← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 103

Sashe 102

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Amra duk suna hanya dan Sumayya ko zuwa ma bazata iya yiba saboda nauyin da tayi itama haihuwa Yau ko gobe,

Su Azeema ma ana ta faman kayan ciki haka suka zo ita da Amra, Amra cikin ta watan shi bakwai ita kuma Azeema wata takwas itama ta kusa haihuwa,

Sati na zagayowa akayi suna inda aka sanar da mutane sunan da aka kuma sawa anƙara saka Sameer wajen na shida kenan a masarautar, in ka cire mutum ɗaya Sarkin farko da ya mutu, sai kuma Abban Ameesha, Abuu, Sam, Meer, sai kuma auta da aka haifa yanzu,

Mutane sunyi murna da hakan dan ana ganin hakanne ya kamata tunda masarautar ma gaba ɗaya da Sameer ake amfani kamata yayi ace duk sarkin da ya hau idan ya haifi ɗa yasanya masa sunan saboda hakan sai yafi tafiya daidai ta yanda baza'a taɓa mantawa da sunan ba, koda kuwa Masarautar zatayi shekara sama da ɗari za'a samu sunan.

Ranar suna anci ansha ba ƙaraya dan ba ƙaramin taro akai ba acikin harabawar masarautar, kowa teburin sa daban abin ci za'akawo kayi sarving ɗin kanka da kanka,

Can na hango teburin ƴan group ɗin sarki Sameer an gyara zama ana ta kwasar waku, Aunty me jidda na hango da cinyar kaza ankai baki ana yagar ta da hannun biyu, bakin ta duk ya ɓaci da mai saboda ci,

Mrs me martaba naji tana kallon Bajatu tace ke me kuma meye hakan kikeyi sai wani yagan mu, da sauri Bajatu ta É—ago tana mata alama tayi shiru a hankali tace ke Æ´aÆ´ana zankaiwa tana faÉ—a taci gaba da kwasar abincin tana zubawa a cikin jaka,

Mrs me martaba ta É—an yi shiru can kuma tace kai kuma fa kinyi gaskiya wallahi nima É—iba, zanyi yo Allah na tuba abun da baka saba ci ba, yau banza ta samu ai kinga fa sauran ma duk ba aciba, wallahi badan kar aganni ba da sai naje na kwaso waÉ—ancan lemukan,

Mr Saif tace "ku wallahi kuyi a hankali kar wani ya ganku, ku ta abinci kuke ni  kun san me na shirya duk ɗagowa sukayi suka haɗa baki wajen cewa a'a, itama tace kunga wancen kuɗin da ake liƙawa ƴan dubu dubu, su zanje in kwasa kallar su fa da yawa su kansa masu kwasar basa kwasa, Maman Faruk dake gefe tayi musu shiru tace da camara dai duk wanda yayi ana ganin sa,

Ƴar baba tace ƙyalesu dai, ni wallahi ma duk sun ban haushi, sai sunsa anyi mana kallon ƴan can garin,

Gaskiya dai nima sun ban amma dai dan Allah idan kun kwaso, su Bajatu  nima ku kawo min in ɗanɗana abincin gidan sarki Sameer kar abarni a baya,

               After 10 yeare ago......

Bayan haihuwar kowannen su na kowa aka nema masa aiki ɓangaren da ya karan ta,

Su Ameesha an zama lauyoyi, inda ta cika burin mahaifin ta, su suka ɗau case ɗin gidan su inda aka fito da su daga wajen sojoji aka gurfanar da su gaban koto tare da bada ƙwararran shedu, 

Ba awani ja case ɗin ba aka yanke wa kowanne su hukunci, Ammah da ƙanwar Dadda da kuma Dadyn Rasheeda life in prison, sauran kuma gaba ɗayan su tunda basuyi kisan kai ba aka yanke musu zaman shekaru ashirin ashirin wanda wasun su ma balalle bane sukai ashirin ɗin basu mutu ba....,

