Sashe 16
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shafa kanta yayi, yana sakin ƴar ƙaramar dariya, yace "nikwa nasan shi bayan barin yarinyar nan ai gidan marayu ta koma shima kuma ɗan gidan marayun ne acan yataso, naje ziyara na tadda yarinyar acan shima kuma acan yake shiyasa nasan su, kinsan kwa samun shi bazai min wuya ba inacewa ina buƙatar sa za abani shi dan haka karki wani damu ki kwantar da hankalin ki, kuma maganar auren ki dashi ki haƙura saboda bana son ki auri wanda baida asali ko so kike ƙawayen ki su yi miki dariya kin auri ɗan gidan marayu,
Da sauri ta girgiza kai tace "dagaske Maraya ne Allah sarki wallahi Dady ya ban tausayi sai naji na ƙara sonshi Dady ni na yarda duk ma abun da zasuce suce zan aure shi da haka tundade yana da ƙyau idan kuma kuɗi ne basai kabashi ka ɗau nauyin mu kawai tunda de Kai kana da kuɗi amma nidai bazan iya rayuwa babu shiba,
Mom ɗin tama dake zaune tana sauraron su bata saka musu baki ba saboda tun farkon maganar tasu, da tasaka baki Dady ya yanka mata magana shiyasa bata sake saka musu baki ba, itama ba ƙaramin mamaki tayi ba jin wai marayane agidan marayu yake bayan kuma ƙawarta ta gaya musu ko shi waye, to kodai bashi Dady yake nufi ba,
Ɗan gyaran murya tayi tana kallon su tace, anya kuwa kasan wanda ake magana gaskiya wannan ba ɗan gidan marayu bane ɗan gidan marayunne zai zo yanayiwa mutane rashin mutunci son ransa, Fatima ma fa (momy) tace a Abuja yake yana da babban asibiti nasa nakan sa asalin suma ba ƴan ƙasar nan bane, a ƙasar Yamen ne, kuma na yarda dan kaf faɗin garin nan bana mijin da na taɓa ji yakama ƴan mata yana duka kamar Allah ya kawosa duk kuɗin uban mutum kuwa, amma tunda kaji yana aikata haka ai kasan da abun da ya taƙala shiyasa yake rashin mutun cinsa,
Wata wawuyar harara ya watsa mata mai cike da gargaɗi da yasa loƙaci ɗaya ta fahimce sa ta kuma gane yaren masa, dan haka taja bakin ta tayi shiru bata ƙara tanka masa ba, tasan dawar garin idan taƙara saka baki,
Rasheeda tace "nima dai haka nagani mom wallahi baiyi kama da wanda yasan wata wahala ba ko marar gata, nidai Dady ina tunanin baka san kowa ake magana akai ba,
Kamo hannun ta yayi yace "Baby kina ja da magana tane?
