← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 103

Sashe 78

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daram...Daram Daram gaban wasu yabada sauti loƙacin da suka shigo ciki kollo ɗaya wasu sukayi mata suka gane ta amma kokonta da rashin yarda yasa basu gasgata hakan ba,

A tsakiya suma suka tsaya Bossay sai ya koma bayan su, Meer kuma ya ƙaraso gaba inda suke,

Sunkuyar da kai matar tayi dan ita kanta ta gama shan jinin jikin ta,

Zagayawa Meer yayi ta bayan ta dan yabawa kowa damar samun ganin ta da kyau,

A hankali ya ɗora hannun sa akan niƙab ɗin, a hankali ya shiga ɗaga niƙab ɗin har yagama yaye sa gaba ɗaya fuskar ta ta bayyana a bainan nasi,

"NOOOO........!!!!! ya faÉ—a tare da yanke jiki ya faÉ—i agun,

Cike da tashin hankali da mamakin da yagama kashe ta a tsayen da ta miƙe, loƙaci ɗaya jikin ta ya ɗauki ɓari, hawaye har yagama wanke mata fuska dan kamar famfo haka suke sauka daga idon ta😭😭😭😭😭😭😭

Hannu ta ta É—aga tashiga nuna ta cikin wata iriyar murya da kanaji kasan tana cikin tsantsar damuwa da tashin hankali,

Muryar ta har saƙewa take ga kuma karkarwa da take ba iya muryar bama har jikin karkarwa suke,🥺

Cikin sarƙarƙiyar muryar ta wacce da ƙyar ta iya buɗe baki, ta tattaro kalmomin da suka maƙale mata a maƙogaro cikin rarraba sunan tace... "D..D...DA...D...DDAA...!!!!!!!

Tana faɗa ta saki wata iriyar ƙara tare da zubewa agun, ɗif ta ɗauke wuta tare da zama sumammiya,🥺🥺.........

To nima dai dole in ɗauke wuta anan gurin dan al'ajabi bazai bari in iya ci gaba da ɗauko muku rahotan nan ba, sai an kawon ɗauki da yayyafin ruwan sanyi ko zan samu in farfaɗo, zuwa gobe........,, Kuma Allah yasa idan na farfaɗo acemin abun da naji ba gaskiya bane mafarki nake, kunji dan Allah ku gayan gaskiya kodai nice banjiyo daidai ba ne..🥺🥺😭

  
[19/11, 10:23 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                    *_🅿️46_*
                  

...Cikin sarƙarƙiyar muryar ta wacce da ƙyar ta iya buɗe baki, ta tattaro kalmomin da suka maƙale mata a maƙogaro cikin rarraba sunan tace... "D..D...DA...D...DDAA...!!!!!!!

Tana faɗa ta saki wata iriyar ƙara tare da zubewa agun, ɗif ta ɗauke wuta tare da zama sumammiya,🥺🥺.........,

Da sauri Dadda tayi kanta zata taɓata, Meer yayi saurin tare ta, yana binta da wani mugun kallo yace "kar ki kuskura ki taɓata, ko kinaso ki ƙarasa kashe tane?

Yayi maganar yana juyawa yayi saurin ƙarasa wa gurin Ameesha ya ɗago ta, ya ɗorata ajijikin sa,

Can ɓangaren kuma Abuu da Papa sukayi saurin komawa gurin Abban Ameesha da shima yake a sume,

Da sauri wasu daga cikin fadar sukayi saurin miƙawa Meer ruwa, da su Papa,

Meer ne ya yayyafawa Ameesha amma bata farfaÉ—o ba, su Papa kuma suna yayyafawa, Abban Ameesha ya farfaÉ—o,

Yana farfaɗowa ya fara bin su Papa dake tsatstsaye akan sa, yana kallon su ɗaya bayan ɗaya, can kuma saiga hawaye  ya fara sakkowa ta gefen idon sa, ko motsi yakasayi, ya ƙame kawai a kwancen,  yana kallon su, yadai farfaɗo daga suman da yayi amma har yanzu bai dawo daga shock ɗin da ya shiga ba,

