← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 103

Sashe 2

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meer da taƙaici da mamakin kalaman ta suka isheshi tana cikin maganar cike da ɓacin rai jijiyoyin wuyan sa har sunyi raɗau raɗau dasu idanun sa sunfara canza kala, tana cikin maganar baisan loƙacin da ta kwashe ta da wani irin rikitaccen mari ba tare da kai mata shaƙa awuyan ta ya haɗata da jikin bango, jikin sa duk sai rawa yake tunda yaji sun ambatar masa iyaye hankalin sa yafara gushewa idanun sa suna neman su ƙafe saboda wani tsabar taƙaici da baƙin ciki da yake jin suna taso masa daga ƙasan zuciyar sa ji yake idan baikashe taba agunnan hankalin sa bazai taɓa kwantawa ba, yana cikin shaƙar tata, Waziri yafara ƙoƙarin jansa ta baya amma ko gezau baiyi ba, wani sirinji ya zaro daga cikin aljihun sa taf yake da ruwa aciki ko ruwan meye Allah masani, Meer bai ankara dashi ba sai jin saukar allaura yayi agefen wuyan sa take kansa ya fara juya masa tun yaba gani har ganinsa ya ɗauke, a hankali ya shiga sakar mata wuyan saboda jikin sama gaba ɗaya ya saki, suna kallon sa har yafara tafiya zai faɗi saima matsawa da Waziri yayi dan kar ya faɗo kansa a haka har yakai ga ƙasa ya faɗi agun,

Numfashi ta shiga saukewa na wahala dan ba ƙaramin shaƙa yayi mata ba, ruwa Waziri ya ɗauko mata ya bata ta shiga sha da sauri da sauri saida ta shanye suka sannan ta jefar da robar tana ɗan shafa wuyan ta, Ta kalli Waziri tace Allah kuwa yaron nan baida hankali ƙarfi kamar na doki da bakayi sauri ba ai sai ya kashe ni kaji kuwa zafin da naji dan har na fara jin ƙamshin lahira,

Ɗan dariya Waziri yayi yace ke ai daga ganin zubin shi kinsan bazaiyi imani ba idan ya riƙe mutum yanzu dai ai munyi maganin ɗan iska, yau yaga samu yaga rashi, ta kalle sa cike da rashin fahimtar magananr sa tace "bangane ba yaga nema yaga rashi,

Jinjina mata kai yayi yace"ƙwarai kuwa yaga samu yaga rashi dan kwa yana tashi babu abun da zai iya tunawa mugama gaya masa komai kuma mungoge masa sanin wannan allurar da nayi masa ai ta mantau ce ta idan ya tashi sai tambayi abun da ya kawosa nan ke ina taƙaice miki ma saidai mukai shi makwancin sa dan bazai iya komawa da ƙafar saba,

ÆŠan zaro ido tayi tace kana nufin zaiyi losing memory É—insa ne gaba É—aya,

"A'a ba haka nake nufi ba ina nufin ba kawaidai zai manta abun awa biyu da yafaru dashi na baya, zai cigaba da harkar gabansa zaima manta da abun da yakawo sa gaba ɗaya bare kuma ya tuna abun da muka gaya masa ko ɗaya bazai tuna ba.........✍️✍️

*Plsss ayi malej da wannan wallahi yau bamu samu wuta ba,*
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

_____A'a ba haka nake nufi ba ina nufin ba kawaidai zai manta abun awa biyu da yafaru dashi na baya, zai cigaba da harkar gabansa zaima manta da abun da yakawo sa gaba É—aya bare kuma ya tuna abun da muka gaya masa ko É—aya bazai tuna ba.........,

Wata iriyar shu'umar dariya ta saki harda tafawa tace "shiyasa nake ƙara sonka na wajena aikin ka na kyau, yanzu meye plan ɗinmu na gaba, dan naga alamar yaron nan da zafin sa yake bazai raga mana ba dole mu fara kawar dashi, kar muje muna kallon ruwa ƙwaɗo yayi mana ƙafa,

Kallon ta yayi yace kar ki damu dashi a rana ɗaya zanyi maganin sa in yasan wata ai baisan wata ba, daga yanzu duk wani motsin mu zai kasance akan idon mu zan zuba masa idanuwa akansa duk inda zai shiga za a kawo min rahoton sa daga zarar naga zaiyi min hauka zan nuna masa na fisa iyawa, kedai kibar komai a hannu na dan wannan ba wani babban abu bane da zaifi ƙarfin na kar kisanar da kowa a ƙungiya, bare labari ya riske shi nasan zaifi ɗauka da zafi magana har takai ƙarshe, a zo afara tsari ba nutsuwa, gwara abi komai a hankali asannu komai zai dawo normal labarin zai ƙara shuɗewa kamar da za a manta dasu kamar yanda aka yi abaya,

Ah daman ni wazan gayawa, ai yaron nan fa yaban tsoro wallahi bakaji shaƙar da yayi min ba nifa ina tunanin ma anya ba ya tare da aljanu masu ƙarfi ajikin sa,

Waziri ya ɗanyi murmushi irin nasu na manya yace "ke bakiga zubin saba daman ai kinsan ya riƙe mutum bazai ji da daɗi ba, yanzu dai duk ba wannan ba ɗauko min wayata inkira Ab........, Shiru yayi da maganar yana kallon wajen ƙofa sannan ya maida kallon sa ga matar tasa yace "kamar motsin mutum nake ji fa yayi maganar yana kallon ta da kyau,

