← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 103

Sashe 8

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maƙe kafaɗa tayi tana turo baki tace "Allah kwa ko me zakamin bazan sake ka ba sai nayi abun da nayi niya kuma sai kaban amsa ta indai kana so intafi to ka amsa min tambaya ta sai mu rabu lafiya idan kuma masifar zakayi sai kai tayi kuma ka dake ni inje inyi maka sharri wajen Abu yazo yayi maka faɗa tunda naga baka son faɗa saboda gaka ɗan mai kai baza ayi maka faɗa ba,

Zaro ido yayi waje yana duban ta da kyau yana tunanin anya kuwa yarinyar nan lafiyar ta ƙalau kodai tasamu taɓin ƙwaƙwalwa ne basu sani ba ko kuma tana da mental problem, loƙaci loƙaci yana tasar mata yanzu kuma loƙacin tashin nashi ne yazo shiyasa take masa haka a tunanin sa to inba hakaba me zaisa tana gaga masa haka bayan yarinyar tsoran sa take yasani duba da shigowar tama yanda ta tsorata tana kuka amma ace loƙaci ɗaya ta burkice ta ringayi masa waɗannan surutan har yana mata magana tana cewa bazata yiba,

Tunanin hakan dan har ga Allah yagama tunanin tana da taɓin ƙwaƙwalwa dan yasan da a hankalin ta take bazata taɓa yi masa kwatankwacin abun da take masa ba yanzu, dan haka ya yanke shawara gwanda ya bata amsar su rabu lafiya kar haukan ya ƙaru tasaka masa ciwon kai yana zaman zaman sa,

Ɗan sassauta fuskar sa yayi daga haɗe tana da yayi sannan yace "ni ba mugu bane duk wanda nayiwa abu shi yakawowa kansa sa bai shiga harkata ba ko inda yake bazan kalla ba, idan kuma yayi min dole nima inyi masa abun da zai ƙoma masa rai bawai danjin daɗin raina ba dan ya kiyaye gaba kar ya ƙarayi min abun da yayi min, kin gane?

ÆŠaga masa kai tayi tace nagane amma kuma ni me nayi maka kada keni kuma kataka min ciwo inda ba mugun ta nace,

"Oh my God, ya faɗa aransa yana dafe kansa, sannan yace ke kikajawowa kanki tunkan in kwanta nace miki kije wajen su ummy su baki abun da kike so sannan kibar gidan kar nafito naganki aciki, amma kika ƙi ji daga ƙarshema kuma ki haumin kangado kika kwanta a inda nake harda rufa saboda kin rainani shiyasa na zane ki saboda banason ko wacce mace ta taɓani, nace kifita kiƙi fita saboda bakya jin magana,

To meyasa yanzu na taɓaka kace bakason mace ta taɓaka,

"Saboda a loƙacin banda alaƙa dake ba kamar yanzu ba, da kike ƙanwa agurina,

Wani daɗi taji jin yace mata ƙanwar sa daman yasan da haka ashe ko shiyasa har yanzu bai dake taba dan itama aƙasan ranta duk abun da take masa tana sane kuma cikin tsoro takeyi tayi mamakin ganin ba abun da yayi mata, duk wannan abun da take masa, amma duk da haka sai ta ƙada dakewa bata nuna jin daɗin hakan ba a fili,

Sai kawai ta karkaɗa kai tace "To ai loƙacin daka faɗa nayi bacci bansan ka faɗa ba kuma abun da yasa naƙi tafiya idan na tafi bansan inda zani ba, shiyasa na maƙale maka da naga ka taimake ni, nayi tunanin kana da mutunci idan na bika zaka ƙara taimakamin ka mayar dani gida sai kuma naga ashe baka da mutunci, mugune kai,

Buge mata baki yayi da É—ayan hannun yace "kar kisake cemin mugu kuma kitashi kibar min É—aki tunda na baki amsarki ki rabu dani kifita,

Dafe bakin tayi saida ta daina jin zafin sannan tace "To kuma badan niɗin ba ai da ba tuni yanzu bakasan inda dangin ka suke ba da ka koreni na tafi da tuni ka kori danginka kaifa wallahi kamata ma yayi ka gode min tunda na taimake ka, kuma wallahi kayi na farko wallahi ka ƙara taɓani daga nan sai wajen Abu Allah in kuma kana wasa ka ƙara,

Meer fa yafara fusata, da ƙarfi yaƙara ɗaga hannun nasa zai ɗauke ta da mari sai kuma komai ya tuna sai yadakata baikai hannun nasa kan fuskar tata ba,

Ita kuma har ta rufe ido tana jiran taji saukar marin sai kuma taji É—if, a hankali ta fara buÉ—e ido É—aya tana kallon sa taga abun da yahanasa marin nata,

