← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 103

Sashe 90

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma a cikin shekarun, Alahamdulillah cikin ikon Allah su Ameesha sun kammala karatun su, inda suka samu kyaututtaka masu tsoka, daga cikin makaranta saboda ƙoƙarin su da jajir cewar su ta kowane fanni, Ameesha da Azeema suka karanci Law, sumayya kuma takaranci, ɓangaren accounting, inda su twins kuma suka karance ɓangaren harkar zanen gida, su kuma anan tasu fasahar take, ko waccen su yanzu ta canza sun zama cikakkun ƴan mata, kyawun su da hasken fatar su duk sun ƙara fitowa, daman Azeema ta girme su, ita da sumayya, dan haka sun ɗan fisu girma, twins kuma ƙiba kaiɗai suka ƙara, Ameesha kuma batayi kiba ba, kawai ta mulmule, ƙirjin ta ya ƙara cika, ƙasan ta kuma ya baɗe, masha Allah akwai diri iya diri, irin jikin mahaifiyar ta tayo, saidai bata kai mahaifayar ta tsawo ba, domin ita doguwa ce, sai haske da ta kumayi, tayi wani fresh da ita ta ƙara kyau hancin nan yaƙara fitowa, fatar jikin suwail suwai kamar ba karatu take ba, ko da yake ba wuya suke ci ba a wajen karatun makarantar kuɗi suke, dole ta ƙara murmure wa,

Yau suke murnar graduation ɗin su, inda mutane daga cikin masarauta, har da ƴan waje irin su Bossay da su Shettima mutane dai da dama sun shirya sunje haka suka ringa zuwa mota mota, dan guri na musamman ma aka bawa family ɗin su, domin kowa yasan su  a makarantar akwai ƙoƙari, gasu dashi ga rai kowane malami yasan dasu......,

Guri ne ƙayataccen guri kana gani daman kasan ba taron ƙananu bane, na masu shine,

Nan aka fara gudanar da taro cikin tsari inda aka fara kiran mutane an basu kyaututtakan yabo, idan aka kira ɗanka sai ka fito ka taya sa karɓa sannan ayi maku hoto, za abaka wani abu kamar zare amma yana da ɗan faɗi kowa anrubuta masa sunan da da sunan makaranta idan aka baka kai kuma saika saƙalawa wanda yazo karɓar maka ɗin,

loƙacin da akazo kan Azeema Shettima yayi ƙarfin hali shi zaije saboda matar sa dan haka shi zai karɓar mata, Sam kwa da yaga haka shima yace shi zai karɓarwa tasa matar (oh ni ƴar nan ko yaushe akayi auren da suka zama matansu,)

Babu wanda ya hanasu haka Shettima na dawowa aka kira Sumayya shi ma Sam yaje ya karɓo mata,

Manyan da suka ga haka sai suka to su basai sunje ba yaran duk suje su karɓo musu, sai kuma aka fara tunanin wanda zai karɓarwa Ameesha da Amra, domin ita Hamra, Hamza ne zaiyi caraf da ita, acikin shekarun har ta bayyana mata son da yake mata saboda ya yaba da hankalin ta shiyasa tunda yarasa Azeema ya fahimci soyayyar dake tsakanin su da Shettima sai haƙura ya koma kanta yayi tunanin ma baza ta amin ce ba amma sai ta amince masa da wuri ma baisha wata wahala ba, shiyasa itama da aka kirata yaje yabkarɓar mata,

Daga ita kuma aka koma kan Amra anata tunanin yanda za'ayi sai kawai Hamza yaje ya gurin Bossay yace yaje ya karɓo mata, da ƙin zuwa yayi saida yaji anƙara kiran ta sannan kawai ya daure yaje ya karɓo mata ita kanta tayi mamakin ganin sa, dan tana tunanin ita waye zai karɓar mata kowacce acikin su sarauyin ta yazo ya karɓar mata ita kuma gashi bata da saurayi, amma ganin Bossay yasa taji daɗi sosai,

yanzu tunanin su ɗaya yanda zasuyi da Ameesha dan sun san Meer ba ya ƙasar da sai suka shi ko ta dole ne yaje yabkarɓo mata, amma gashi baya nan, tun kan azo kanta, sai Abuu yace shi zaije ya karɓar mata ai ƴarsa ce, amma sai Maama tace a'a a matsayin ka na sarki bakai ya dace kaje ba,

