← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 103

Sashe 30

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumy da taga kamar baida niyar tashi, sai ta miƙe tsaye, tace "nifa bazan ƙara zama dakai guri ɗaya ba, ka kaini gida bazan zauna da kai ba, ana min wani kallon daban,

cire hannun sa yayi daga tagumin da yayi haɗi da miƙewa tsaye, yana zuba mata jajayen idon sa duk kaucewar da yake kar su haɗa ido amma yanzu da kansa ya zuba mata su yana kallon tsawon ƴan muntina, tun tana kallon sa itama har ta kasa ta kawar da nata idon,

"Kema zaki guje ni fine ga ƙofanan yanzu bazan hanaki ba tunda haka kika zaɓa kije, Nagode daman haka kike so ko to na rabu dake kema tunda baki so, kije ki ci gaba da rayuwar ki nima zanyi rayuwata ni kaɗai,

Daga jin yanda yake magana kai kasan yana cikin matsanan ciyar damuwa marar misaltuwa, jitayi ya bata tausayi ita taja masa yabar gidan iyayen sa amma gashi tana cewa zata tafi tabarsa cikin halin da yake ciki, da shine bazai taɓa yi mata haka ba to mai yasa ita zatayi masa haka bayan duk abun da yake dan ita yake dan yasama mata farin ciki yake,

Sunkuyar da kanta tayi murya cikin sanyin murya tace "kayi haƙuri,

"No kije kawai plss go yafaɗa yana nuna mata ƙofa,

Ƙin motsawa tayi daga wajen,

Ganin hakan yasa shi daka mata tsawa da ƙarfi tace " I say go, get out!!

tsorata tayi da yanayin sa bata san loƙacin da ta faɗa jikin sa ba tare da fashewa da kuka, tasa hannun ta gaba ɗaya tayi cropping ɗin tana ƙara sakin kuka, rumtse idonsa yayi yana maijin rungumar da tayi masa har cikin ransa, duk wani sassa na jikin sa saida ya amshi wani irin sabon lamari da shi kansa baisan wane irin yanayi bane,

Batare da ya buɗe idon sa ba yasaka hanu ya cireta daga jikin tare da janta yaje har bakin ƙofar ɗakin da kansa ya buɗe sannan ya turata waje cikin main office ɗin shi kuma ya rufe kansa acikin ɗakin dake cikin office ɗin,

Abakin ƙofar ta zube tana kuka tana basa haƙuri dan ji tayi bazata taɓa iya tafiya ba tabar sa ba,

Tun tana bashi cikin ɗaga murya har muryar ta tafara dishashewa, tana faɗa ƙasa ƙasa,

Sam shima yana bakin ƙofar kawai ya haɗa kai da gwiwa yana tunani, yana jinta amma yakasa haƙura ya buɗe mata duk da harcikin ransa yake jin kukan ta, amma bazai iya buɗe mata ba yanzu sai ta wahala so yake tafara jin yanda yake ji, da tanajin yanda yake ji da bazata ringa yi masa magana irin haka ba,

Tun tana jinta ƙasa ƙasan har yadaina jin ta hakan yasa ya tashi da sauri ya buɗe ƙofar, abakin gurin yaganta ta kwanta tana bacci, tsugunnwa yayi ya ɗauke ta ya shigar da ita ciki akan gadon ya kwantar da ita tare da rufa mata abun rufa, yana kallon fuskar ta da duk ta ɓaci da hawaye,

tashi yayi ya shiga wanka, yana fitowa yayi sallar nafila, sannan ya koma kan kujera ya kwanta da tunanin inda zai samamu su, zauna duk da yaje ya gargaÉ—i wasu koda anzo neman sa ko waye ace baya nan amma duk dahaka sai yabar cikin hospital É—in bazai ci gaba da zama ba, wayoyin sa ma ya kashe su gaba É—aya....,,

Adaren dai da ƙyar yasamu bacci ya ɗauke sa,

A ɓangaren momma ma haka dan har ta fishi shiga damuwa ma, gashi ita kaɗai abun yake cinta takasa gayawa kowa, sai juyi kawai take tana tunanin sa takasa bacci, Abban sa kam tunda ya tambaye ta mai yake damunta tace masa bata da lafiya ya tambaya tasha magani tace eh, daganan bai ƙara bi takan ta ba saboda shima ba acikin nutsuwa yake ba, dan shima da ƙyar yayi bacci,

Itakam takasa daga ta tashi zaune sai ta kwanta ko kaÉ—an takasa jin baccin (uwa kenan, Allah yaja da ran iyayen mu idan ba uwa ba waye zai iya yin hakan)

idon ta biyu har aka fara kiran sallah saida saidai tayi sallar asuba sannan bacci ya É—auke ta akan sallayar da tayi sallar,

_*Washe gari*_

Azeema na tashi ta fara haÉ—a ina ta ina ta dan tace da wuri zata tafi, Maama har tasama mata motar da za'a kaita gida, amma saida tasan yanda tayi akace Hamza ne zai kaita, sai Ameesha ta rakata har gida, sannan adawo da ita,

Azeema na murna tafiya Ameesha ta taƙaicin tafiyar ta ta,

wajen ƙarfe shaɗaya na safe ragama shirya wa tsaf taje tayiwa su Maana sallama da Dadda, har part ɗin Ummy sukaje tayi musu sallama sannan sukaje part ɗin su Hamra, nanma suma basuji daɗin tafiyar da zatayi ba atare suka ƙara fitowa sukaje part ɗin Salahudeen da tare dashi zasu tafi sai Papa ya hanasa yace yabari ba yanzu ba, hakanne yasa yafasa zuwa,

part ɗin suka ƙara komawa saboda har yanzu Hamzan bai fito ba kuma ta kirasa baiɗaga ba, shiyasa suka koma falon suka zauna zaman jiran sa, su Ameesha na ta tsokanar ta Allah yasa kar yazo Allah yasa afasa tafiyar yau, ko na yimaga bakin kar ta tafi,