Ganin kamar baya cikin hayyacin sa yasa, Papa ya fara yi masa addu'a yana tofa masa, sannan ya kamo sa ya zaunar da shi, da kyar aka samu ya dawo cikin hayyacin sa, amma yana dawowa ya fashe da kuka, yana cewa dan Allah idan mafarki nake ku tasheni daga wannan mummunan mafarkin,

Dan Allah kuce min abun da naji nagani ba gaskiya bane, dan Allah ku taimake ni ku gaya min gaskiyar abun dake faruwa, danna san ba daidai nake jin komai ba, ƙwaƙwalwa ta tafara samun matsala, ta fara jiyo min wasu abubuwan da ba daidai ba,

Shiiiiit... Ya isa haka ka kwantar da hankalin ka dan Allah kadaina waɗannnan maganganun duk abun da kaji kuma ka gani, babu ƙarya aciki, komai gaskiya ne dan haka ka kwantar da hankalin ka kar ka sanyawa kanka wani ciwon. Cewar Abuu yafaɗa yana me rarrashin ƙanin nasa,

Ameesha kam har zuwa yanzu bata dawo hayyacin taba, Meer yana kanta amma taƙi ɗaukan ta yayi yamaida ita can bayan kujerar karagar mulki, ya kwantar da ita agun,

Sannan yaƙara yayyafa mata ruwan tare da kamo hannun ta, cikin tafin hannun ta ya ɗora nasa yafara murza mata yana hura iska ajiki, har da su tafin ƙafarta yana murzawa amma duk da haka tayi nisa bata motsa ba,

Cikin ɓacin rai ya ɗago daga gurin daga inda yake ya nuna DADDA da hannu cikin ɗaga murya yace wallahi idan wani mugun abun yasamera ko kuma ta rasa ranta ta sanadinki, wallahi wallahi sai na kashe ki da hannu nagaya miki, duk abun da yasame su sai kingane kuranki,

Wani irin kuka me tsuma zuciya Dadda ta fashe dashi, tare da tsugunnawa agun, cikin kukan tace wallahi ni ban aikata komai ba, babu abun da nayi musu, ku barni inje wajen jikata, wallahi ina ƙaunar ta,

wani irin ƙaton abu Meer yaji wani abu yazo masa wuya, ya tsaya watakon ɗan rainin hankali tasan me ta aikata amma take irin wannan maganar kodan taga bai taɓa ta bane har yanzu shiyasa tasamu bakin yin magana,

A fusace ya dawo wajen yazo gaban ta, yana binta da wani irin matsiyacin kallo,

ÆŠan tsugunnawa yayi tare da É—ago kanta cikin wata iriyar murya yace "bakiyi musu komai ba, kike faÉ—a ko,

Yanda yayi mata maganar a hankali yasa tayi tunanin ko ya yarda da abun da ta faÉ—a,

Sai kawai ta É—aga masa kai, tare da cewa "EH...

Girgiza kai yayi kawai tare da miƙewa tsaye, cikin yanayin rainin hankali da gatse, yace mata,

"Ok taso kike to, na yarda,

Da saurin ta ta miƙe, saidai tana gama miƙewa bazato ba tsammani taji wani irin gigitaccen mari wanda saida yasa tayi juyi ta dawo,

Zai ƙara mata wani kenan, Abban Ameesha yayi saurin riƙe shi yace "dan Allah kar rabu da ita, bakaji me tace ba, bafa ita bace ni nasan daman umma bazata taɓa yi mana haka ba, kundai saɓa bincike ne amma ni nasan ba ita bace,