Suna cikin neman me zuwa sukajiyo ana kiran sunan ta, aka kira ta saubiyu babu wanda yaje hakan yasa ta fito ita kaɗai sai aka fara sanar wa ina ƴan uwanta suke, hakan yasa Abban ta miƙewa yace ni bari inje in karɓar mata kawai, nan duk suka amince daman inba shiba waye zaije,

Cikin takun sa na musamman me cike da nutsuwa ta musamman ga ƙasaita da cikar kamala, yaci wasu shegun ƙananun kaya masu laushi rigar fara ce me dogon hannu sai wata ƴar top balack da yaɗora akai gaban rigar a buɗe yake, sai kuma baƙin wando, takalmin ƙafar su both ne fari ƙal kalar rigar sai black p cap da yasaka, fuskar sanye da face mask, idon sa kuma ya saka wani siririn space (galas ɗin ido) ga hannu wansa da suka ji wani fitinan agogo, ɗayan kuma yasaka masa wani silver ɗin abun hannu, sai wata azurfa me kyau da tsada,

Abban Ameesha bai lura dashi ba saida yanadaf da zuwa, sai kawai ganin sa yayi agaban gurin hakan yasa shi saurin dakatawa, cike da wani farin ciki da ya ziyarci zuciyar sa, a hankali ya fara ja da baya da baya,

Ameesha idon ta na kan Abban ta dan haka bata san da zuwan sa, saida taga Abban ta ja da baya, kuma idon sa yana kan wani gurin, tana tunanin me yasa shi yake ja da baya, bayan kuma yasan shi ake jira,

Tsayiwar mutum taji a gaban ta, tare da wani irin ƙamshi da ya daki hancin ta, idon ta' ta sauke a kan ƙafar sa, tundaga nan ta fara binsa da kallo gaban ta na ƙara tsanan ta faɗuwa, a hankali ta sauke idon ta akan fuskar sa, tsorata tayi da ganin sa duk da de har yanzu tana kokwanton shine ko bashi bane, dan bata taɓa tsammanin sa, tasan bazai taɓa zuwa ba,tunanin tane ya tsaya akan ai bashi bane bama, kuma duk wannan abun idon ta na kansa takasa janyewa,

Ganin kamar tana yi masa kallon rashin sani yasa ya ɗan saka hannu ya juyar da p cap ɗin gefe sannan yasa hannu ya zaro face mask ya cire sa gaba ɗaya, asalin fuskar sa ta fito, shima ya ƙara kyau yayi wani mugun haske duk da de daman da hasken sa, amma yau hasken nasa kamar harɗaukin ido yake, ko dan gemun da ya tarane yasa hasken sa yaƙara fitowa dosai,

Ai da ta gansa saida ta rufe ido ta buɗe domin ganin shi tayi kamar aljani, saboda tsabar kyaun da yayi, tana buɗe idon ta, ta kuma yin wani gamon da saura kaɗan zuciyar ta ta tsinke sakamakon wani murmushin gefen baki da yayi har saida farin haƙorin sa ya fito, yana ɗage mata gira ɗaya, da ɗan wara idon sa ta cikin glass ɗin, irin yadai ɗin nan, ko da magana,

Hakan ba ƙaramin sata yayi a cikin wani irin yanayi da ita kanta bata san sunan saba, tunda take bata taɓa gani koda baki ya motsa ba da niyar yin murmushi,

