← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 103

Sashe 44

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai a loƙacin ma yagama fahimtar ta kuma yagano laifin sa, dan haka ko ɗaki bai koma ba yace yanzu zai tafi gidan su, tunda de yasani, gwanda yaje da wuri tun loƙaci bai ƙure masa ba, kar yaje yaji labarin aure bai shirya mutuwa ba, dan idan yarasata ji yake sai ya rasa ransa,

Sallama yayi Hajiyar sa sannan ya tafi tana ta tsokanar sa tanayi masa dariya, haka ya fice daga gidan tabi shi da addu'ar samun nasara.......,

'yana kan hanyar sa yana tasakin murmushi sai yanzu yagama ashe kansa ya ƙulle duk baiga abun shiga damuwa ba, akan ɗan wannan abun da bai taka kara ya karya ba, duk laifin sane ma amma yana tafaman jin haushin ta ashe shine ma abun haushin gashi har ta daure ta kirasa amma yayi mata rashin mutunci yanzu kuwa dole yaje ya bata haƙuri akan abun da bata sani ba ya hauta da faɗa da jin haushin ta,

yana daf da ƙarasawa unguwar tasu dan kwana zaiyi kawai sai yaga wata mota tayi kwana, motar kuma kamar dai yasanta,

Da sauri yayi rivers ya juya yabi motar, dan yana da tabbacin motar asibitin suce kuma babu wanda yake shiga inba Sam ba, dan haka ya ware yajata da gudu yabita saboda waccen É—in ma gudu ake,

Haka sukaci gaba da tafiya suna tafiya yana bin bayan motar har suka ƙaraso kusa da wata unguwa sai yaga motar tafara slow tare da samun guri akayi parking ɗin motar,

Tsayawa yayi shima daga É—an nesa dasu yana hango motar yana jiran mai fitowa,

Yana gurin kuwa saiga Sam yafito daga ciki fuskar sa ɗauke da face mask sai p cap Dan badan yayi masa farin sani bana bazai taɓa gane saba,

yana ganin fitowar sa shima ya fito da sauri ya nufo inda yake,

Sam yana fitowa ya zagayo ya buɗewa sumy tare da miƙa mata hannu ta ɗora nata akai tana kallon fuskar sa ta sakar masa murmushi wanda hakan kana gani kasan tsatstsan murmushin ƙauna ne,

Shima da murmushin ya mayar mata, yana ƙarasa fito da ita daga ciki,

Fuskar sa ɗauke da murmushi idon sa akan ta, yace "yarinyar nan kin raina ni wallahi ɗan kwali yaja riga ko kinsaka ni agaba saida burinki ya cika gashi munzo to kuma wallahi ƙafata ƙafarki tare zamu shiga kuma a haka dan ko sakin hannun ki bazanyi ba, ba ruwana da idon mutane,

Ƴar ƙaramar dariya ta saki tace "wallahi baka isaba muje dai bakin ƙofa sai ka dawo ka jirani bafa daɗewa zanyi ba yanzu zan fito wallahi,

(tun bayan barin su gida washe gari ya ɗauke ta ya kaita wani gida ya ɗauko mata wata tsohuwa su ringa kwana tare saboda tsaro badan tsoro ba a ɗan kwana biyun nan da sukayi ba ƙaramar shaƙuwa sukayi ba har suka ƙulla soyayya zuwa loƙacin kowa ya fahimci yana son ɗan uwansa, duk sun tattara komai da kowa sun ajiye gefe sun rungumi junan su, ba inda suke zuwa soyayyar su kawai suke yanzun ma dalilin fitowar su, itace ta takura musu wai ya kawota gidan wata ƙawar ta zata karɓi wani abu yayi yayi da itama tagaya masa mai zata karɓa amma taƙi gaya masa,

Shi kuma sai yace bazai zoba sai ta faɗa ita kuma tace bazata gaya masa ba saboda sirri ne, daga nan suka rigayi yace baza su zoba, sai da ƙyar ta shawo kansa tayi masa wayo ta lallaɓa sa da kalamai, sannan ya yarda suka shirya suka fito tana yi masa kwatance har suka ƙaraso)

Sam zai yi mata magana kenan saiga shettima ya ƙaraso wajen, tare dayin gyaran murya,

Juyowa Sam yayi da mamaki yake kallon Shettima dake tsaye agabansa shima yana masa kallon mamaki yana kallon hannun su dake riƙe da juna, kallo ɗaya yayi wa sumy yagano ta, amma ita bata gane saba ganin sa yasa ta fara jan hannun ta daga riƙon da yayi mata amma sai yaƙara riƙewa ƙam,

"Malam kallon fa daga ina haka? Sam ne ke yiwa Shettima tamaya da ya tsatsaresu da ido,

"Hmmm daga sama nake É—an rainin hankali kai watakon kana nan hankalin ka kwance kabar mutane acan cikin tashin hankali,sai neman ka ake ka kashe wa mutane waya anrasa inda kake,

Sauya kalar fuskar Sam yayi cike da yanayin rashin daÉ—i yace "idan an nemeni mai za ayi min, bayan an kore ni to kuma mai zan tsaya inyiwa mutane kaga malam kaima idan ba gaisawa ce ta kawo kaba ka rabu dani dan Allah ina cikin farin cikina kar ka sanya min damuwa ina zaman zama na,