Ɗan maƙale kafaɗa tayi tace anya kuwa gaskiya bana tunanin akwai wani ni banji motsin komai ba amma dai bari induba ingani tafaɗa tana ƙarasa miƙewa tsaye,

Tana tashi sai wayar sa ta ɗauki ruru hakan yasa ta dakata da niyar zuwa wajen ƙofar ta nufi inda wayar sa take, tana ɗaukowa tace kaji ɗan halak ana maganar sa saiga kiransa, ƙarasawa tayi wajen sa tare da miƙa masa wayar, Ya amsa yana ƙara faɗaɗa murmushin fuskar sa yana karɓar wayar sai sukaji ƙarar waya ƙes kamar an ɗauki hoto da sauri ya ƙara maida kallon sa ga bakin ƙofar, Sai kuma yaƙara kallon ta kamar ɗazu yace "kinji abun da naji yanzu taɓe baki tayi tace haba kaidai wallahi kana neman kazama ma tsoraci ba wani abu da naji kasan ance marar gaskiya ko a ruwa gumi yake shiyasa abubuwa suka fara yi maka gizau amma dai bari dai in duba maka kaga zahir saika daina tsorata haba sai kace bakaiba kana neman ka canza da tsoro,

ÆŠan murmushi yayi tare da amsa wayar yana jinjina kai dan ya yarda da maganar ta ta,

Ita kuma ta nufi bakin ƙofar tana ƙara tsokanar sa da matsora ci tana dariya.......,

_______Cikin zaro ido cike da tsoro da fargaba tayi baya zata faɗi  tana shirin fashewa da kuka, Azeema dake gefen ta tayi saurin toshe mata baki tare da janta baya da sauri suka bar gurin ƙofar gudun kar asirin su ya tonu,

suna fitowa waje Ameesaha ta fashe da kuka ta rungume Azeema, Azeema da itama jurewa kawai take tayi saurin  kamo hannun ta suka bar gurin gaba ɗaya basu nufi inda mutane suke ba can bayan wani waje suka nufa gurin da ba mutane a wajen,

Saida suka je sannan Azeema ta zaunar da ita akan wani É—an tudu ta dafa kafaÉ—ar ta tace besty plsss dan Allah kiyi shiru ki nutsu miyi magana, kada wannan maganar ta sa kifita daga cikin hayya cin yakamata ki aro jarumta kisaka wa kanki bafa mutuwa yayi ba,

Cikin kuka Ameesaha tace "besty bazan iyaba waɗannan mutanen sunfi ƙarfi na kinfa ji me sukace sai sun tarwatsa rayuwar mu shin me muka tsare musu gwanda ma kawai inje ingaya musu mubar gidan nan nidaman hankalina bai kwanta ba acikin gidanan idan bamu barmusu gidan ba kashe mu zasuyi mumu duka gashi yanzu sun fara takan dadda ta wataƙil ma yanzu sun kashe ta tana faɗar haka taƙara fashe wa da kuka tana faɗawa kanta,

Riƙeta Azeema tayi tace "kidaina faɗar haka in sha Allah ma dadda bata mutu ba tana nan da ranta zata dawo ku cigaba da rayuwa kuma acikin gidan nan kisa Allah aranki babu abun da suka isa suyi muku wanda Allah bai muku ba, abun da nakeso dake shine kiyi shiru, nifa banma ga abun tada hankali sosai ba tunda idan suna ganin shi baida shaida mu ai muna da ita kama ta yayi ma ki godewa Allah da Allah ya kawo mu akan loƙaci kisan ba yin kanmu bane Allah ne ya aiko mu, dan ya taimake kune shiyasa mukazo gurin, ki godewa Allah yanzu da bamu zoba da shikenan kamar yanda yace yaga samu yaga rashi hakan zai kasance saidai kuma gashi ta Allah ba tasu ba samun ya tabbata kamar yanda yace sai da ƙwaƙwarar hujja za a yarda dashi to gata munsa mu duk wanda yaji wannan maganganun nasu ai dole ya yarda, ko ya kikace kamata yayima kiyi murna ba kuka ba, please besty kiyi shiru kiban hankalin ki mu tattauna akan maganar nan kinji,

Shiru tayi tana nazarin maganganun ta atake kuma maganganun tsohonnan suka shiga dawo mata ƙwaƙwalwa tabbas yanzu ta yadda wanda zai nuna maka soyayya a fili ba lalle yazama masoyin ka abaɗini ba idan tayi la"a kari da Waziri da suke uwa ɗaya uba ɗaya da papa amma ji yanda yake da mugun nufi akansa da iyalen sa, alhalin a zahiri nunawa yake babu wani abu to ɗan uwanka ma da kuka fito ciki ɗaya ma yana zalintar ka ina kuma ga wanda ba haɗin iya bare na baba, babu abunma da bazai iya aikata maka ba,

Azeema ce ta ta taɓota ganin tayi shiru bata ce komai ba, yasa ta ɗan dafa kafaɗar ta tare da kiran sunan ta,
Hakan yasa Ameesha katse tunanin da take tare da É—agowa tana kallon Azeema, Hannu Azeema tasa tashiga yi goge mata hawayen ta, tace "tunanin me kike?

Ɗan murmushin yaƙe Ameesha tayi ta girgiza kai tace "ba komai.
Chapter 2 · 0% Book details