A ɓangaren su Rasheeda kam abun sai gaba da yayi dan ba Sa'a, suna can ƙauye mom wataran sai tayi bara take samun abun da zataci,

Rasheeda kam da taga ba hazi bare hazihi tuni ta koma ƙauyen daga baya kuma wanda de batason ko gani shi ta aura dan har barazana yayi mata idan bata yarda ba sai ya lalata mata rayuwa daga nan kuma ya kashe ta,

Jin tsoro hasa ta amince tun tana ƙyanƙyamin sa har ta dena amma sai ta fara sana'ar kayan ƙulle ƙulle da kuɗin da yake bata taja jari, shima kuma loƙacin ya ɗan ƙara kuɗi, da wayo da wayo ta ringa sakashi yana gyara jikin sa da wanke bakin sa, Allah ya taimake ta kam duk ya gyara, saidai ƙauyan ci kawai da shirme,

Da ƙyar mom itama Allah ya rufa mata asiri ta samu wani tsoho ya aure ta amma irin mazannanne masu ɗaukar mata ba abakin komai kuma shi ba'a haihuwar masa agida, duk wacce ma ta aure sa tasan da hakan, kuma laifi kaɗan zakiyi masa ya kamaki ya jibga son ransa,

Duk wannan rayuwar da suke Khalid bai sani ba babu irin neman da baimusu ba amma ya rasa inda suka shiga saboda baisan sunan ƙauyen da suka koma ba,

Ranar wata laraba, yaje wata kasuwa kawai ya haÉ—u da Rasheeda duk ta lalace ta fita hayyacin ta kamar ba ita ba ya tausaya mata sosai, nan ta kwashe duk abun dake faruwa da rayuwar da suka tsinci kansu ciki, har kusan kuma yayi musu, dan duk wannan abun ba kowa bane yaja musu illah mahaifin ta alhakin abun da mahaifin ta ya aikata ne yake ta bibbiyar rayuwar su, nan yabita har inda suke ya taimaka musu da kuÉ—aÉ—e sannan yace zai ringa zuwa yana duba su, sannan yabata shawara yace ta kira mahaifiyar ta suje su nemi tafiyar waÉ—anda dadyn ta ya zalinta idan suka yafe musu sai suga daidai arayuwar su,

Ta É—auki shawarar sa kuwa suka shirya ita da mahaifiyar ta suka je har cikin masarautar suka nemi yafiyar kowa harda ta Ameesha abun da suka ringayi mata da tana gidansu,

Duk an yafe musu harda haɗa su da kuɗaɗe masu yawa da kyaututtuka, sunji daɗi kam dan shine ma silar warwarewar wasu matsalolin dan sun taimaka musu sosai, yanzu suna cikin wani ƙauye ne suna Sauna......

Allah yayiwa gwaggwo rasuwa itama tun shekara biyar baya, duk da ta tsufa amma mutuwar ta taɓa su saosai, ansha koke koke, ansha kuka, angode Allah,

               *****************

A cikin shekarun nan Ameesha nada yara uku maza biyu sai autar su mace,

Azeema kuma nada biyu, sumayya ma uku gare ta, sai Amra  da take da guda huɗu haihuwar ta ta farko ƴan biyu ta haifa maza, sai kuma ta ƙara haifar mace da namiji,  Hamra kuma biyu gare ta tana da cikin na uku,

Rayuwa ta sauya kowa ya canza, aikin ko wannen su na tafiya, dai dan Shettima ma zuwa yanzu ya buÉ—e nasa asibitin na kansa inda yasanwa sunan asibitin AZEEMA HOSPITAL,
Sam kuma sai ya canza wa nasa suna ya koma, S&S spatial hospital, (sameer and sumayya)

Bossay kuma ya buɗe babban capy bayan kuma plaza daman kuma yana ƙaton mall, daga ciki ya ɗauki ɗaya yasanya sunan Amra ajiki sannan yace ya bata mallakin tane,

