← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 103

Sashe 17

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baby ya isa haka kibar min godiya kinsan banaso yi sauri ki saka kayanki mufita,

Sakin shi tayi da sauri ta É—auki kayan da ta fito da su ta hau shiryawa agaban sa, cikin hanzarin tagama kimtsa kanta cikin riga da wando saidai rigar ta É—an sauko mata ta rufe mata É—uwaiwai, ta É—auki hula ta É—ora akanta sannan ta kalli Dady tace "Dady komai normal?

Hannu ya jinjina mata yace "yesss fine girl muje ko, riƙo hannun sa tayi suka nufo ƙofar fita ranta fal cike da farin ciki, duk da farin cikin da take zuciyar ta takasa yarda ɗari bisa ɗari dagaske ne inta fita zata gansa, amma dai bata nunawa Dadyn nata ba a fuska saboda kar yaga kamar tana ƙarya tasa shiyasa kawai tayi shiru tabishi a yanda yake so,

Buɗe ƙofar Dady yayi suka fito daga ɗakin sannan suka fara takowa benan da zai sauko dasu falon, tunda suka fara saukowa take rarraba ido ta inda zata gansa amma bata gansa ba har suka ƙarasa fitowa tsakiyar falon,

ÆŠagowa tayi ta kalle sa da alamar tambaya,

Murmushi ya sakar mata tare da shafa gefen fuskar ta, yace "kin karaya ko?

Kai kawai ta samu damar É—aga masa,

Sai yaƙara wani murmushin tare da kallon ƙofar shigowa yace "Come in...

Turo ƙofar akayi tare da shigowa ciki, da sauri taja baya ganin abun da bata taɓa tunanin ba duk atunanin Dadyn ta wani zai kawo mata daban amma sai taga da gaskennen murya na rawa ta kalli Dady tace "Da...dy wai da gaske ne abun da nake gani ba mafarki bane Dady shine fa wallahi shine..... Gaba ɗaya ta fita hayyacin ta duk son da take ta gansa amma ganin sa sai ya ɗaga mata hankali gaba ɗaya ta tsorata da ganin sa musamman ma da suka haɗa ido dashi taga idon sa ya juye kamar bana mutane ba.......✍️✍️✍️

Wayyo Allah na mai yake shirin faruwa Meer har cikin gidan su Rasheeda tabbb, lalle Dadyn Rasheeda na jinjinama ƙarfin halin ka kayi namijin ƙoƙari dole mu tsorata dakai........,

         
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

     
            _*BAYA*_

_____ Abun da yafaru  har ya samu ya ɗauko Meer....,

Loƙacin da Meer yacewa Ameesha ta shirya zasu fita da daddare, ita kuma bayan ta fita daga ɗakin sa, tana fitowa direct ta wuce ɗakin dadda saboda Azeema ma tana can tana jiran ta,

Tana shiga ta tarar da Azeema kwance akan gado amma ba bacci take ba shigar ta yasa ta tashi zaune tana mata dariya tace matsoraciya to yanzu ba gashi angama komai ba amma da kin tsaya wani jin tsoro sai kace kin haÉ—u da dodo,

Itama dariyar tayi ta ƙarasa gurin ta zauna agefen ta, tace ba wani nan aidai nayi ƙoƙari ahakan, ni abun da yafi ban tsoro ma, kin san mai yace,

Kai Azeema ta girgiza mata tace sai kin faÉ—a,

"Wai yace mu shirya anjiman zai aike mu gaba ɗayan mu wai harda su Amra, wai zaisa wani daga cikin gidan nan yakaimu a mota mukarɓo masa saƙo,

Azeema tace to kuma maiye abun tsoro aciki naji daɗin hakan ma, ke ai wannan dama ce kika samu da zaku ƙara sabawa sosai yanda zaku ringa fahimtar juna, duk wani abu da zai kusantaku ai mu dama ce agurin mu, ba wani abu wallahi kar ki damu ai yasan mai yake kindai san bazai taɓa sawa akaimu inda za'a cutar damu ba,

Ameesha tayi jugum tayi tagumi saida Azeema tagama maganar ta sannan tace "besty nifa bawai wani abun nake tsoro ba, abun da yafi tsaya min arai kinsan dai mutanen nan sunganmu kuma nasan yanzu dole idon su a kanmu yake duk wani motsin mu zasu saka mana ido kinga kwa suna ganin fitar mu zasu iya binmu, gashi kuma yace wai mutafi da wayar yama mayar da memoryn ciki, bansan dalilin sa nason aiken namu ba, kumafa da farko haka yace kar musake mufita har sai yace mufita amma shine kuma ayau abun yafaru kuma zai samu mu fita dan Allah É—an wasa da rayuwa,

Dariya Azeema ta kamayi jin yanda tayi maganarta ta taƙarshe tayi tana haɗe rai da turo baki gaba kamar zata fashe da kuka, Azeema tace  "kai besty wai wasa da rayuwa ke haka yace miki wasa zaiyi da rayuwar mu, dan Allah kibar wannan maganar, mubar tama gaba ɗaya yanzu ki taso muje wajen su Amran tun yanzu inyaso idan ya nememu sai mu dawo nan mu shirya mu tafi,

Har Ameesha zata sake magana sai ga dadda nan ta fito daga banɗaki tayo alwallar salar magariba duk da loƙacin ta baiyi ba, fitowar tane ya hanata yin maganar da taso yi,

