← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 103

Sashe 22

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan an idar da sallar ya dawo  saida yaƙara ɗan dube duben a laptop ɗin har gari yafara haske sannan ya samu ya kwanta......,

_____papa da Maama ne zaune a É—aki suna tattaunawa akan batun fulani,

Maama ta kalli papa tace "to tunda har ta rantse ba ita bace ai ni banga amfanin rufeta ba tana matsayin matar ka, ni aganina kawai afito da ita, idan wani hukuncin za ayi mata kuma na ɗauko salahuddeen sai ayi mata afito da ita inyaso sai a cigaba da binciken ko ya kace,  duk dade har yanzu shiru babu wani labari ko alamar cin nasara sai a fito da ita wataƙil ma ta hanyarta zamu iya gano wani abun, kaga ance mutuwar daga ɓangaren ta aka fara sanar da ita, dole idan aka nutsu aka bi a hankali zata iya tuna wasu abubuwan da suka faru aloƙacin sanar da mutuwar,

Tana yin shiru papa ya ɗora da cewa "nima abun da yake ban mamaki kenan tun ranar nake zuba ido ko zan gano wani abun amma shiru, munyi maganar ma tace zatasa a binciko gidan su Wasila (jakadiyar ta kenan) saboda tun loƙacin mutuwar ba aƙara ganin taba acikin masarautar kuma anrasa inda gidan su yake,

Jinjina kai Maama tayi sannan tace "wai ni wama ya kawota da ba asan asalin taba aka kawo min ita duk dade zaman lafiya mukayi da ita tunda nake zaune da ita bantaɓa ganin wata alamar rashin gaskiya ba a tattare da ita ba bantaɓa tunanin za a haɗa baki da ita a cutar dani dan loƙacin da abun yafaru aka shigo min ɗaki dole tasan da zuwan su tunda tunkan dare yayi sosai a ƙa'ida a irin wannan loƙacin tana tare dani bata barina har sai tagama komai taga nayi bacci wataran ma aɗakin take baccin sai na farka nake tashin ta ta koma ɗakin ta kuma bata da nauyin bacci motsi kaɗan yana iya tashin ta, amma nayi mamaki tun wajen magriba na kwanta amma bata leƙo inda nake ba har akazo aka fita dani tace bata sani ba kaga kwa dole da sanin ko suwaye sukayi wannan abun,

Papa yace "maganar ki gaskiya ce ai ta inda ma takama kanta barin masarautar da tayi shine babban abun da yasa aka zargeta, daman kuma Waziri ne ya kawo ta kuma Saida ya tabbatar min da cewa yasan ko wacece ita har iyayen tama yasani amma bayan faruwar abun sai ya nemi kowa nata ya rasa ashe ba alkhairi bane ya kawota, tun loƙacin akaita nemanta amma ba asamesu ba,

Tunda yace Waziri amma take binsa da wani irin kallo mai cike da tarin tambayoyi, amma dai bata nunawa papa ba saikawai tace "Allah sarki Waziri nawa, to Allah ya bayyana su duk inda ta shiga zamu sameta da yardar Allah mudai dage da addu'a kawai itace mafita,

"Hakane Allah dai ya ƙara karemu ya toni asirin duk wani me hannu acikin" cewar papa

Maama ta amsa masa " da Ameen"

suna É—akin sukaji ana nocking Maama tace "waye shigo saboda tasan dai ba wani baren bane shiaysa tace a shigo kawai,

daga can wajen Ameesha tace bani shigowa tsofaffi ku fito kawai abinci yana jiranku in kuma kuka tsaya zakuga wayam muncinye kuyi sauri dan yunwa nake ji nikaÉ—ai ma zan iya cinyewa, tayi maganar cike da tsokanar su tana faÉ—a musu haka kuma ta juya ta bar wajen tana dariya...,

Suma ga baÉ—ayan su saida suka dara suna maijin daÉ—in tsokanar da tayi musu, papa na mayar mata da martani amma sukaji shiru tabbacin tabar gurin kenan,

Fuskar kowannen su ɗauke da murmushi suka tashi atare suka fito daga ɗakin, suna fitowa suka ga kowa agun su dadda duk sun hallara a tsakiyar falon inda aka baje musu kayayyakin breakfast kala kala, kuma daman tunda suka dawo idan zasuci abinci gaba ɗayan su suke ci a ƙasan falon kan capet basa hawa dinning,

Maama ce ta kalli Ameesha loƙacin da suka ƙarasa zama agun, tace "to acici munzo da fatan dai kin rage mana baki cinye ba,

ÆŠan murmushi Ameesha tayi tace "ai kunji tsoro naga kun fito da wuri amma da tuni kunga babu,

Papa yace yanzun ma da muka fito ai ke zaki cinye shi tunda kika faɗa kam sai kin ciye ko cikin ki zai fashe inkinƙi kuma indanne ki intura miki,

Hhhh Ameesha ta saki dariya "tace lalle ma tsohon nan kai da wannan tsufan nakama me taya zaka iya danne ne ai tuni zan ƙarasaka daman kazama guntu,

"Au haka kikace zakwa kigani bari innuna miki tsohon ƙashi da sabon ƙashi da bambanci, yana faɗa ya tashi ya koma kusa da ita yana kallon kwani kan gaban ta da kansa ya buɗe wani ɗan kwano mai kama flaks ya cika mata shi da doya da dankali ya buɗe wani yaƙara mata yamballs,