Cikin kuka Dadda tace "Eh, Eh bazan taɓa yi muku haka ba, ka ganar dashi gaskiya kagaya masa ko ni wacece, nice mahaifayar ka, da na riƙeka, tun kana yaro, nice uwar Nooryn ka, taya zan iya cutar daku, kaifa sirirkina ne, da zan cutar daku ai duk da bankasan ce cikin wannan halin ba, amma tsawon loƙaci nakasance cikin talauci na zauna, daga ni sai ƴarka, sanadin ka narasa ƴata na rasa mijina, na rasa dangina, duk san saboda, saboda shigowar ka rayuwar mu, amma duk hakan bai isaba, sai kun zargeni me yasa zaku min haka ne yasa? Ta faɗa tana fashewa da kuka mai ban tausayi,

Rungume ta Abban Ameesha yayi cike da tausayin ta, yace ni nasani, bazaki yi hakan ba, ni bazan taɓa yarda ba,

Raba jikin sa yayi danata, yana kallon Meer yace "dan idan danni ake wannan tuhumar tata, abar wannan maganar koma itance na yafe komai da komai tunda na haɗu daku ni yanzu duk wata dukiya bata da amfani awajena burina kawai inkasan ce tare daku cikin farin ciki,  dan Allah abar maganar nan,

Haɗe rai Meer yayi, yace "Uncle wannan wace irin magana ce kake, taya kake tunanin sharri ake mata ko ƙazafi,

Idan sharri akeyi mata, me ya fitar da ita daga cikin gidan nan? sannan me yasa zata bar ƙasar? Meye haɗin ta da wannan mutumin, kuɗaɗen dake cikin jakar ta, waya bata su?

Uncle kayi tunani, naji indai ta amsa duk waÉ—annan tambayoyin da nayi mata, ni kuma zan yarda za'abar ta babu wanda zai kuma tada zacen tunda haka kace,

Shiru Abban Ameesha yayi amma duk da haka zuciyar sa takasa gasgata hakan,

Cikin kuka tace, "wallahi ni banyi haka dan saboda wannan case ɗin ba, daman tuntuni ina da shirin barin gidan nan dan banga me nake muku ba shi yasa na yanke shawarar nesan ta kaina da ku, nasan idan nagaya muku baza ku taɓa bari na in tafi, ni kuma nagaji da rayuwar gidan, sannan wannan mutumin ni bansan me ya aikata muku ba, bansan shine wanda kuke nema, maƙocin mune shine yake taimaka mana loƙacin da bamu dashi, shiyasa yanzu da natashi tafiyar naje na samesa nagaya masa matsalata yace zai taimakamin, sannan ya haɗani da wannan matar yace idan nashirya inyi mata magana, shiyasa ka ganmu tare amma ni bansan shine akwance a asibiti ba, kawai nagansu tare shiyasa muka shirya tafiyar tare,

"Kaji ko? kaji abun da tace rashin fahimta ce kawai,

"Oh da gaske, gaskiya ne na yabawa ƙoƙarin ki,

"Tom aje mun yarda da hakan, kafin a bar maganar ina zuwa,

Wata waya ya zaro tare da nunawa Abban Ameesha yace "zaka iya faɗo min number ka, ta layinka da ka taɓa yi,

"Cike da fara gajiyawa da tambayoyin da yake tayi, yace masa "Eh, yafaÉ—a tare da karanto masa,

Nuna masa wata number yayi da akayi saving É—in ta da Ummana, yace wannan number waye,

Kaɓa yayi yana dubawa tare da ɗan karantatawa, sai ya ɗago yace wannan number tace mana gashi nan nasaka Ummana, a ina kasamu Sim ɗin,

Karɓa Meer yayi tare da dannawa number kira saikwa ga ringing a cikin aljihun sa, sai ya zaro wayar yace ka gani, to number ta har yanzu tana aiki, mu kuma anan ta nuna mana ko wayar ma bata da ita alhalin tana sarrafa ta a ɓoye,
Chapter 78 · 0% Book details