← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 103

Sashe 11

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajjaju kuwa shikaɗai yasan hukuncin da zai mata duk da tana matsayin kaka agurin sa, amma hakan bazai hanasa ya rufe ido ba yaci mutuncin ta idan batayi wasa bama idan yaji labarin abubuwan da tayi mata, wallahi sai yasa anƙulle masa ita sai yayi ƙarar ta ko kuma ya ɗauki ƙwaƙwaran hukunci da kansa, dan bazai taɓa barin taba, idan kuma yarinyar nan ce ƴar kenan (wacce akeso a haɗasu aure) idan itace sai ya ɓaɓɓalata yanda suka azabtar da ita duk sai yarama mata ninkin baninkin ma abun da sukayi mata, Ɗagowar da tayi ne daga jikin sa ya katse masa tunanin sa,

Da kumburarrun idanun ta take kallon sa shima itan yake kallo da idonsa da suka canza kala daga yanda suke zuwa baƙin ciki,

Janye nata idon tayi tana ƙoƙarin tashi daga kansa amma sai ya hanata hakan,  bata takura ba akan dole sai ta tashin sai kawai ta haƙura, zuwa yanzu ta daina kukan, sai ajiyar zuciya da take saukewa akai akai,

"Wait Hamza, sam yafaÉ—a yana kallon Hamza, da sauri Hamza ya taka burki ya tsaya tare da juyowa yace "lafiya?

Sam yace "EH" yana faɗar haka ya zura hannu a aljihun sa ya zaro ATM card ɗin sa tare da miƙawa Hamza,

Karɓa Hamza yayi yana jiran karin bayani, Sam yace "kaje cikin nan......., Sai kuma ya katse maganar tare da ɗan sakin ƙaramin tsaki yace " Mtsw barshima kawai bani naje da kaina ya karɓi abunsa, sannan ta buɗe motar,

Rabata yayi da jikinsa, yana kallon ta itama shi take kallo, idonsa akanta yace "bari inje indawo kizauna, yanzu zan dawo,

Kamar tace masa a'a zata bishi sai kuma ta tuna da shigar da take jikin ta, dan haka sai kawai ta É—aga masa kai tare Da kawar da kanta ta kwantar dashi ajikin kujera,

Tsayawa yayi yana kallon ta tsawon sakanni sannan ya kalli Hamza yace ka kula da ita kafin na dawo,Hamza yace "In sha Allah,

Sumayya jin maganar tasa yasa ta buɗe ido tare da juyawa ta kallesa, sai kawai ya ɗan sakar mata murmushi kaɗan yace "yanzu zan dawo, ji yake kamar kar yatafi, kai ta ƙara ɗaga masa tare da rufe idon ta taƙara komawa yanda take,

Daƙyar dai ya iya rufe motar ya tafi wani babban shagon sayar da kaya ya shiga, yana shiga ba ɓata loƙaci ya shiga kwaso mata kayan saka dogayen riguna riga da sket harda riga da wando da hijabai, da underwears su panties da bra, duk dai wani abu da yasan zata buƙata saida ya ɗauko mata sannan ya koma kan kayan ciye ciye da su choculate da sauran su abubuwa dai yasiya masu yawa sannan yaje wajen biya ya miƙa ATM ɗinsa aka ciri kuɗin aka basa abunsa sannan aka saka masa kayan a leda wasu suka ɗaukar masa sannan suka fita daga gurin har wajen motar aka kaimasa,

Hamza na ganin su tunkan su ƙaraso ma ya buɗe musu booth suka saka masa aciki aka rufe,

BuÉ—e motar yayi ya shiga yanda ya barta haka yazo ya same ta ko motsawa batayi ba,

Tayar da motar Hamza yayi suka cigaba da tafiya,

Sosai ya tsaya yana ƙarewa fuskarta kallo ganin haryanzu bata ce komai ba kuma bata buɗe idon ta ba duk da yasan taji shigowar sa, amma bata kulasaba,

