← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 103

Sashe 38

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daga nan aka sanar da mutane cewa gimbiya ta mutu kawai da mutuwar aka sanar dan wata gawa muka samu a asibiti da ta mutu aka rasa dangin ta mukuma mukayi amfani da ita sai aka hana kowa ganin ta, tare da ƙullewa kowa baki, har aka manta da maganar ta,

Bayan munfitar da gimbiya muka ƙara samun wani muka ce yabita ya buge ta ta mutu ita da yaron, shine ya karɓi kwangilar, kamar yanda muka tsara yaje ya bugetan daga nan kuma ya kira motar asibiti su ɗauke ta saida yace mana ta mutu loƙacin da yakaita asibitin daman kuma bai tsaya ba muka ce yana kaita ya gudu kar ya tsaya yabar ta anan,,

Tundaga nan hankalin mu ya kwanta ko ince hankalin su ya kwanta danni har loƙacin bawai da zuciya ɗaya nake zaune dasu ba, inayi ne kawai dan ingano inda ƴaƴana suke, inda nayi tawa son zuciyar kenan,

Bayan komai ya lafa kuma ta ɓangaren gimbiya an fara mantawa da babun ta ma a masarauta saboda asirin da akayiwa kowa, na mantar dasu,

daga nan kuma ɗan Fulani ya girma inda sa'adatu tasa aka sanyawa kowa mugunta a zuƙantan su ita da ɗan nata, tunda sarki ya sauka daga mulki yabawa Salahudeen aranar da ya zauna akan karagar mulki aranar komai ya fara canzawa masarautar ma ta canza aka fara gudanar da mulki marar kai da ma'ana mugunta zalunci rashin tausayi rashin imani har kisan kai ma idan takama ana iya yi,

Haka ake ta gudanar da mulkin yayin da cikar burin kowanne mu ya gabato loƙacin kuma asiri yafara warwarewa,
Cikar burin Waziri da matar sa jikan su yazama sarki daga nan sarauta ta dawo hannun su gaba ɗaya, cikar burin Ghali shine a ƴantasa abasa kuɗaɗe da yawa ya koma ƙasar waje, cikar burin hajjaju shine ƴar ta zata auri Sam zata zama gimbiyar masarauta, cikar burin Abdallah (Dady) shine ɗansa zai zama sarki, cikar burin Adama kuma shine ta gano inda ƴaƴan ta suke sannan ta tona asiri a shirmen ta, To cikar burin Ammah (Sa'adatu) kuma ita anata lissafin ma babu duk cikar burin sauran babu wanda zata cikawa burin su acikin su, nata burin kawai taga komai na masarautar ta lalace komai ya tarwatse bata son wani cigaba ko kaɗan da zaizo yasamu cikin masarautar tafi so kullum akasan ce cikin bala'i da masifa da mugunta da zalinci, shine nata shirin.......,✍️✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

     
   
________Shiru tayi bayan ta gama basu labarin tare da dunƙufar da kanta ƙasa yayin da ƙwalla ta cika mata ido,

Gwaggo ce ta miƙe tana sallallami tana hawaye, tace amma wannan yarinya anyi tsinanniy marar albarka, ashe daman ba auren Allah da annabi bane ki shigo gidan nan, uban me muka tsare miki mai Muhammadu yayi miki kike yi masa irin wannan muguntar tun kan kishigo tun kan musan wacece ma ke, ke kika san damu, ni daman banso auren ba tun farko waya sanni ma ko da ƙulle ƙullen ki kika sa aka aura miki, nan gwaggo ta shiga surfo mata masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, harda sun kaiwa Ammah duka. Da ƙyar dai aka samu aka shawo kanta ta haƙura ta koma ta zauna,

Gurinne yaso ya kauraye da haya niya kowa na faÉ—ar albarka cin bakin sa wasu kuma na kuka, irin su momma dan a yau bata ma samu bakin magana ba,

Meer ne yayi ƙoƙarin wajen dakatar da hayaniyar domin ci gaba da jin ta bakin sauran,

Shiri gurin ya ƙara ɗauka, sannan meer ya maida hankalinsa ga Ammah, cike da binta da kallon tsana yace "shugaba ke muke jira munji komai na sauran ba buƙatar su faɗa da bakin su, ta bakin ki kawai muke jira muji, shugabar su,

Yanda yayi mata maganar da rainin hankali tare da harara,

Ammah na jinsa amma sai tayi banza dashi kamar ma bada ita yake ba saima haÉ—e rai da ta kumayi dan daga kallon ta zakasan ba alamar nadama a tattare da ita,

Duk yanda yayi mata magana ƙin kulashi tayi ko ɗagowa ma batayi bare yasa ran zatace wani abu, hakan kwa ba ƙaramin ƙullar da Meer tayi ba, ta kaishi ƙarahe daman yana ɗaga mata ƙafa ne saboda darajar wasu daga wajen amma da tuni ya daɗe da canza mata kamanni,

Cike da fara hasala cikin ɗaga murya mai yanayi da ɓacin rai ya daka mata tsawa tare da kwashe da mari ta gefen fuskarta, yace "zaki yi magana ko sai nayi miki lahani,

Itama kamar wacce ta tsikara ta miƙe tsaye cikin ɗaga muryar tace bazan yi ba ɗin inka isa kasani inyi jaki kawai, marar tarbiya, idan da wanda ya isa agun nan yasakani abun da banyi niya ba, bazan faɗa ba nace bazan faɗa ba ko ubanka bai isa ba karan ƙaɗa miya bare kuma, kabari inyi da waɗancan dabbobin bin ta nuna inda Maama da Papa suke zaune sannan taci gaba da cewa  sune sa'annin yi na ba kaiba, su idan sun cika ƴaƴan akuya suzo su sakan......

