dan tasan idan tayi masa gardama kamar yanda ya gargaÉ—eta, babu abun da bazai iya aikatawa ba kaÉ—an daga cikin aikin sa....

Hannun ta ya ɗaga daga kan ƙirjin ta, ya zuro hannun bra ɗin ɗayan ma haka yayi mata yasako, batare da yana ganin kalar Brest ɗin ba ya jawo hannun ya ɗora su akan kafaɗa yanda dai akesa braziar sannan ya saka mata maɓallan a nafarko yasaka sai yaga kamar yayi sakoko sai ya mayar mata shi na ƙarshe,

Itadai ta miƙa lamarin ga Ubangiji dan abun yafi ƙarfin ta, ta tsaya tana ganin ikon Allah,

Wani abun mamakin ma sai kawai taga ya miƙa hannun sa yajawo wani lace pitch and light blue acan ƙasan kayan ta, wanda tanama tunanin sau ɗaya ta taɓa saka sa,

waresa yayi doguwar rigace da É—an kwalinta, tana a haka baice ta juyo ba ya zuge zif É—in yasaka mata, ba yanda ta iya dole ta basa haÉ—in kai ta zura hannun rigar,
Chapter 62 · 0% Book details