Sashe 18
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk baƙin cikin da Ameesha take ciki da suka shigo saita ɗan saki fuskar ta suka hau yin hira suka manta ma da faɗan da sukayi, suna ɗakin har aka kira magriba suka tashi sukayi suka ƙara cigaba da hirar su sai gab da sallar isha'i da wayo da wayo Azeema ta jawo su suka fito daga part ɗin suka nufi part ɗin maama,
Suna zuwa tundaga bakin ƙofa sukayi karo da Meer da hannu ya nuna musu motar da zasu shiga akusa dasu daman su yake jira tun ɗazu, ba musu Azeema ta kuma jansu suka koma suka shiga motar su Amra na tambayar su ina zasu sai suka kace shopping zasu je nan bakin su hamra yafara washewa da dariya suna shiga, drivern da zai jasu yatayar da motar suka fice batare da sanin kowa ba,
Meer na gurin saida yaga fitar su sannan ya koma cikin falon su maama duk na falon ita da dadda da kuma ummy wucesu yayi yaje ɗakin sa ba daɗewa ya ƙara fitowa cikin sauri sauri, baiyiwa kowa magana ba ya fita cikin motar da zai fita yaje har ya buɗe zai shiga sai kuma yaƙara tuna wani abun sai ya rufe yaƙara komawa can, ɗakin sa yaƙara komawa, ya ɗauko wata ƴar ƙaramar jaka, ya ƙara fitowa har zai fita maama tayi saurin dakatar dashi da cewa wai ɗan gidan gwaggo mai kakeyiwa saurine haka ina zuwa?
Ba tsaya da tafiyar ba yace "ina zuwa.... Yana faɗa yaƙarasa fita daga falon,
Binsa tayi da kallo tana jinjina kai sannan itama ta miƙe tacewa ummy bari ta koma ɗaki, daman su biyu ne a falon tun ɗazu dadda da tashi saboda bata jin daɗin jikin ta har yanzu,
Meer na fita yafaÉ—a motar sa yashiga ya tayar da ita sannan yazaro wayar sa ya kunnata yana neman location É—in da yahaÉ—a da wayar hannun Azeema, yaga inda sukayi, duk da yasan inda za akaisu amma sai yayi tracking É—in su, yana tayar da motar yajata shima yafita yabi bayan su,
Tun kan ta hau kan titi yafara tafiya kawai sai yaji kamar motsi acikin motar, slow yafarayi da motar yana shirin juyowa kawai yaji saukar allura a gefen wuyan sa ɗan ya tsina fuska yayi yana dafa gurin yana ƙarasa juyowa amma sai yaga baya ganin nacikin motar da kyau, hakan yasashi taka burki ya tsaya gaba ɗaya da tafiyar, yana tsaya na bayan motar ya dawo gaba, tare da karɓe muƙullin motar, sai ya zaro wayar sa ya danna kira yace, angama,
Yana sauke wayar saiga wasu mutane biyu nan sun ƙaraso gurin suka buɗe motar suka fito dashi suka mayar dashi cikin motar su suka tayar da ita suka ƙara gaba shikuma ɗayan ya biyo su da motar Meer ɗin,
Duk abun da suke Meer najin su saidai yakasa taɓuka komai ko magana yakasa yi, har suka ƙaraso gidan su Rasheeda dashi.............., Kunji ta yanda akai suka sameshi...,
  ****************************
     Cigaban labari........,
_________Ƙarasa shigowa ciki sukayi dashi har gaban Dady suka kawasa sannan suka sake sa suna sakin sa yafaɗi agaban Dady a durƙushe, yayin da hannuwansa duka biyun suke a ɗaure ta baya, jikin sa kuma babu ƙwari duk asake yake,
Rasheeda na bayan Dady takasa fitowa dan gani take kamar zai tashi yaƙara dukan ta,
Dady ne ya ɗanyi murmushi ya juya yana kallon ta yanda take ta rawar jiki, yace "baby kinga abun da dadyn ku yayi ko ai na gaya miki zan kawo miki shi har gabanki, ko bashi bane yaƙarasa maganar yana ɗage girar sa alamar tambaya,
Da ƙyar ra iya ɗagowa ta kalle sa sannan ta jinjina masa kai dan batama samu damar buɗar bakin taba tace wani abun,
Juyawa yayi gaba ɗayan sa yana kallon ta sanann yakama hannun ta suka zauna akan kuje ra saj yace "maye hakan kuma kince kina buƙatar ganin sa amma kinzo kina ɓuya babu abaun da ya isa yayi miki saboda baya cikin hayya cinsa kuma komai kikayi masa babu abun da zai iya, ki yarda dani kinjj ko yanzu gashi agaban ki kifaɗi duk abun da kike so ayi masa, wuƙa da nama na hannun ki,
Girgiza kai ta shiga yi tana cewa "Dady ni na haƙura dan Allah kawai a fita dashi ni wallahi tsoron sa nake ji bazan iya yi masa komai ba, kasa a mayar dashi inda yake, ina son sa kuma zan aure sa amma bata irin wannan hanyar ba, zan koma inda yake rayuwa zan sameshi ta cikin sauƙi, yanzu da ka gusar masa da hankali ko ma meye ai ni bazan ji daɗi ba nafi so inma ramuwar zanyi in rama yana cikin hankalin sa batare da gushewar hankalin saba yanda zaifi jin ciwon abun kuma yayi da nasanin abun da yayi min,
Dady zaiyi magana kenan saiga shigowar su momy gaba ɗayan su, su su biyar ɗin suka shigo kowanne bakin sa ɗauke da sallama suka shigo, saidai basu ƙaraso cikiba duk suka ja burki suka tsaya suna kallon Meer da mamaki, momy kam da sauri taja baya gudan kada yagan ta,