Maganar me sanarwar ce ta katse mata tunani ta sakamakon miƙamata kyautar da akayi tare da shi suka miƙa hannu wajen karɓa, yana sane wajen karɓa ɗin ta ƙasa sai ya haɗa da hannun ta ya ruƙo, da sauri ta ɗago ta kalle sa, tana ɗagowa sai ƙes aka ɗauki hoton su, shi kuma suna haɗa ido sai ya kashe mata ido ɗaya, da sauri ta sauke idon ta ƙasa,

Bayan wanna Saida aka ƙara mata da wasu kyaututtukan kan, kuma duk a haka suka karɓa, duk karɓa sai ya haɗa da hannun ta, tarasa gane kansa,

Bayan angama bata duk wani abu da za'a bata sannan aka bata abun da zata rataya masa, ɗin kamar ta fashe haka take ji, daurewa kawai take, dan ƙafar ta har karkarwa take, ga wani gumi da  yake tsatstsafo mata ta cikin jiki,

Riƙe abun tayi a hanu ta kasa rata ya masa, ɗan matso da bakin sa yayi, gurin kunne ta, murya can ƙasa ƙasa yace "ko sai an ɗaga ki ne naga kamar tsawon ki bazai kai ba ko,

Rumtse idon ta tayi tana me ƙara jin taƙaicin abun da yake mata, ji tayi gwanda ma ta rataya masa a wuce gurin, tunkan ya kuma yi mata abun da zata jaɗiyi zuciya, ko ya bata kunya  a gaban mutane,

Yana matsawa ta kawar da idon kawai ta ɗaga abun, da gaske tsawon ta bazai kai ba, saida tayi ɗage sannan tsawon ta yakai amma dake ɗan rainin hankali ne tana daf da zata saka masan, sai kawai yayi baya, saura kaɗan tafaɗi sai ya riƙo hannun ta,

Wasu daga gurin duk saida sukayi mata dariya dan wasu a tunanin ko ya da ƙanwa ne, wasu kuma direct suka ce duk yanda akayi masoya ne, shiyasa tun farkon zuwan sa MC bece komai daman itace ta ƙarshe, baiyi duba da baƙin da suke ba, ya rabu dasu, dan sun matuƙar burgesa, masu yi musu dariya sunfi yawa,

Kallon sa tayi kamar zata fashe da kuka, dan ta ƙaici, da ya riƙe hannuwan nata, sai ya sunkoyo da kansa daidai tsawon ta sannan ya ɗaga hannun suka zura abun atare, sannan ya sake ta, haɗa mata kyautar akayi aka basa, ya karɓa, maimakon ya tafi sai kawai ya riƙo hannun ta, yaja ta har zuwa inda suke zaune, ya ajiye ta saida yaga ta zauna sannan yayi bar wajen,

Sarai yasan inda family É—in sa suke amma ko inda suke bai kalla ba, yabi ta hanyar da yabiyo ya koma gurin motar sa,

Ameesha kam tana zaune ne kawai amma duk wata nutsuwa ta bargangar jikin ta, bata tare da kowa, tunanin nakan wannan sabon lamarin da Meer yazo mata dashi, ba zato ba tsammani, Su Azeema na ta tsokanar ta amma babu wanda yasamu da ma ta tanka masa koda da 1 word ne, hasali ma bata tantance abun da suke faÉ—a, gaba É—aya hankalin baya gurin, tama rasa kuma wane irin tunani zatayi akan hakan,

Family su kam babu wanda baiyi mamaki ba suma, sunyi matuƙar mamakin sa kuma sunji daɗin hakan,

Daga nan aka cigaba da gudanar da taron ƙarfe biyu daidai aka rufe taro da addu'a aka sallami kowa,

Nan aka shiga taya juna murna ana hotuna WaÉ—annan suzo su gaida iyayen wasu haka suka ringayi, anci ansha, anyi hotuna ba a dadi, daga nan kuma kowa ya fara watsewa,
Chapter 90 · 0% Book details