Ƙarasowa tayi zuwa inda suke tace sai yanzu kika shigo mai kuke tattauna wane yaran nan anya kuwa kuna da gaskiya, sai ƙusƙus ake nakasa gane kanku fa yau ɗin nan,

Ameesha ta saki ƴar ƙaramar dariya tace "haba dadda kinsan ai bazan taɓa yin abuba baki sani ba, ba wani abu ba muke shiryawa ba kawai kin san ɗazu yaya shiru tayi bata ƙarasaba sakamakon jin da Azeema tasaki ta ɗane kan gadon gaba ɗaya, tana nuna ƙasa,

Gaba É—ayan su bin inda take nunawa sukayi da kallo amma basuga komai ba,

Cike da ɗan shiga ruɗani Ameesha tace "besty mai yafaru mai kika gani haka, ɗan leƙowa Azeema tayi daga kan gadon, sai kuma taƙara saukowa gaba ɗayan ta tana dire dire tace wayyo Allah na wallahi motsi nake ji ajikina, tanayi faɗa tana zazzage kayan ta tana ƙara sakin ƙara, ɗan kwalin kanta tacire kawai tace besty ina zuwa bari inje incire kayan jikina in duba inga gurin yafara min zafi,

Tana faÉ—a tayi saurin ficewa daga É—akin, Ameesha nacewa "Besty ki tsaya mana anan idan kinfita a ina zaki cire kayan to, bata bata amsaba hakan yasa Ameesha tayi saurin binta abaya,

Tana fita daga ɗakin ta ganta a tsaye a tsakiyar falon a tsaye, Ameesha na ƙarasawa gurin ta takama hannun ta ta jata suka fita waje,

Saida suka fita Ameesha, ta kalle ta da mamaki tace besty yana ga haka kuma ko abun ya fita?

Azeema ta taɓe fuska tace "ke nifa ba wani abu ajikina, ina sane nayi haka kawai banason kigaya mata abun dake faruwa ne shiyasa nayi hakan ina tayi miki alama da ido kar kifaɗa amma naji zaki faɗa shiyasa na ɓullo Miki ta nan nasan dole zaki shiru, dan haka ko ba yauba kar kisake kigaya mata komai na gaya miki idan kuma ba hakaba nida kene wallahi, tafaɗa tana doka mata harara,

Ameesha kamar wata gunki haka ta tsaya tana kallon su da 68887877 Azeema kamar ta samu television,

A hankali tace "besty kinsan kwa me kike faɗa bangane me kike nufi ba, dadda ce fa daddar kike cewa kar na faɗa mata wani abun da ya shafe ni, maye aciki dan nagaya mata ina da wacce ta fita itace komaina dan haka babu abun da zan ɓoye mata, besty ina da wanda yafiye min dadda arayuwa ta bandashi, babu wanda yakaita matsayi aguna, matar da tun ina ciki take wahala dani har ta na taso ina tana fama dani bama ni kaɗai ba kinmanta ɗawainiyar da tayi da mahaifina, taimakon da tayi masa ta sanadin mahaifina ta rasa duk wani farin cikin ta tarasa mijin ta ta rasa ƴarta, duk saboda mu, amma har kike cewa kar nasake na gaya mata abun da ake ciki ni banga wani abuba aciki, maganar gaskiya besty banji daɗin abun da kika yiba wallahi, dan Allah kar irin haka ta sake faruwa a tsakanin mu, tana kaiwa nan, ta juya zata shige ciki tayi karo da Meer dake tsaye abakin ƙofar tun fitowar su,

ÆŠan ja tayi da baya dan batayi tunanin ganin saba agun, sunkuyar da kai tayi ganin irin kallon da yake mata sai taji duk ta tsargu da irin kallon,

"Wuce ku tafi inda tace miki kuma ana idar da sallar magriba zaku fita, sannan kar ki fasa gaya mata ɗin kije kigaya mata komai ɗin kiga yanda zanyi dake, bance ma kar ki sanar da kowa ba shine bayan kingaya mata shine kike shirin gayawa wata to bismillah ban hanaki ba kike kigaya mata duk abun da yafaru yauɗin dama abun da zai faru nan gaba kar kifasa kigayawa duk wanda kikaga damar gayawa, ɓace min dagani kafin indama kanki anan,

Sum Sum Sum tayi baya ta fara tafiya idon cike da ƙwalla,

Kallon Azeema yayi dan ya fahimci ta tafita saurin fahimtar abu  sai yace "ki kula da ita bata da hankali karki bari ta ringa kasancewa da kowa ita kaɗai,

Kai Azeema ta kaÉ—a masa, batare da tace komai ba ta juya tabi bayan Ameesha da ta nufi part É—in su Amra,

Shikuma ya koma ciki yana jinjina irin halin yarinyar nan ya lura inbaiyi da gaske ba bazata ringa basu haÉ—in kai ba, zata basu matsala wataran,

Azeema na zuwa gurin Ameesha haƙuri kawai tabata daga nan suka ƙarasa cikin falon da suka shiga suna ɗakin su dan haka suka haura saman suma inda suka samesu suna game a waya, jin shigowar su yasa suka ajiye game ɗin suka gaisa,
Chapter 17 · 0% Book details