Ji tayi ankwashe da wani irin mahaukacin mari ta gefen kunnen ta wanda loƙaci ɗaya jin ta ya ɗauke hakan ya hanata ƙarasa maganar, idon tama saida ya ɗauke gani taga duhu sannan ya baje bayan ƴan sakanni ta dawo ganin haske, saidai bata gama tantancewa ba ta kuma jin wani ta ɗayan ɓarin cike da tsatstsan ɓacin ran da bai taɓa shiga ba Abu ya shiga nuna ta da yatsa yace "kisan a inda kike kuma kisan da waɗanda ba kowace kalma zaki faɗa ba abarki ki kiyaye tunda aka fara abunnan babu wanda ya tanka miki amma har kin samu bakin cigaba da cin mutuncin mutane,

kasa magana tayi dan har yanzu azabar bata gama barin taba, dan saida ta ɗimauce tunda take ba 'ataɓa marin taba bare kuma irin wannan zazzafan da Abu ya sauke mata su,

Meer da shima jira yake yakaimata mugun bugu Abu ya rigasa sai ya haƙura, juyawa yayi ya kalli inda momma take ya ƙara juyawa ya kalli wasu daga ciki, sai kawai ya kama Ammah ya zaunar da ita ta zauna da ɗuwawunta,

Maida kallon sa yayi ga ƴan cikin fadar sannan yace "dan Allah in badamuwa ina son wasu su bamu guri waɗanda bai dace da suji ba wannan sirri ne abun da ya shafe mune dan haka mu zamu ƙarasa jin sauran, ina tunanin taƙi faɗa ne saboda kunyar wasun ku, dan Allah kuyi mana afuwa ku fita zamuji ta bakin ta, baikamata ace kunji komai ba kuma daga bakin ta, shiru yayi yana satar kallon wasu daga cikin su waɗanda daman dan suɗin yayi maganar bazai iya cewa su fita bane kai tsaye shiyasa yabiyo ta nan yasan dole zasu fita dan baza suso su ciga ba da kallon abun da yake faruwa ba, dan yanaso idan suka fita ya ɗan sassamata ya koya mata hankali idan yayi mata yaren da zata gane to dolen ta ta faɗi duk abun da suke so, dan ya fahimci taurin kai gare ta,

Allah sarki momma daman ƙiris take jira dan haka kuwa ita gafara miƙewa daga gurin yayin da take jin wata juwa na shirin zubar da ita a ƙasa tayi saurin riƙe kanta saboda zuciyar ta ta fara bushewa dan ko kukama takasayi abun yakaita ƙarshe,

Mamy ce ta miƙe itama takama hannun ta suka fita daga ciki batare da sun kalli kowa ba, nagun, daman su kaɗai ƴaƴan ta acikin gidan sai jikoki su kuma babu wanda aka shigo dashi gurin,

Sunkai bakin ƙofa kenan zasu fita suka tsikayo muryar ta "tace ku dawo ku zauna cike da raunin murya da loƙacin ɗaya ta canza ita kanta batasan tayi ta ba,

Tsayawa sukayi cak batare da sun motsa ba, saida ta ƙara cewa nace ku dawo ku zauna babu inda zaku sai kunji komai,

Mamy ce ta juyo da ƙyar ta ɗan kalle ta sannan tace "muji komai fa kika ce to mai ya rage wanda bamuji ba, hakan ma ya ishe mu ko so kike kiƙarasa kashemu da ranmu Ammah wallahi nayi da nasanin kasancewar ki uwa agare ni duk wanda yasamu uwa irin ki yayi asara dan haka muma asararru ne munyi asarar uwa dan dake da babu yanzu duk ɗaya ne,

"Ya isa haka kizo mutafi kibar ta Allah zaiyi mana sakaya ranar gobe ƙiyama, ga duniyar nan ai ta isheta riga da wando, cewar momma da har yanzu bata yarda ta kalli inda Ammah take ba,

Juyawa sukayi zasu fita Papa ya ƙara dakatar dasu tare da basu umarnin su dawo su zauna sannan kar wanda yaƙara magana daga cikin su, babu yanda suka iya dole suka koma gurin su suka zauna badan suna son ci gaba da zaman gunba dan ji suke laifin ma kamar ya shafe su tunda za ace mahaifiyar suce,

Karon farko arayuwar Ammah da taji zuciyar ta ta karaya saboda ƴaƴan ta, loƙacin guda taji wani abu nayi mata yawo ajiki, ganin ƴaƴan ta cikin wannan halin da kuma maganganun da sukayi mata hakan ba ƙamin tsaya mata arai yayi ba,
Chapter 38 · 0% Book details