Ganin su da Rasheeda tayi sai kawai taji wata dauriya da ƙwarin gwiwa sunzo mata atake ta cire tsoron da take yi masa, ta miƙe tsaye tana sakin murmushi tace "sannun ku da zuwa ku ƙaraso mana kunga abun da nake gaya muku ko, gashi agabana, kamar yanda Dady na yayi min alƙawari gashi ya cika min dan hama burina ma yana daf da cika,  zai zama nawa kamar yanda nayi tunani tun farko zai zamo nawa zai dawo kan tafin hannuna sai yanda nayi dashi zan juyasa son raina sai abun da nace yayi shi zaiyi,
Duk surutun dai da take musu babu wanda yayi gigin tofa nasa bakin aciki dan har yanzu kowa da guntun tsoron sa aransu dan abun da yasama suka zo suna tunanin kamar ƙarya take faɗa musu hakan bazata taɓa yiyuwa ba amma sai gashi ga mamakin su wai sunzo sun tarar dashi agidan su, abun ba ƙaramin ɗaure musu kai yayi ba musamman momy da tafi su sanin ko waye shi taya akayi har suka iya kamosa,
Kusa dasu ta ƙaraso tare da kama hannun wansu tafara jansu zuwa gaban Meer dake zaune har yanzu kamar mutum mutumi duk yana jin su amma bazai iya yin komai ba ko tashi tsaye da kansa bazai iya yiba,
Kamar sokaye haka suka zama suna kallon sa,
Dady da yaga kallon nasu yayi yawa sai ya dakatar dasu ta hanyar cewa, duk su samu waje su zauna,
Ba musu suka zazzauna, suna zama saiga mom itama ta sauko tana ƙarewa yaron kallo,
Tundaga sama take ƙarewa Meer kallo har taƙaraso gurin idon ta akansa bata daina kallon saba, loƙaci guda kuma taji ya kwanta mata arai taji tayiwa ƴarta sha'awarsa, atake zuciyar ta tabata dole tasan yanda zatayi ya kasance ma aurin ƴarta ko ta halin ƙaƙa sai ta haɗa jini dashi dan tana ganin sa ta yarda da maganganun fatima (momy) tasan sun tara dukiya idan fa haɗa jini kuwa dashi ai ba ƙaramin morewa zasuyi ba daga ita har ƴarta ta, duk aɗan ƙanƙanan loƙaci take wannan tunanin,
Itama zama tayi tare da maida dubanta ga Dady tace "Amma fa babu abun da zamu ce maka sai godiya gurin tsayawa ka jajirce wajen nemowa ƴarka farin cikin rayuwar ta kayi namijin ƙoƙari ai ni ina ganin kawai ahaɗa su auren nan nasan zaka iya, yanzu kuma ta haƙura da batun ɗaukar fansa akan sa mubi ta bakin nata abar sa ya tafi ɗin amaida shi inda aka ɗauko sa, zamu nemeshi daga baya yanzu ai ga shiga hannu tunda har ansan inda yake, bamu da wata matsala da hakan, ko ya kagani dan ni wallahi sai nafi kowa farin cikin auren nan nasu,
Ɗan gyara zama Dady yayi yana ganin ta da kyau yace "kina ganin hakan mai yiyuwa ne taya zai amince da ita ya aure ta, ni ina ganin wannan maganar haɗin ku haƙura da shi ni banga abun da kuka gani ba kuke son haɗa aure dashi, ni aganina na kawo sa nanne kawai ta faɗi hukuncin da za ayi masa a rama mata dukan da yayi mata mu azabtar dashi tayanda bazai ƙara dukan wasu matan ba, asa ya shiga hankalin sa akoya masa hankali, daga nan amayar dashi inda yake bashikenan ba mu rabu ko ahanya ya ganta ko kallon banza bazai kuma yi mata ba,
Rasheeda murya kamar zatayi kuka tace "Allah kuwa Dady ni inason sa ahaka kuma saina aure sa kama daina wannan zancen ni nace na haƙura da hukun cin yanzu zan rama idan munyi aure ta wata hanyar daban amma wannan maganar abarta,
Shiru Dady yayi yana Æ™ara tunanin ta yanda za afara wannan maganar auren da suke so ayi bawai yanajin tsoron ko bazai iyaba, a'a kawai dai yana tunanin idan akayi auren Æ´arsa zata iya fuskantar wasu abubuwan daga gareshi saboda yaji labarin sa gaba É—aya yasan baida mutunci babu abun da bazai iya aikawa ba idan yana cikin hankalin sa yanzun ma dan yasan babu abun da zai iya yi musune sakamakon allurar da wani likita yabashi yayi masa, shiyasa yakasa komai,Â
Mom ce ta katse masa tunanin sa da cewa "my daughter ai banga laifin kiba dole kisoshi kar ki damu kamar kinsame shine kin gama ki kwantar da hankalinki kamar ma anyi auren angama, amma saidai kiyi haÆ™uri aure bazai yiyu nan da sati É—aya ba, dan sai nayi Æ™waƙƙwaran shiri na musamman akan sa, ki bani nan da sati É—aya komai zai kammala daga nan kuma maganar aure zata fara, kafin nan ma kamar yanda kikace zaki koma jikin sa to dole ta wannan hanyar za abi wajen Æ™ara kusancin ki dashi da kuma iyayen sa zan miki shiru na musamman, kafin kishiga cikin gidan su,Â
Mayar da duban ta tayi kan Dady, tace nasan zaka iya aikin ka anan shine kasamo mana hanayar da zata shiga cikin gidan su cikin sauƙi, wannan karamin aikine awajen ka nikuma zanji da sauran,