← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 103

Sashe 35

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙulle ledar yayi yana kallon "Meer yace "waye baya son mugunta ni na taɓa ganin ma mugu irin ka jifa yanda kasa zuma ta mai dasu kamar saniyoyi ji yanda wannan yayi kamar alade, wallahi ka rage mugun ta ni ai tawa mai sauƙi ce kuma kaine kasa akawo ta asaka musu ni labari kawai nabaka,

Hararar sa Meer yayi yace "to naji ya isa haka banason surutu yayi yawa ka kamo wasu mufita kasandai mu ake kira tun É—azu ka tsaya kana wasan yara,

"Wa?  waye zai kama wani ai wallahi babu wanda zan taɓa kowa ya tashi yataka da ƙafarsa ya fita idan kuma sunƙi Allah saka musu zanyi ita zata iya fita dasu idan su baza su iya ba,

Kai tashi kaima tashi ya dake su da ƙafa yana turasu,

Meer yace "dude baka ji wallahi baka da mutunci ko Æ´ar kara ma baza kayi min ba ganin ido na agun kakannina ne fa da iyaye na amma kake musu haka to zan rama musu,

Dariya Khalid da yayi yace "to ai ni ba iyayen na bane "jika sai kace gaske shiyasa naga jiya ka zage ka ware hannu ka dake su to shikena bari inyi maka kara muje mubar su sannan kaÉ—auko kayan aiki kayi musu aiki su dawo mutane shine zansan iyayen kane,

Jinjina kai Meer yayi yana matsawa kusa dasu daidai  kan Waziri ya tsaya tare da caƙumo wuyan sa da hannu ɗaya ya ɗago sa yana tura sa haka duk yayi wa sauran ya miƙar dasu cike da mugun ta, wasu ma harsaida wuyan su yayi shatin ja saboda ɗago sun da yayi matan kuma da gashin kansu ya ɗago su, Ammah da tayi kitso kuma ba damar kamo gashin ta, sai ya kamo jilar kitson tana jin hakan gudun kar ya tsige mata kai yasa tayi saurin miƙewa batare da ta shirya ba,

Kafin su fita duk saida yasaka su suka maida É—an kwalayen su da mayafan su, matar waziri kam daman ba mayafi akan ta,

Abdullah (dady baban Sam) shi harda cire riga shima saida ya mayar da ita sannan suka fara takawa da ƙyar suna daddafawa suka ƙaraso cikin fadar, su Meer na bayan su,

Gaba É—aya mutanen ciki suka zuba musu ido kowa idon sa nakan su,

Loƙaci ɗaya zuciyoyin wasu suka ƙara raunan jin ganin mutane fal acikin gurin duk da ba wanda suka ɗago suka kalla amma suna da tabbacin mutane da dama nakusa dasu suna cikin gurin,

Wani guri a tsakiyar gurin da aka tana da dansu anan suka zazzauna aƙasa tare da durƙufar da kan su ƙasa dan bazasu iya haɗa ido da kowa ba a halin da suke ciki, ji sukayi tsanar kansu da tsanar Meer takama su saboda bai kamata yayi musu cin mutunci irin haka ba kuma ya tara mutane ya fito dasu a haka,

Duk da halin da ake ciki bai hana wasu yin dariya ƙasa ƙasa ba, wasu kuma bama su kalle su ba irin su momma dan tunda suka fito bama tabari idon ta ya sauka akan kowa ba ta rufe ido tare da kawar da kanta gefe,

Ƙananun maganga nune suka ɗan fara fitowa sai cikin gurin yanemi ya kauraye da haya niya saboda kowa yana faɗar albarkacin bakin sa,

Meer ne ya koma ya zauna akan wata kuje ta tare da ɗora ƙafa kan ɗaya Khalid kuma ya tsaya agefen sa,

Minti biyar Meer ya basu kafin daga baya ya dakatar da su kowa yayi shiru, babu meyin wata maganar bakajin motsin kowa kamar babu mutane aciki tsit kake ji sai ƙarar Ac dake aiki agun,

Bayan kowa yayi shiru, Meer yayi gyaran murya tare da gyara zaman sa yana fuskantar kowa da kowa,

Cike da tattaro duk wata nutsuwar sa ya haÉ—a ta waje guda, É—an É—aga murya yayi yanda kowa zai iya jiyo sa,

"ASSALAMU ALIKUM, WA RAHAMATULLAHI WA BARAKATUHU,

"WA'ALAIKASSALAMU WARAHAMATULAHI WABARAKATUHU

wasu daga cikin suka amsa waɗanda suke da ƙwarin gwiwar amsawar,

Bayan sun amsa, Meer yace "kowa yasan maƙasudun abun da ya haɗa mu anan waɗanda ma basu sani ba zasu sani,

Da farko ina mai bawa wasu haƙuri bisa ga duk abun da zasuga anyi da wanda yayi musu da akasin haka, ina so kowa ya cire komai aransa duk abun da kaga yafaru da kai bawai yin kanka bane Allah ne yasa hakan zata faru dan haka kuɗauki haƙuri kudaina wani koke koke ko kuka, yawancin mutanan gurin abun ya taɓa su kuma su akayiwa a cutar da rayuwar su,

Ni bansan taƙamaman abun da suka aikata ba kawai dai nasan sune suka kori gimbiya tare da iyalen ta, alhalin duk suna cikin gidan nan, sai gashi kuma loƙaci ɗaya Allah ya kawo ƙarshen abun,

