← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 103

Sashe 83

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai jira tayi magana ba kawai yajata da ƙarfi yana cewa muje muje muje muje sauri kiyi sauri kar wani abun yasame ta, dan ke zan kama, haka yaita tayi mata surutu ita mamakin sama ya hanata yin magana, inajin tunda take dashi bata taɓa ganin sa irin hakaba, sai taga gaba ɗaya ya sauya mata kamar bashi ba yanda yake wasu abubuwan,

Saida suka shiga ɗakin sannan ya sake ta, loƙacin da suka shiga Papa yana zaune yana ta jiran shigowar su daman dan harɗan gyangyaɗi yafarayi a zaune,

yana ganin shigowar su yace yauwa tun É—azu nake jiran ku, har na fara gyangyaÉ—i a zaune,

"Me yasa baka biyo taba, tana can ta addabi rayuwa ta, wai ita acan zata kwana ni kuma nace bani kwana da ita tunda ita ba mata ta bace, saidai ta dawo gun tsoho irin ta me ƙasusuwa kar inje ina bacci inji an fasa min kai da ƙashin hannu, da ƙyar fa ta haƙura yanzun ma sai da nakawo ta baka gani ba jawo hannun ta nayi ta ƙarfin tsiya,

Kasaƙe sukayi dukan su suna kallon sa Papa na tunanin yaushe ya iya magana haka dan shi daman basu saba magana ba har gwanda ma ita Maama sunayi wani loƙacin, ita kuma tana mamakin ƙaryar da yayi mata wai tace sai ta kwana a ɗakin sa dan ƙarya ma da saida ya jawota ta ƙarfin tsiya sannan ta taho,

Maama zata sauke masa magana, ya tsugunna ya suri Ameesha ya saɓata akafaɗa, yace "to Allah bamu alkhari old men and old women,

Yana jinsu suna yi masa tsiya amma yaƙi sauraron kowa yayi gaba abun sa ya fita daga ɗakin yabar su da kunfar baki,

Yana fita ya sauya fuska yana hararar ta ta gefe, badan yau yana cikin farin ciki ba, kuma yana ɗan tausayin ta akan abun da yafaru, amma badan haka ba yaseen da yana fitowa zai sake ta aƙasa,

Da farko ɗakin su yayi niyar kaita sai kuma ya tuna da maganar Maama kar ta farka ta ganta aɗakin ga ba kowa babba akusa da ita, hakan zai iya ƙara sakata cikin wani halin,

Ɗakin sa ya shiga da ita, yana zuwa ya shimfiɗe ta akan gado sai kawai ya tsinci kasa da ƙurawa fuskar ta, idon ta ya kunbura ga sahun hawaye ya bushe, bakin ta kuma ya ɗan bushe kaɗan yanda de yakeyi idan mutum ya daɗe yana kuma kuma yayi shiru baiyi magana ba zakuga bakin mutum na ɗan bushewa to itama irin haka yayi,

Sauda yagama ƙare mata kallo sannan ya janye idon sa, duk da yanda zuciyar sa take fusgar sa tana ingiza shi, akan wasu abubuwan, amma kuma yana so yaja girman sa kar ta ƙara rainasa akaro na biyu,

bargo ya jawo ya rufa mata shikuma sai ya samu gefenta ya kwanta tare da jan blanket É—in shima ya rufa kuma har kansa,

Wajen minti talatin bawan Allah nan yakasa bacci sai wasu wasu zuciyar sa take masa takasa kwantawa, bare yayi baccin daga ga ta ayyana masa wannan sai ta ayyana masa wancen, tsaki yaja tare da yaye bargon ya fito da kansa, yana fitowa, idanun sa suka sauka akan fuskar ta da tajuyo site É—in da yake,

Ƙura mata ido ya kumayi yana ƙara ayyana abun da zuciyar sa take raya masa, yana ayyana hakan tare da hasaso abun aransa yake, ji yayi jikin shi ya wani ɗau ɗimi loƙaci ɗaya wani irin yimmmm yafara ji a duka jikin sa............,
[24/11, 12:54 am] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                      49
                  
........Ƙura mata ido ya kumayi yana ƙara ayyana abun da zuciyar sa take raya masa, yana ayyana hakan tare da hasaso abun aransa yake, ji yayi jikin shi ya wani ɗau ɗimi loƙaci ɗaya wani irin yimmmm yafara ji a duka  jikin sa...,

a hankali ya lumshe fararen idanun sa masu ɗauke da zara zaran gashin ido, rufesu yayi tsawon ƴan mintina yana jin wani abu na ƙara ratsa sa, buɗesu ya kumayi ya sauke akan ta,

Ji yayi kamar jansa ake haka yaja jikin sa yana matsawa kusa da ita, bai tsaya ba saida yayi kamar zai shige jikin ta, hannun sa ya É—aga ya É—ora sa a daidai saman west É—in ta, yaÉ—an matso da ita jikin sa kaÉ—an, jikin su na gogar na juna,