"Haba Sam ni kake gayawa haka, koda yake banga laifin ka ba, amma dai koma meye ya kamata ka ajiye komai agefe abun da ya faru ya riga ya faru saboda gida ba lafiya ya kamata ka dawo gida kodan saboda mahaifiyar ka, duk da ta yanke hukunci cikin fushi amma yakamata kayi mata uzuri, ni bata gaya mana ainahin abun da yafaruba kawai dai tace kun samu matsala, tace ka tafi kar ka ƙara dawowa inda take, to amma tun ka ayi nisa ta gane kuskuren hakan nemanka take kamar me tayi kuka ba adadi, ga kuma babbar matsalar da ta faru acikin gidan, abun ya matuƙar cutar da zuciyar ta abun ka tausaya mata ne yanzu tana cikin wani hali babu wanda take buƙata kamar kai tana buƙatar ka akusa da ita yakamata ka koma gida Sam,

"Shiru Sam yayi kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya kalli sumy da jikin ta gaba ɗaya yayi sanyi tayi shiru ta sunkuyar da kai tana taso yasakar mata amma yaƙi,

Ganin damuwa a fuskar ta, yasa ya É—an saki fuskar sa saboda ita, sosai ya zuba mata tare da kiran sunan ta a hankali É—an É—agowa tayi ta kalle sa batare da tace komai ba,

janta yayi can baya sannan yace "maiye haka kuma ki saki fuskar ki kinsan dai banson ganin ki cikin damuwa ko,

Kai ta É—aga masa still dai bata ce komai ba,

Hannu yasa ya É—ago ta yana kallon ta, sannan yace "plss ki daina nagaya miki yanzu kishiga cikin gidan kifito ina jiran ki a mota,

"To" tabashi amsa

"Yauwa tawan muje in rakaki,

Hannun su riƙe suka ƙarasa bakin gate ɗin sannan ya ƙwanƙwasa gate ɗin mai gadi ya buɗe musu saida yaga shigar ta da ta shiga ɗin ma saida tayi nisa sannan ya bar bakin gate ɗin, ya koma gurin Sam da yana tsaya yana kallon ikon Allah,

Sam na zuwa, Shettima yace "Allah Sam wai kaine haka Allah mai iko yau naga abun da yafi ƙarfi na, yaushe ka zama haka?

ÆŠan murmushi Sam yayi yace "abun da yafi haka ma zaka gani indai akan tane,

Shettima yace "ai naga alama, nima akan hanya nake duk ka tsayar dani, yanzu ya muke ciki zaka koma É—in ko bazaka koma ba,

"Shettima kai kasan yanda akai na ɗauko yarinyar kuma kasan halina kasan abun da zan iya yi da abun da bazan iya yiba, yanzu kamar ni dan momma ta ganni da mace zata ringa zargina har tayi min irin korar nan ta bari inyi mata baya ni ma amma taƙi saurarata ta koreni akan abun da bata da tabbas akai..,

Shettima yace "Tofa mai yafaru ni wallahi bansan komai ba yama akai ka kaita gidan, kuma ka bari ta ganta,

Sam yace "yarinyar nan tana cikin wani hali tana buƙatar taimako bayan na maida ita a loƙacin ta kirani tana kirana kuma sai tasaka min kuka na tambaye ta mai yake faruwa sai tace min mahaifin ta nace zan dawo mata dashi, bayan nan kuma washe gari ta ƙara kirana muna cikin waya kuma najita shiru to da har zan kashe sai kuma naji ana zaginta har da su duka, daganan na tashi na tafi gidan su ina zuwa naga anturo ta waje an watso mata kayan ta ana zaginta..........daga nan dai yabasa sauran labarin da inda yakaita gidan hajjaju har suka cutar da ita ya ɗaukota da labarin da tabasa na mahaifiyar ta shima saida yabasa har zuwa abun da yafaru tsakanin su momma tazo ta gansu tare ta yi masa wannan karon,

Shettima yayi mamakin yanda duk waÉ—annan abubuwan suka faru amma baisan komai ba, sai yanzu,

Nan dai ya tausayawa Sam, sannan yace masa yayi hauƙuri idan itama da kaifinta shima da laifin sa da yabari har tayi kwanaki a ɗakin sa batare da yayiwa momma bayani ba ai kamata yayi ma tun loƙacin da ya ɗauko ta yakaita gurin ta yayi mata bayani ai zata riƙeta amma baiyi ba, dan haka duk hukuncin da ta ɗaukama bai kamata shima yayi fushi ba,

Daga nan kuma Shettima ya É—ora masa da labarin abun dake faruwa iya abun da yasani,

Ba ƙaramin tsorata Sam yayi ba da jin abun da yafaru baya nan, cike da mamaki yake kallon Shettima yace "wai Ammah kake nufi yanzu bata cikin gidan, shi abun da yafi ƙara basa mamaki ma shine wai shi ake so a ɗora sarauta shiyasa duk suke wannan makircin wannan wacce irin rayuwa ce ai bashiri Sam da kansa yaje wajen gate ɗin yacewa mai gadi yacewa sumayya ta fito, ba daɗewa ta fito, tana fitowa yajata suka ƙarasa gurin motar ya buɗe mata gaba yasaka ta aciki,

Sannan ya kalli Shettima yace "mutafi gidan,

Shettima yace "a'a kadai je ni ba gida nayi ba zanje wajen tawa cikas É—in,

"Allah ko wacece? cewar Sam,

A'a ba yanzu ba idan tayi tsami kaji, yanzu dai sauri nake gashi ka ɓatan loƙaci sai anjima,

Nan dai sukayi sallama kowa ya kama gaban sa, Sam ya nufi masarauta, shikuma Shettima ya nufi gidan su Azeema....,✍️✍️✍️
Chapter 44 · 0% Book details