Tun a loƙacin da muka shigo cikin gurin nan tun anan nafara gane wasu kawaidai hujja ce banda ita da zan kama mutum kai tsaye, saidaga baya da nafara wani tunani sai nafara zargin Waziri aranar da naje masa da maganar yanda za ayi agano ko su waye, nikuma anan nayi amfani da damata nagano sa cikin bugar cikin sa, bayan fita ta kuma sai na bar wayata ina ɗaukan sa video batare da sanin saba, todai bansan ya akai yagani ba, suka haɗa min wai tarko ne shine bayan na nuna masa videon yasaka min dariya tare da gaya min duk wasu ƙudurin su akan mu shi da matar sa aloƙacin na zuciya na shaƙe matar tasa ba luraba shi kuma sai yayi min allurar mantau na awa ɗaya baya,

Ɗayan videon da nayi musu tun farko shine wanda yawancin ku kungani videon da na turo, bayan sunyi min allurar ban san adadin da nakai ba agun su, sai farkawa kawai nayi naganni a cikin falon su, da mamakin abun da yakaini tun kan inyi wani tunanin saboda har loƙacin ban dawo cikin hayya cina ba,

Ina gurin bansu san na farfaÉ—o ba, sai shi Wazirin yafara yin waya yana cewa zaije wata unguwa ance masa unguwar da bokaye da yawa zaije ya lalubo wani bokan da zai kuma yi musu aiki,

Da naji haka sai kawai na koma na kwanta saida nagama jin sunan inda zashi, har ya tashi ya fita daga falon nikuma da naga ya fita sai kawai nabi bayan sa saboda loƙacin matar sa ta koma ciki kuma dai maganar gaskiya na manta mai ya kawo ni ɗin sakamakon allurar da sukayi min, saidai kawai naji yace boka nikuma na yanke shawarar binsa inga inda zashi,

Bayan na fito kuma har na nufi hanyar gate zan bishi danni nama manta ana zuwa a mota, har na kusa zuwa kuma shine Papa ya kirani dalilin da yasa banje ba kenan,

Da na dawo kuma na shiga ɗakina ina ɗaukar wayata sai naga wannan videon yafaɗa yana zaro wayar sa daga aljihu videon yayi playing ɗinsa yana nuna wa wasu wasu kuma suna jiyo muryoyin Waziri da matar sa, saida suka gama ji tundaga farko har ƙsrshe sannan ya kashe wayar ta mayar tare da ci gaba da cewa "bayan nagani na tuna komai duk abun da yafaru na tuna, nayi mamakin ta yanda akai yazo wayata amma sai nabar ta wannan,

Tunawa da yafita É—in yasa nayi saurin kiran abokina nagaya masa unguwar da yake sai akaci sa'a ma ashe unguwar suce inda Wazririn zashi, sai nagaya masa abin dake faruwa nace inaso yasamomin shi yana nan unguwar yazo neman malami a unguwar ance masa da akwai malamai a unguwar yasaka masa ido akan sa idan yazo yasaka wani yataresa,

Rasa inda yake mukayi, sai Washe gari nasamu na ɗauki wayar Papa na ɗau number Wazirin a wayar sa, sannan na kirashi da wayata, yana ɗagawa nace masa naji yaje wata unguwa yana neman malami nasan inda wani malami yake aikin sa kamar yankan wuƙa bama a bashi kuɗi sai aiki yayi kyau baiyi wani tunanin ko waye niba kawai ya amince min nikuma sauna haɗasa da abokina nace yayi shigar bokaye muka samu wani ɗan daji,

Shikuma Wazirin yaje yasame shi suka gama magana sai Waziri ya buƙaci da shi bokan yazo cikin masarautar suna da guri mai kyau sai su haɗu gaba ɗayan su acan yanda zasu fi tattaunawa da kyau,

Da wannan damar muka samu suka haÉ—u agu É—ata gaba É—ayan su ta yanda basai na sha Wahalar bincike akan kowa ba, daga nan muka ringa shirya abun da zasuyi, ranar da suka taru nikuma ranar nasamu na É—auke matar waziri sannan nasaki videon ya kashe matar sa ta yanda duk wanda yagani zai yarda, kuma yanda na tsara Alahamdulillah komai ya tafi yanda yakamata har zuwa ranar jiya da muka shirya bayyana muku hakan, yanzu gasu nan zamuji ko idan da wasu sai su fito dasu idan kuma sukaÉ—ai kowa zai faÉ—i laifin da yayi da kansa sannan a yanke musu hukuncin da ya dace da su, dan barin wata matsalar ce,

Shiru yayi bayan ya gama maganar ya maida duban sa ga Papa yace "papa bissmillah gasu nan, ya miƙa sauran baya nin ga Papa,

Papa zaiyi magana gwaggo tayi caraf ta rigasa, da cewa ai yaron nan babu wani abu da za ace ka faɗi komai kayi ƙoƙari yanzu kawai ta bakin su muke jira muji dalilin da yasa su aikata haka,

Jinjina kai Papa yayi, yace "hakane mai sunan baba yayi ƙoƙari babu abun da zance yanzu sai muji ta bakin su inji ko nayi musu wani laifinne da yasa na cancanci wannan ɗanyen hukuncin na rabani da iyalina, musamman ku ya kalli Waziri da matar sa Ammah,

shiru sukayi babu wanda ya iya cewa ko uffan,

Meer ne yace matso kusa da mai gadin yace "kai É—ago dakai zamu fara, waye kai? sannan kuma wa kakeyiwa aiki? mai ya kawo ka cikin gidan nan?

kuma kar ka ɓata mana loƙaci muna sauraron ka,

Ɗan ɗagowa yayi kaɗan ya kalle sa, yasake sauke idon sa da baigama buɗewa ba har yanzu, shiru yayi na ƴan loƙuta kafin daga bisani yafara magana,
Chapter 35 · 0% Book details