Ƙwace hannun sa yayi gada riƙon da tayi masa yana miƙewa tsaye cikin daka mata tsawa yace tashi ki fita ga mamakin sa sai kawai tama faɗa kan gadon nasa ta kwanta daga bayama ta ɗora duka ƙafafun ta akai, sannan ta ƙara da cewa "bacci nakeji kabari idan natashi zan barmaka ɗakin ka ba ci zanyi ba wai kai meyesama bazaka barni ba kake kora duk duniyar nan kana da wata ƴar uwa kamata baka da ya baka da ƙanwa sai ni kaɗai kai da zaka lallaɓa ni amma ba abun da ka iya sai yimun mununta da cin zalina, Allah ya shiryeka ka gane gaskiya, nasiha nake ma amatsayi na ƙanwar ka wallahi kadena abun da kake ka shiryu kuma kadena yiwa iyayen ka rashin kunya, inba hakaba kajefa kanka cikin wutar jahannama yakamata ka ringa jin maganar iyayen ka kaga ni da ace agaban iyayen na taso ace mahaifiya ta da ranta bata mutuba da sunga biyayya da kulawar da zanringayi dasu, Allah yasa mahaifina yana raye Allah ya bayayya na min shi ko shikaɗai inyi masa biyayyar tanayin maganar kuma sai jikin ta yayi sanyi ta ƙarasata a hankali,

Loƙaci guda taji hawaye ya cika mata ido tunawa da tayi ayanda mahaifiyar ta ta rasu wani irin kuka ne ya taho mata me ƙarfi dan sosai zuciyar ta ta karaya, da sauri ta tashi daga kan gadon ta kwasa aguje saboda bataso tayi kukan anan gabansa,

Saidai kuma ko taku uku batayi ba taji an riƙo hannun ta tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba tana ƙoƙarin ƙwace hannun ta, shikuma ya ruƙe da ƙarfi tare da jawota ta dawo baya agaban sa ta tsaya suna facing ɗin juna yayin da kukan ta kuɓuce mata tasake shi me ciwo,

Tsayawa yayi yana kallon ta yanda take kukan kamar ranta zai fita akaro na farko arayuwar sa da yaji ya tausaya wa mace har yaji shima jikinsa yayi sanyi yaji bayason ganin irin wannan kukan da take,

Ƙoƙarin ƙwacewa taƙara yi zata fita daga ɗakin sai shima yayi saurin ƙara riƙota ya fisgota ya haɗata da ƙirjinsa ya rungumeta tare da kwantar da kanta akan ƙirjinsa saboda bata da tsawo gaba ɗayan ta a ƙirjinsa ta tsaya,

Shafa kanta ya shiga yi cikin son rarrashinta saidai kuma shima yanda zuciyar sa ta karaya yasa yakasa furta koda da kalma É—aya wajen kwantar mata da hankali ta dena kukan,

Aɓangaren ta kuwa hakan da yayi mata sai taji kamar yace taƙara volum haka taƙara fashe masa da wani irin kuka da ita kanta batasan ta yanda akai take irin wannan kukan ba......
✍️✍️✍️

_Afuwa jiya banyi ba bansamu damar yi ba ina shirin yi data ta taƙare bansamu nasaka ba sai yanzu shiyasa banyi ba jiya_

_Sai kuma ranar asabar kamar yanda nace zanringa hutun kwana biyu Alhamis da juma'a ba update, sai asabar idan Allah yakaimu,_
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

                 *_Typing........✍️✍️_*

                        

_______kuka ne sosai yaci ƙarfinta tana ƙara gyara shigewa jikin sa,

ganin taƙi yin shirun kuma yakasa ce mata komai saboda baisan ma ta ina zai fara rarrashin taba, daga ƙarshedai da yarasa mafita sai kawai yafara tafiya tana jikin nasa ya ƙarasa bakin gadon sannan ya zauna ya ɗorata akansa kamar wata baby haka ya riƙeta sannan yasaka hannun akan sumar kanta yana shafawa a hankali ɗayan hannun kuma ya shiga bubbuga bayan ta dashi,

Daidai saitin kunnen ta yakai bakinsa sannan a hankali yasamu damar furta mata sorry, stop crying, ya isa haka,

Duk da tajishi amma sai taji ta kasa daina kukan ita kanta tanaso tayi shirun but she can't, ba yau ta fara tunawa da suba amma bata taɓa yin irin kuka makamacin irin na yau ba bata san me yasa ba,

Meer dai yau yaga ta kansa bai iya rarrashi ba amma yau saida ya koya ya rarrashi tilon ƙanwar sa, haka yayi ta rarrashin ta har saida yaga tayi shiru ta fara ajiyar zuciya,

Tunda tayi shiru tayi lamo ajikin sa ko motsawa batayi kawai tayi shiru sai taji wata nutsuwa tafara saukar mata,

Shima shiru yayi yana sauraron bugun zuciyar ta da take bugawa a hankali a bankali, sunkai wajen minti ashirin ahaka kafin daga bisani Ameesha ta raba jikin ta da nasa ta sauka daga kan cinyar sa zata tafi ya riƙo hannun ta tare da dawo da ita gefen sa ya zaunar da ita batare da yace da ita komai ba, itama shirun tayi batayi yunkurin tashiba kuma batace komai ba bata kalle saba ta sunkuyar da kai kawai tana sauke ajiyar zuciya,

Saida ya tabbatar da tadawo daidai, yasa ta goge hawayen, duk da idon ta sunÉ—an kunbura amma amma saida ta samu nutsuwa sosai kamar batayi kukan ba, kallon ta kawai yake ita kuma bata iya É—agowa ta kalle sa ba duk da sakayau take jinta ba wata damuwa ammadai takasa sakewa dashi yanzu kamar yanda tasake dashi É—azu,

Sakin hannun nata yayi  sannan ya zaro choculate ɗin da yasa a aljihun sa ɗazu, ɓare ta ya shigayi saida yagama buɗeta gaba ɗaya sannan ya miƙa mata,
Chapter 8 · 0% Book details