Ƴar ƙaramar ledar da ya ɗauko a hannun sa yashigo da ita cikin motar ita ya buɗe ya zaro hijabi aciki, ahaka bata motsaba shima kuma baice mata komai ba ya ware hijab ɗin yafara ƙoƙarin saka mata sai aloƙacin tayi saurin buɗe idon ta tana kallon hijab ɗin, kallon ta tamayar kansa sannan ta ƙara kallon hijab ɗin sai kawai tasa hannu ta karɓa taƙarasa sakawa,

ÆŠas yayi mata daman kalar da tafi so ya siyo mata maroon colour shikuma baisan shi tafiso ba kawaidai ya É—aukar mata shi saboda irin shi yafara ganin ta ranar da suka fara haÉ—uwa, shiyasa ya É—aukar mata kalar,

Wani Choculate Biscuit ya ɗauko mata tare da ɓare mata shi ya miƙa mata da farko ƙin karɓa tayi saida ya watsa mata wani kallo sannan tayi saurin saka hannu ta karɓa  murya can ƙasa ƙasa ta ɗan kallesa tace thanks....,

Wani ƙayatacen murmushi yaƙara sakar mata, duk da bata gani ba hakannan yake jin daɗin godiyar da tayi masa, gashi abun da yake basa mamaki shine yanda ya zuba mata ido yake kallon ta ko ƙiftawa bayayi,

Aɓangaren ta kuma kallon da yake mata yafara isar ta, sai take jin duk ta takura dashi, gefe tayi da kanta tana kallon waje, ganin inda suke shirin shiga yasa tayi saurin juyowa tana kallon sa, daman shima ita yake kallo dan haka tana juyowa suka haɗa ido sai tayi saurin janye nata tare da cewa "naga munzo nan ba gida ba?

"Eh nan gidan mune, zan kaiki amma ba yauba,

Zata ƙara magana kenan yace "shiru karkice komai, yafaɗa yana ɗauke kansa daga gare ta,

Itama bata ce ɗinba kamar yanda ya buƙata, amma a ƙasan zuciyar ta tunanin ta shine karfa yaƙara kaita inda za a kuma cinzalinta irin gidan da yakaita dan baƙaramar wuya suka bata ba duk azabar da umman su Waleed take mata baikai irin wannan ba, ita iyakacin ta duka amma nasu yayi yawa ga aiki ga duka ga zagin cin mutunci, sai taji muguntar gidan su nafilace akan ta gidan da yakaita shiyasa take tsoron kar yaƙara kaita inda za' azabtar da ita, duk da taji yace gidan sune amma hakan baisa taji zuciyar ta kwanta ba, so take kawai ta ganta agaban mahaifin ta hakan sai yafiye mata fiye da duk inda zaikaita,

Hamza na shiga cikin masarautar Sam yace "yakaisu daidai ƙofar part ɗin fulani ta yanda suna fito zasu shiga ciki batare da kowa yaga shigar suba, haka kwa yayi ya kaisu daidai ƙofar shiga sannan yayi parking yana parking ɗin kuma ya buɗe motar ya fita yabasu waje,

Sam ne ya kalli Sumayya da gaba É—aya hankalin ta baya jikin ta ya lura bama taga shigowar su ba ta tafi tunani,

Hannu yasa ya riƙo hancin ta, hakan yasata saurin dawowa daga duniyar tunanin da ta faɗa,

"Tunanin me kike ya jefa mata tambaya, kai ta girgiza masa tana kallon cikin gidan ashe har sun tsaya bata saniba, gaban motar ta kalla taga, mejan su ma har ya fita daga motar duk bataji ba tana tunani,

Buɗe ƙofar yayi ya fita sannan yace itama tafito, da ƙyar ta jawo jikin ta ta matso kusa da murfin sannan ya matsa mata ta fito,

Suna fitowa ya riko hannun ta ya buɗe kofar da ɗayan hannun sannan suka shiga ciki, ya mayar da ƙofar ya rufe, Hamza dake bayansu ya buɗe yafara fito da kayan da Sam ya siyo mata sannan ya bisu dashi ciki,