Wani ɗumi yaji ya ratsa sa me daɗi take yaji wata nutsuwar ta ƙara sakko masa, ji yayi hankalin sa ya ƙara kwanciya, yana fidda wani irin sanyayyen numfashi, yayin da yake jin nata na sauka akan fuskar sa,

bargon ya jawo ya lulluɓe su har kawunan su, hannun ta ya kamo shima ya zagayo dashi ta bayan sa ya rungumo ta jikin sa gaba ɗayan, (nidai ina daga bakin ƙofa ina kallon hannun sa yana ta yawo ta cikin bargon bansan ina da ina yake taɓowa ba....su o'o da o'o ankasa kunne aji me zai faru to asuba ta gari sai da safe...😜😜😹)

_Washe gari_

Kiran sallar farko Meer ya tashi daga baccin da yake me daɗi, musamman da ya haɗasa da mafarkai masu daɗi sai yajisa ya tashi garau, ita kam har yanzu baccin ta take itama hankalin ta kwance, dan duk wainar da akeyi batasan da ita ba, kamar wacce tasa wani abun haka ta ringa, shi har mamaki ma ta bashi da yasha farkawa yaga ko ta tashi amma sai yaga baccin ta kawai take, sai ya koma har yanzu kuma baiji tayi ko motsi ba, a hankali ya zare jikin sa, ya sauko daga kan gadon kai tsaye bathroom ya nufa, ba jima wa ya fito jikin sa sanye da towel alamaun dai wanka yayi, cikin sauri yafara shiryawa gudan kar sallah ta wuce sa, kuma kafin ya fita saida ya haɗa duk wani abu da zai haɗa, saboda badawo zaiyi ba, daga can zasu wuce kamar yanda sukayi wa Abban Ameesha alƙawarin da asuba zasu fita shiyasa ya shirya koman sa yaɗau maƙullin mota,

Har yakai bakin ƙofa sai kuma ya dakata tare da juyowa, komawa yayi zuwa bakin gadon yana zuwa ya daki jikin fuskar gadon a wajen saitin kanta, amma bata motsa ba, mayar da dukan yayi kan kumatun ta, yana ɗan bubbugawa, yace "ke.! Ke !!

Saida yayi da ƙarfi sannan ta fara motsi kaɗan kaɗan amma bata buɗe idon ta ba, tafara miƙa,

Kallon ta yayi, sai yayi saurin kawar da kansa, yace "ki tashi loƙacin sallah yayi,

"Um hum, tabasa amsa sai can kuma tayi saurin buɗe idon ta dan sai daga baya ma, bayan ta bashi amsa muryar tashi ta dawo mata akai hakan yasa tayi saurin buɗe idon ta, dan tabbatar wa da kanta abun da taji, saidai kuma loƙacin da ta buɗe shi har ya juya ta nufi hanyar ƙofa,

Kan tayi wani yunƙuri ma har ya fice daga ɗakin, tashi tayi zaune tana me mamakin abun da yakawo nan, jikin ta ta shiga bi da kallo wai ko yayi mata wani abun amma sai taganta a yanda take, tunawa tayi ɗakin Maama ta kwanta to yaushe ma aka dawo da ita nan bata sani ba,

Ganin babu me bata amsa yasa ta sauko daga kan gadon tana ƙara yin miƙa dan gaba ɗaya jikin ta wani iri kasala take ji, gashi yau suna da jarrabawa danma wannan ce final saura biyu suka rage musu sunayi sun gama gaba ɗaya, maimakon ta nufi banɗakin sa sai kawai itama tayi ficewar ta daga ɗakin zuwa nasu ɗakin......,

Suna idar da sallah basu tsaya wani ɓata loƙaci ba, suka wuce, su su huɗu suka tafi, Meer Abban Ameesha sai Sam da Bosaya......,

Da wuri suka sauka agarin Gombe, direct inda aka kwatanta musu nan suka je, tare da jagoran cin wani masanin garin da tun suna hanya, Ayuba yasa akazo aka tare su, harda Æ´an sanda ma ya haÉ—a musu,

Gidan babba ne sosai acan bayan garin Gombe ala gina shi dan babu wasu mutanen ma da sukayi gini a kusa dasu,

A tare suka shiga gidan, dan suna bugawa me gadi ya buÉ—e kawai sukabi takansa a kayi masa duka, dan ko tambayar sa ma basu tsaya yi ba, sukayi maganin sa tare da danna kai cikin gidan, falo ne babba gashi da komai na more rayuwa a ciki, duba É—akunan suka shiga yi amma duk inda suka buÉ—e, sama suka hau nanma suka ci gaba da bincike ko ina, duk da gidan babba ne amma basa tunani akwai inda basu duba, dan ba zuwa sukayi kowa ya kama hanyar sa, ga gidan da uban É—akuna sai kace gidan yari, ko gidan haya,

Wajen minti ashirin suna abu guda basu same ta, har sun fara tunanin kode waccen ɗin ƙarya ta gaya musu bata, ciki,

Muryar wani ɗan sanda sukajiyo yana cewa ga wata ƙofar amma bata buɗuwa ko, duk waɗanda sukajiyo sa duk sukayo hanyar da sauri, tun iya su kaɗai ne suka ki sai gashi kowa ma yaji nan suka dawo suka taru ana ta tunanin yanda za a ɓude ta,

Meer ne yacewa Sam da Bosaya su haɗa ƙarfi kawai su buge ƙofar dan bazata buɗuba, nan duk suka tattaro ƙarfinsu suka saka ƙafa atare suka doka ƙofar da ƙarfi, taji maza bugu ɗaya suka ɓale ta,
Chapter 83 · 0% Book details