Shiru tayi bata basa amsa ba, hakan yasashi cigaba da cewa "bani minti biyu ina zuwa, tashi yayi daga gurin ya zaro wayar sa yana ƙarasa fita daga ɗakin,
Zama sukayi suna jiran sa shiru shiru baidawo ba, Rasheeda tace mom kina ganin kwa da gaske Dady yagane wanda muke nufi,
Mom ta gyara zama tare da kishin giÉ—a akan gado tace "tunda kikaji haka ai yasanshi É—in amma dai kibari yadawo É—in muji mai zaice,
Bata gama rufe bakin taba sai gashi ya shigo hannun sa É—auke da waya, yana sakin murmushi yaÆ™araso kusa da ita yace "baby zangoge miki tantamar ki yanzu akan yaron nan,Â
"Ba shine wannan ba yafaÉ—a yana nuna mata screen É—in wayar sa,
Da sauri ta karɓi wayar tana kalla ta ɗago ta kalle sa tace "Dady wallahi shine a ina kasamu hoton shi Wallahi shine amma kuma Dady ai nan kamar ba gidan marayu bane kaga fa wani zane kamar irin na gidan sarauta ko mom kingan saba, karɓa itama tayi tace "au shine ni daman bantaɓa ganin saba, gaskiya dai nan gidan sarauta ne gama mutane nan agaban sa, hoton Meer ne zaune akan kujera loƙacin da yake zaune akan kujera loƙacin da ya tara mutanen nan acikin masarauta ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya bisa ga dukkan alamu kuma anyi hotonne batare da sanin saba,
Karkaɗa kai Rasheeda tayi tare da karɓe wayar daga hannun ta, tana kallon Dady, cike da jiran ƙarin bayani,
"Kidaina ko kwanto akan duk abun da zangaya miki, kedai kijira zuwa anjima kuma zaki gansa agaban ki, kinji ko, yana faɗa ya miƙe tsaye yace kijirani,
Cike da murna tana washe baki tace Dady ina sonka kuma na yarda da maganar ka, duk abun da zaka faɗa nayarda kawai ina buƙatar ganin sa, zan shirya ina jiran dawowar ka,
Fita yayi yana ƙara sakin dariyar manya yana sakin murmushi yana cewa "don't worry my baby duk abun da kike so afaɗin duniyar nan sai namiki shi komeye kinfi ƙarfin komai awajena, ƙiƙara dawowa ta yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin bai jira amsar taba,
Tashi ta tsaye tana tsalle tsalle har da zuwa ta rungume mom É—inta tace mom yau zangan sa agabana, bari inyi sauri inkira su momy da Zeee suzo dan afiyin komai agaban su gani da ido yafi abaka labari, daman nasan suna can suna min dariyar kun kasa nemomin shi, shiyasa ma na korasu amma yanzu zan kirasu in antaya musu wannan sweer story É—in, tana maganar tana wani juyi tana dariya, ta fita daga É—akin,
Itadai mom na inda take bata tanka mataba, saboda tana mamakin mijin ta, ta yanda yake kashe ta da mamaki kamar aljani sai kaga abu kamar bazai taɓa yiyuwa ba amma sai kaga yaje shi ya lalubo yanzu a ina yasamo wannan hoton nasa, dan ta fahimci duk ƙarya yayi ƴar tasa nacewa wai ɗan gidan marayu ne yayi hakane kawai dan ya cire mata son yaron to amma meye dalilin sa nayin hakan tunda harta nuna tanaso ai kamata yayi ya shige mata gaba amma shine da kansa yake mata ƙarya yana mata zame zame dan ta haƙura dashi, dole akwai ƙwaƙƙwaran dalilin sa nayin hakan, akwai abun da ya hango ko kuma yasani akan yaron da baya so su sani,
Tashi tayi zaune bayan fitar Rasheedan, a fili ta furta koma maikake shiryawa zan gano kane, na lura akwai abun da kake ɓoye min da baka son nasani tunda daɗewa amma yanzu take taken ka yafara yin yawa dole insaka maka ido aduk wani takun ka zan ganoka ne tayi maganar tana miƙewa tsaye tafara zagaye ɗakin tana saƙe saƙe a cikin zuciyar ta,