Hamza da Meer kam, (au na manta) sarki Sameer da me martaba Hamza, suna daga gida, daga fada sai fada, saidai shi sarki Sameer yana da asibitin sa a Abuja kuma yana ta tafiya yanda ya kamata loƙaci zuwa loƙaci yakanje ya leƙo sa,

Suma kuma matan dukkan su babu wacce bata aikin ta, dake duk ba'aikin fita suke koda yaushe ba, su Amra suna daga gida ma yin nasu suke su aika, su Azeema kuma sai wani case É—in ya tashi sukanje suyi shari'a su dawo,

To dai Khalid ma de ga angwance tare da wata tsaleliyar budurwar sa da ya zaɓo acikin garin kano, me suna Hauwa'u,

Saleema ba abarsa abaya ba yayi aure shi kuma ƙanwar Bossay ya aura me suna Aisha,

Suma kuma duk sun haifa musu yara É—aiÉ—ai Khalid na da É—an namiji saleema kuma nada Æ´a mace.....,

SARKI SAMEER...

shigowar sa falon kenan ya tarar da Ameesha tana yiwa Ameer (babban ɗan su Sameer) faɗa take yi masa akan rashin cin abin ga mugunta da dukan ƙanen sa basu isa sun rabe saba, zaice su matsa shi ba sa'ansu bane, ga idan ya haɗe rai kwata kwata bashida fara'a dan har yaso ma yafi ubansa akomai,

Kama yaron yayi yana zama akan kujera yana "me kuma mukayi za aringa yi mana faÉ—a, mufa ba"ayi mana faÉ—a inba hakaba kuma yanzu mu É—aga hankalin kowa dan kan me uwa jawabi zamuyi kowa ma zamu iya hucewa akan sa, ai gado ba banza ba akan me za'aga laifin mutum....,

HaÉ—e rai Ameesha tayi tana hararar su gaba É—ayan su tare da kaiwa yaron duka Meer yayi saurin janye sa yana cewa Allah kuwa baza adakar min É—a ba,

Kallon yaron yayi yace "Ameer ne kake so kaci,

Cikin haÉ—e rai yaron yace "meat pie,

Da sauri Ameesha tace "Allah kuwa saidai ka kwana da yunwa bashi abinci sai snaks taya rayuwa zatayi ace kullum bashi da abun ci sai kayan fulawa to wallahi ka sauya hali tun wuri dan bazan ci gaba da É—aukan wannan rashin mutuncin naka ba,

Meer yace "to ai gwanda kayan fulawa suna cika ciki, ko kin manta ni me nake ciki kuma gashi na rayuwa babu abun da ban iyaba,  dan haka kema ki rabu dashi yaci abun da yake so idan ya girma ya haɗu da wata beb ɗin sai ta canza sa kamar yanda Lily ta canza ni.....

Filo ta ɗauka ta jefa masa cike da ta ƙaici tace "daman ai kai kake sawa yake yin duk abun da yake,
Ameesha na kallon su cike da taƙaici tace...
"wallahi da nasan halinka zai É—auko da banyarda ansaka masa sunan nan ba, fata na É—aya kar ya É—auko wannan rashin kunyar taka in shiga uku, yanzu ya É—auko komai a halin ai wallahi saidai in tarkata shi inkaiwa besty tunda naga yafi sakewa acan,

"kai tashi kabar wajen nan kafin ranka yayi mummunan ɓaci,
Gaba yayi zai tafi Meer ya riƙo sa yace "tsaya sai ta fara baka sai katafi,

Kallon mahaifin nasa yayi yana haɗe girar sama da ta ƙasa tare da turo ɗan ƙaramin bakin sa da yaɗauko irin na Ameesha, kamanin sa kuma na uban sa,  cikin haɗe yace "Sarki Sameer ka sake ni bazan ci ba ko ta ɗauko kuma ta mayar dani gidan marayu ma daman nasan ai baso na take ba,
Chapter 102 · 0% Book details