Meer me ya fito daga É—akin sa zai fita saiga su Hamza nan sun shigo suma da sallama abakin kowannen su, su su uku ne, Hamza, shettima, bossay, da tun safe suke gidan saboda momma ta kirasu ta tambaye su ko yazo wajen su, sukace A'a shine daga nan kuma shettima yakifa Hamza dan yaji mai ke faruwa Hamza yaga masa iyakacin abun da yasani, shine yakira bossay suka taho gidan tare, tunda suka zo kuma suke kiran layi kansa amma akashe,

Shine momma tace suzo siyiwa Papa bayani dan bazata iya faÉ—a ba da kanta,

tsayawa sukayi tare da miƙawa Meer hannu suka gaisa ɗaya bayan ɗaya duk ya tsaya suka gaisa kuma fuskar sa ba yabo ba fallasa bazaka ce walwala yake ba kuma bai haɗe taba kamar kullum kawai dai asake take, ba ɓacin rai,

Tunda Bossay ya shigo idon sa yana kan Ameesha masoyiyar sa yayi kwar ta da yawa bai samu damar zuwa ganin taba a ƴan kwanan saboda tashin hankalin da shima yake ciki, tun ranar da sukayi waya da Rasheeda har yanzu komai yaƙi dawowa daidai, tace bata sonsa amma su dady da dad ɗin ta su dage aure ba fashi sunci gaba da shirye-shiryen su batare da sanin ita kanta Rasheedan ba,

Ganin ko kallon sa batayi ba irin kamar ma bata san da zuwan sa ba gurin,

A hankali yace babyna, yana kallon ta, bashi kaɗai ba gaba ɗayan su ɗagowa sukayi suna kallon sa, Meer ma zuba masa ido yayi yana jiran yaji wacece baby shidai tunda yake dasu bai taɓa jin an kira wata da baby ba,

Haɗe rai tayi tana turo baki gaba kamar zatayi kuma tace, "ba ruwana da kai kaje ka nemi inda babyn ka take shine tunda katafi kaƙi dawowa inganka sai yau zaka tuna dani saboda baka damu dani ba ko ƙara turo baki tayi a ƙarshen maganar har haɗa masa da harara,

Hakan ba ƙaramin burgeshi tayi ba dan haka yasama mata dariya yana cewa kaina bisa wuya nayi kuskure a yafe min nama dawo nan daga yau kullum muna tare,

Da sauri ta miƙe tsaye cike da farin ciki da kuma yarinta tace "dan Allah da gaske kake,

Kai ya É—aga mata yace "ina miki wasa ne,

Cike da farin ciki tayi kansa da sauri tana shirin rungume shi saboda itama tayi kewayar sa, bata kai ga ƙarasawa ba, Azeema tayi saurin riƙota, tace a wajejen kunnen ta tace "ke bakida hankali ina kike shirin zuwa, ko jan aji babu,

Kunya ce takama Ameesha karom farko kenan da gafara jin kunyar bossay komawa tayi ta zauna,

Su kuma duk dariya suka saka mata saboda yanda tayi yasa suka fahimci abun da take nufi, ƙarasa zama sukayi akan kujerun falon,

Sannan su Amra suka shiga gaida su, duk suka amsa, Amra kam tashi tayi daga inda take ta koma gefen Shettima mutumin ta,

Shima shettima idon sa yana kan Azeema kuma sarai yana lure da ita dan ko gaida shi batayi ba kuma bata kalli inda yake ba hakan ba ƙaramin ciwo yayl masa ba abun ya tsaya masa arai,

itama kuma a ɓangaren ta abun da take rayawa kenan mai yasa baiyi mata magana ba, kuma tunda ya shigo taji ta kasa sukuni gaba ɗaya mood ɗin ta ya canza tunanin ta duk ya koma kansa, duk da ga Hamza agun da loƙaci zuwa loƙaci sukan haɗa ido sai ya sakar mata murmushi amma takasa mayar masa dashi koda sauɗaya ne,

Bayan sun gama gaisawa Shettima yake sanar da Meer abun da yakawo su, suna so ayi musu magana da Papa,

Shine ake sanar dasu ai Papa tun safe ya fita baya nan, saidai su jira yadawo,

Daganan Meer ya fice daga falon yabar su aciki,

Sai Hamza ma ya miƙe yace "to ko zakujirasa ni bari inje indawo ko ku bincika gurin aikin sa idan yana nan sai asanar da ita ko ya kuka ce?

Bossay yace eh hakan ma yayi amma maiyasa baza mu tafi tare ba ina zaka daman naga kamar sauri kake,

ÆŠan shafa kansa yayi yace "eh wallahi zan É—anyi rakiya ne Madam zan raka gida tun É—azu ma zuwan kune ya tsayar dani, da mamaki Bossay yace wace kuma madam,

Da hannu ya nuna masa inda Azeema take,

Daram daram shettima yaji gaban sa na bada sauti, mai hakan yake nufi da ya kirata da Madam,

Take duk wani annuri na farin ciki ya É—auke daga kan fuskar sa ji yayi kamar zuciyar sa na tsintssinkeya ga wani rin bugu da take masa fat fat fat

Da sauri yasa hannu ya dafe saitin dan ji yake kamar zata faɗo, loƙaci ɗaya gaba ɗaya yanemi nutsuwar sa ya rasa,
Chapter 30 · 0% Book details