Sashe 87
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ke ko kunyar faɗin haka ma baki yi ba, koda yake banga laifin ki ba, daman munafukin mutum baka taɓa gane kansa, ai baza ki taɓa jin kunyar faɗar komai ba tunda bakiji tsoron Allahn kiba wa kuma zaki ji tsoro, Allah wadai da halin ki,
Tofa wata sabuwa kowa yayi saƙare yana jin wani sabon zancen, Dadda kam ai saura kaɗan numfashin ta ya sarƙe, da sauri tayi baya zata faɗi, Abban Ameesha ya riƙota,
Baba bai damu da halin da ta shiga yaci gaba da cewa, sai yanzu hankalin ki ya tashi kenan ko duk a tunanin ki bansan wace ce ke ba, nasan har yanzu kina mamakin ya a kai muka kasan ce araye ko?
To kisan........,
Da sauri Abban Ameesha ya tari numfashin sa, cike da shiga ruÉ—ani yace "Baba wai dan Allah me kake son cewa ne, me Dadda ta aikata maka, me kuma tayi, ya kamata kayi mana bayani ka duba kaga halin da ka jefata saboda maganganun nan naka,
"Duk na munafurci ne ai, dan baku san ko wacece ita, nafi ku sanin ko wacece ita, duk wani abu dake faruwa, itace musabbabin sa, duk ita ta jefamu cikin wannan halin, kowa ya taso cikin mawuyacin halin,
Hmmm dukansu akusan tare suka sauke ajiyar zuciya, dan yana faÉ—in haka duk suka fahimci inda zancen nasa ya dosa,
Ita kanta Dadda loƙaci ɗaya taji kamar ankwashe mata wani abun me nauyi daga cikin zuciyar ta, amma da gaba ɗaya tunanin ta ya tsaya, ta rasa ma wane irin tunani zatayi gurin gano abun da tayi masa yake jifan ta da waɗannan maganganun haka,
"Allah sarki Baba, wallahi har ka tayar mana da hankali, a ina ka ganta, Baba wallahi ba ita bace ai,
Wani kallo Baba ya watsa Abban Ameesha tare da cewa "har kake rantsuwa ingan ta da ido na ƙiriri ranar da tasa aka kama mu, amma kace ba ita bace,
Abban Ameesha harda É—an murmushi yace "Baba ka kwantar da hankalin ka ayi maka bayani, itama yanzu da kake ganin ta anan tsawon kwanaki bama tare da ita, jiya mukaje Gombe acan ma muka kwana, sai É—azu muka dawo,
cike da kallon rashin fahimta Baba yake bin Abban Ameesha da kallo,
Papa ne da kansa ya ɗora da yi masa bayani, da ƙyar suka samu Baba ya haƙura akayi masa cikakken bayani, tundaga A har Z saida aka basa, labarin kowa da halin da kowa ya tsinci kansa, sannan aka ɗora masa da labarin ganin mahaifan Abban Ameesha, yanzu haka acikin gidan su yake zaune,
Baba yayi mamaki mutuƙa abun da yafi komai basa mamakin shine ƴar biyun Dadda da take waɗannan abubuwan,
Nan ya ɗora musu da nasa, labarin bayan mutanen nan sun kamasa sai suka kaisa wani guri kwanan shi biyu kuma suka kawo Nadeeya loƙacin da suka kawo ta bata cikin hayyacin ta, saboda alurar da sukayi mata loƙacin da ta haifi Ameesha, itace ta taɓa mata ƙwaƙwalwa, gaba ɗaya sai ta burki ce, ta fita daga hankalin ta, abun sai ya haɗar mata biyu ga zafin haihuwa ga allurar da sukayi mata gashi kuma da ta tashi sai ta ringa kiran yarinyar da ta haifa taitacewa a fito mata da ƴarta, da mijin ta,
Dade suka ga abun nata ba sauƙi sai suka kira likita yazo yayi mata allurar da zata sa ta bacci, dan ta rage kwakwazon da take yi musu, bayan kuma anyi mata, ɗaya daga cikin su yace su Baba su shirya zai fita dasu sai suyi wani wajen idan ba haka ba kuma suka ci gaba da zama agun zasu iya rasa ransu,
Bayan sunyi haka da kwana ɗaya suka zo su su biyu sai suka fito dasu da niyar zasuje su kashe su, agurin waɗancen amma su awajen su idan sun fita dasu ba kashe su zasuyi ba, shiyasa ma aka amince musu da su fita dasu ɗin, suyi nesa dasu da gari sannan su kashe su,to a wajen fitowar ne, shi kuma Baba yaga ƴar biyun Dadda a cikin mota, basu bar gurin ba kuma, yaga fitowar ta daga motar ya ƙara tabbatar wa kansa itace,
Amma duk da haka da suka shiga motar sai da ya tambayi mutanen yace dan Allah wacece waccen matar Yahaya masa ai itace tasa aka kamasu, kuma yanzu haka ma da suka ɗauko su itace tasa, duk wani abu da zaiga ya faru itace take sawa, tunda ga wannan loƙacin Baba yake ƙullace da Dadda saboda duk a tunanin sa itacen da gaske,
Bayan kuma waÉ—annan mutanen sun fita dasu, sai suka kaisu asibiti suka biya komai da za a dubata koda bata samu lafiya ba gaba É—aya to a É—an bata abun da zaisa ta rage,
Suka yi musu godiya sannan sukayi sallama, suka tafi suka barsu agun,
Satin su ɗaya a asibitin aka sallame su saboda kuɗin su ya ƙare amma sun basa maganin da zai ringa siya mata idan ya ƙare zai iya zuwa wani asibitin ya siya,