Yana shiga ya wuce ɓangaren Sam, abakin ƙofar ta tsaya ya kwanƙwasa jin shiru yasa ya tura kofar ya shiga kaitsaye,

Basa cikin falon sai kawai ya ajiye kayayyakin afalo sannan yajuya yabar falon,

Saida Sam ya shiga da ita É—akin sannan ya sakar mata hannu kan gado ya nuna mata yace ta zauna, shikuma ya wuce bathroom, shiga yayi ya haÉ—a mata ruwan wanka me zafi sannan ya fito yace "taje tayi wanka,

"To tace masa saboda daman a buƙace take da son yin wankan saboda yau kwanan kwanan ta wajen huɗu batayi ba tunda taje gidan batayi wanka ba, sun hanata yi,

Ahaka yanda take ta tashi ta nufi banÉ—akin, da kallo kawai yabita baice mata komai ba, saboda bayaso ya takura mata,

fita yayi daga É—akin, yana fita ya tadda kayan afalon sai kawai ya É—auka ya shigar dasu É—akin, ware su ya shiga yi sannan ya É—auko mata wasu riga da sket da wata hula harda pant da bra, ya ajiye mata su akan gado,

sauran kuma ya haɗe su ahaka ya buɗe wardrobe ɗin sa yasaka su ya rufe, sannan yaƙara fita kitchen ɗinsa ya shiga ya ɗauko plate sannan ya buɗe frigh ya ɗauko holandiya me sanyi sosai tare cup sannan ya koma ɗakin har loƙacin bata fitoba,

Mamakine yakamasa ganin irin daÉ—ewar da tayi, tunani yashiga yi kodai ba lafiya ba,

Banɗakin ya nufa yana zuwa yakara kunnen sa yanaso yaji da motsi ko ba motsi, saidai kuma yana kara kunnen nasa, ita kuma tana buɗe ƙofar, da sauri tayi baya cike da tsoro tare da sakin ɗan ƙaramin ihu, shima saida saida yaɗan tsoratan yanda tayi masane yasa ya tsorata,

Ajiyar zuciya ta sauke tana tace "wlh ka tsoratani,

"Sorry naji shirun yayi yawane shiyasa nabiyo inji ko lafiya, yana gama faÉ—ar haka kuma yayi baya dan yabata damar fitowa,

Fitowa tayi tana faman sunnar dakai duk da hijabi ne ajikin ta amma sai kunya ta kamata,

bakin gado ya zauna yana jiran ƙarasowar ta, tana ƙarasowa ya ɗauki kayan ya nuna mata kayan yace gashi sai kisaka ɗaukar su tayi sannan ta juya zata bar wajen "yace ina zaki?

Tace "shiryawa zanje inyi,

miƙewa tsaye yayi yace "kiyi sauri kishirya, sannan ya fita waje,

Yana fita tacire hijab É—in sannan ta É—auki bra É—in tunkan tasaka take mamakin yanda akai ya É—auko size É—in tana sakawa kuwa tayi mata cas kamar ya gwada ko tagaya masa size É—in da take sakawa, pant É—inma daidan ta, haka kayan ma komai daidai ita, saida tagama sakawa sannan ta É—auki towel É—in data cire ta É—aure gashin ta da tawanke shiyasa ma ta daÉ—e saida ta ware kalbar kanta ta wanke kan,

Tana cikin tsane kannata ya shigo ciki, bakinsa ɗauke da sallama amsa masa tayi tana cigaba da goge ruwan kannata, ƙarasowa yayi gaban ta yana ganin abun da take yasa hannu ya karɓi towel ɗin, ya ajiye sa gefe yace "akwai draya gata can, yafaɗa yana nuna mata inda take, tare sukaje gurin, zatayi da kanta ma yayi saurin karba ya busar mata dashi ya gyara mata kan kamar mace harda yi mata oiling sannan ya ɗaure mata shi da wani zare saboda babu reboon akanta shima kuma basiyo mata ba,
Chapter 11 · 0% Book details