Kowa na gurin ya tsaya yana kallon su babu wanda ya tanka musu kowa nason ganin yanda zasu ƙare waye zaiyi nasara tsakanin Papa da Ameesha,

Yana gama zuba mata, ya tura mata gaban ta yace maza fara ci sai kinye duka in kuma ƙaro miki da haka sai kincinye shi duka, kallon sa ya mayar kan sauran yace karfa wanda ya fara cin komai naga wasu sai haɗiyar yawu suke kuma bamai ci duk natane duk wanda ya matsu ya tashi yaje abasa wani amma bazai ci komai nagun nan ba,

Maama tace "ai daman babu wanda yace zaici ai gaku ga abincin nan kallo muka tsaya yi, indai zata cinye mukam munyafe ma, koya kukace,

Su Azeema da Ummy suna dariya sukace maganar ki gaskiya ce Maama danni har baji nama ƙoshi cewar ummy,

Abu ma yakasa jurewa saida ya kalli papa yace nidai gaskiya bangoyi bayan hakan ba dan tun asuba nake jin yunwa kuma ga abinci ina kallo awani ce bazan ciba alhalin kuma ba iya zatayi ba, kawai salon ɓata mana loƙaci nidai azuba min bazan iya jira ba idan kuma baza a zuba min ba, inzubawa kaina, yafaɗa yana jawo flate yana shirin zubawa Maama tayi saurin ƙwace kwanon tace "Allah kuwa sai ka jira ko nan da shabiyun rana ne sai kajira ko kuma katashi daga nan,

HaÉ—e rai yayi yana kallon ta yama kasa cewa komai,

Papa da yaga haka sai yasaka dariya yace "kinga wannan wasan angama sa dan baza a ɓatawa masa raiba agabana abun da yake so shi za ayi azuba masa abinci yaci ke kuma Allah ya taimakeki da kinga yanda ake ɗurawa mutum abinci dan ko ta hanicine sai na ɗura miki amma yanzu dai kin tsallake sauran kuma nan gaba,

Ameesha "tace kadai ji tsoro bawani, dungure mata kai yayi yace "kaf family É—in mu ba matsoraci, kawaidai kinci da rajar mai daraja,

Duk dariya suka ƙara yi ƴan gurin kowa na tofa iyakacin albarkacin bakinsa cike da raha da tsokana, Saida sukayi mai isarsu sannan suka fara cin abincin,

Suna cikin ci Maama tace wai ni ina mutumi nane bangan saba ko motsin sa banjiba, duk wannan hayaniyar, tayi maganar tana kallon kowannen,

Abu yace "to Maama mu da kikatsatstsare mu da ido ina zamu san inda yake baki san É—akin saba, ganin damar fitowa ne baiyi ba,kinsandai halinsa,

Hararar sa Maama tayi tace "to ina ruwanka idan kuma bacci yake bari ni inje in nemoshi tunda nan duk tarin maƙita yatara bamai tunawa dashi kowa kansa yasani, wallahi idan baku gyara halinku ba akansa sai mun fara saka ƙafara wando ɗaya daku tana faɗa ta ƙarasa bakin ƙofar sa nocking tayi tana juyowa tana harar su ganin ko ajikin su kowannen su ma abincin sa yake ciki hankalin sa kwance,

Meer dake kwance can cikin bacci yafara jin kamar kuka kukan mutum a hankali yafara buɗe idon saida ya tashi zaune yaji ashe matar da ya ƙulle ce ta farka, shi yama manta da ita so yayi tun asuba ya fita da ita daga gidan amma ya manta ya kwanta tashi yayi ya ƙarasa bakin drower ɗin ya buɗe yana buɗe ta faɗo ƙasa tana ta faman juyi tana son kunce hannun ta, ganin sa agaban ta ba ƙaramin tsorata tayi ba, cike da tsoro tafara uhmm uhmm tana karkaɗa hannun ta da ƙafafun ta,

Tana cikin haka sukaji bugun ƙofar sauri yayi ya maida ita ciki ya rufe sannan ya nufi ƙofar yana gudun Allah yasadai kar ajiyo motsinta dan anaji idan kana cikin ɗakin, cike da magagin bacci ya ƙarasa bakin ƙofar ya buɗe yana leƙawa, ganin Maama atsaye yasa shi ɗan buɗe ƙofar yana kallon ta itama kallon sa take yi,

Murmushi ta sakar masa tana shafa fuskar sa tace "É—an gidan gwaggo mai ya hanaka fitowa, tayi maganar tana tura kai cikin É—akin, dafe kansa yayi gashi ba damar yace mata ta fita, yarasa dabarar dazai mata tafita........
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                        
Da sauri yasha gabanta ya haÉ—e rai sai kuma yarasa abun cewa, tsayawa yayi yana kallonta itama shi take kallo da mamakin tare tan da yayi,

Ɗan shafa ƙeyarsa yayi sannan yaɗan tsugunna ya kawo daidai tsawon ta, sannan yace "am uhm naceba kiɗan je waje ganinan zuwa zan shirya kinji yayi maganar yana kafe ta da tare da kama hannun ta alamar zai fita da ita saboda daman bata shigo dakin ba gaba ɗaya tana bakin ƙofa,
Chapter 22 · 0% Book details