Rasheeda na zuwa ɗakin ta, ta ɗauki wayar ta, Zee tafara dannawa kira nan ta antaya mata labarin duk abun da yafaru sannan tace ko mai take ta bari tazo gidan su yanzu yanzun nan, bayan sunyi sallama haka tabi sauran ƙawayen ma gaba ɗayan su ta sanar dasu komai sannan tabasu umarnin zuwa, duk suka amsa mata da zasu zo amma duk sai zuwa dare zasu iso, itadai momy dariyar mugunta kawai take mata, dole tazo tagane wa kanta wannan labarin ƙanzon kuraigen, inda rabon ya haɗasu gaba ɗayan su ya ci ubansu, sudai nasu kallo ne suna daga baya.....,
Bayan tagama wayar ta ajiye ta, haka ta wuni tana farin ciki har zuwa dare jim kaɗan sai ta leƙa window tana jiran dawowar mahaifin ta, amma shiru da taga har takwas tawuce ƙawayen nata basu zoba sai kawai ta hau cire kaya, ta shiga wanka ba daɗewa ta fito nan ta fara zubo da kayan ta dan ta zaɓi wanda suka fi kowanne kyau dan ganawa da abin alfaharin ta dan zuciyar ta tabata duk inda Dady yake yana hanyar ƙarasowa gida tare dashi ,
Tana cikin zaɓar kayan wayar ta tayi ringing da sauri ta tashi ta nufi inda ta ajiye ta dan duk atunanin ta sune suka ƙaraso, saidai tana ɗauka tasaki wani wawan tsaki tare da sakin wayar ta faɗi kan gado,
Tana jin kiran har ya katsa wani yaƙara shigowa ahaka saida akayi mata kira huɗu bata ɗaga ba ana biyar ɗinne ta ɗaga tana jan tsaki tare da kara wayar a kunnen ta, tayi shiru shima daga can ɓangaren shirun akayi, saida ta daɗe ahaka har tana shirin katse kiran, yace "mai yasa baki ɗaga ba ina ta kiran ki tun ɗazu,
Taɓe baki tayi tana ya tsina fuska tace "saboda banda ra'ayin hakan,
Bossay dake kwance akan gadon sa riƙe da waya, jin amsar da tabasa yasashi saurin tashi zaune yana bin wayar da kallon mamaki ƙin aminta yayi da abun da yaji, hakan yasa ya ƙara cewa ko baki ji abun da nace miki bane,
Abun da ta gaya masa da farko haka ta ƙara maimai ta masa,
Yace "ok haka kika ce ko fine, ya faÉ—a yana shirin kashe wayar shi daman baiyi niyar kiran taba Ammi ce ta haÉ—asa da Allah ya kirata yaji yanda zatayi tsare tsaren bikin tunda biki na matsowa, dalilin kiran kenan,
Jin kamar zai kashe yasa tayi saurin cewa "Aliyu dakata kaji abun da zan gaya maka ka buɗi kunnuwan ka kajini da kyau kagane ko, bata jira cewar saba, taci gaba da cewa, yanzu bada bace kagane yanzu nafi ƙarfin ka nafi ƙarfin ajinka banda loƙacin ka nasan bikin mu yakusa to amma kasani nayi counselling ɗin sa babu maganar aure tsakanin dakai nasamu wanda nake so wanda yafika komai yanzu shine agabana bakai ba maganar auren babu ita zaka iya sanar da ƴan gidan ku ni nagama yanke shawara saduwar alkhairi please don't call me again and delete my contact, if not sai kayi regretting ɗin ƙara kirana da zakayi arayuwar ka poor boy kawai ni banma san tsiyar da nagani ajikin ka ba da har nasoka wallahi nayi da nasanin saninka ma bare har inyi soyayya dakai nake shirin haɗa alaƙar jini dakai gwanda da Allah ya ganar dani tun wuri yabani irin wanda nakeso cikar mafarkina......, Nayi da nasanin....., Shiru tayi bata ƙara saba sakamakon nocking ɗin da taji anayi mata, yasata yin shiru tace "who is?
Muryar Dadyn ta tajiyo ta waje, yace "Baby angama aiki ke kaÉ—ai ake jiran fitowar ki gashi a falo ke yake jira,
Da sauri ta saki wayar aƙasa tace Dady dagaske!?
Turo ƙofar yayi ya shigo cikin ɗakin yana binta da kallo, yace "kina mamaki ne zo muje ki ganewa idonki,
Tsalle tayi ta rungume sa cike da murna da farin ciki da ya kusan kashe ta ta shiga manna masa kiss a kumatu tace "Dady nagode Nagode kagama yi min komai yanda ka faranta min kaima Allah ya baka abun da kakeso,