Daga nan Baba ya rasa inda zai dosa, haka ya riƙota a hannu suka ringa tafiya shikan sa baisan inda zasu ba,
a wata kasuwa suka tsaya, wanda shi kansa baisan wane gari bane, saidaga baya yake jin sunan garin Kano abun da zasu ci yafara tunani dan haka yana ganin ana dako shima yaje yace a taimaka masa, abashi aikin yi zasu siyi abinci,
Wani mutumine yaji yabasa tausayi, hakannan ya É—auko dubu biyar yabasa, yace yaje basai yayi masa dakon ba,
Tun daga nan, Baba yake zama a cikin kasuwar, tare da Æ´ar sa, kuma har yanzu batadawo daidai ba, kawai dai ta dena sambatun da buge buge,
Wajen Satin su uku a haka suna kwana a ƙasan wata rumfar me tebur sai ya nemi ƙyallaye yake rufe musu ciki idan dare yayi zasu kwanta, daga baya kuma sai aka fara ankare wa dasu, wani mutum ya nemi yayi masa lalata ƴa, sai kawai ya tattara ina sa inasa suka bar kasuwar haka sukai ta garari daga can suyi can daga na su koma can, daga ƙarshedai da Baba yaga abun hakane sai kawai ya ɗauke ta suka koma daji da zama, ya haɗa musu bukka da komai da zasu ringa amfani dashi, sannan ya ringa shiga daji yana nemo wasu magungunan sai yanzu yake ganin amfanin sanin su, ada sana'ar mahaifin sace amma shi baitaɓa maida hankali akan suba, sai yanzu inda ma Allah ya taimake sa duk ya riƙe su, kwaso su yafarayi yana kaiwa cikin gari yana siyar wa, kuɗin kuma da yake samu sai yaringa siyo musu abinci da abun da yasan zasu buƙata daga baya kuma yama haɗa nurhu da kansa yake yi musu abin da zasu ci,
A wajen siyar da maganin ne, ya haɗu da waɗannan yaran su biyu da suka taimake su suka fito dasu, suna haɗuwa suka gaisa cikin mutunta juna, sannan suke basa labari sun shiryu sundena wannan harkar, suma duk kusan marayu ne basu san iyayen su, shiyasa suka faɗa irin harkar, daga baya kuma suka shiryu, nan suka tambaye sa ina ya koma yagaya musu harkar da yake, nan suka roƙashi shine suka haɗa kai gaba ɗayan su suka koma rayuwar da jin idan zai fito sai su fito tare kowa ya nemi nakan sa, a haka har suka tara kuɗi suka buɗe shago da taimakon wani Alhaji da yabasu jari, Alahamdulillah komai yana tafar musu yanda yakamata, a loƙacin ne Bello da Sulaiman suka buƙaci Baba da su koma cikin gari subar dajin tunda suna da kuɗi sai su kama gida...,
Amma baba yace a'a sude suje su kama inyaso kullum idan ya fito da ringa haÉ—uwa, babu yanda suka iya dan sunfi son zaman cikin garin akan dajin, badan suna so ba suka bar Baba Æ´ar sa suka koma cikin garin inda Baba yabasu shawarar su nemi shaguna biyu me daki a ciki sai sun ringa kwana a ciki sun samu kwanciyar hankali, ganin hakan yasa Baba yace su taya shi bincike akan matar agano masa inda take,
Nan suka shiga bincike akan Dadda shi yanayi suma sunayi masa har aka gano inda take da kuma komawar su gidan sarautar duk wani motsin su da labarin gidan babu wanda baya zuwa kunnen Baba, shima kuma yana nemo wani abun da kansa, abun da yasa yaƙi tona mata asiri kawai saboda yana so sai ya fara gano dalilin da yasa ta zaɓi yi musu haka, kuma ya bari sai ranar da asirin ta ya tonu yasan dole asirin ta ya tono ko badaɗe ko bajima, shi kuma agun tonuwar asirin zai bayyana kansa yazo yaƙara da tashi shaiɗar, daga nan ya ɗora musu har zuwa inda ta samu lafiya gaba ɗaya, tun buge tan da Meer yayi da mota tun loƙacin yakaita asibiti daga nan kuma akayi mata aikin matsalar ta gaba ɗaya ta dawo normal,
Yana gama bada labarin, duk sun fahimce sa, kuma basuga laifin sa ba, saboda daman duk wanda yaga haka indai ba bayani akayi maka ba baza ka taɓa yarda ba,
Haƙuri yabawa Dadda abisa zargin ta dayayi akan rashin sani, daga nan suka cigaba da tattaunawa, sai wajen ƙarfe shaɗaya na dare sannan kowa ya fara shirin kwanciya, Dadda da Ameesha da maman ta, akace su tafi ɗaki, shikuma Baba su tafi da Abban Ameesha, da farko Abban Ameesha ƙin yarda yayi wai saidai su tafi tare da Norry ɗin sa, akace masa ai bazai yiyu ba, dole sai an ƙara ɗaura musu aure saidai yayi haƙuri nan da sati ɗaya sai a ware musu part ɗinsu daban bayan an mayar da auren su,
Ba haka suka so ba, dande anfi ƙarfin sune kawai suka yarda daga nan sukayi sallama, kowa ya tafi makwancin sa, asuba ta gari..........,
Washe gari tunda wuri duk suka haÉ—u a cikin falon gurin breakfast daga nan kuma aka haÉ—a taro a cikin fada na gabatar da bayyanar matar Abban Ameesha, da kuma mutumin da ya tsinci Sameer tun yana yaro,