Sashe 89
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A cikin masarauta ma komai yana tafiya yanda yakama yanzu babu wata matsala, ana mulki yanda ya kamata, mutane da yawa suna kawo kukan su, kuma ana share musu kukan su, duk wanda zai zo neman buƙatar wani abun ana biya masa, kowa dake garin yasan anyi sabon sarki, saboda yanda aka gudanar da mulkin cikin tsari da adalci, babu me cewa anyi masa wani abun daga cikin masarautar,
Dadda da malam suma Yanzu hankalin su kwance babu wani abu da zasu nema su rasa, saidai godiya kawai,
Su Noory da Norry kam sai soyayya ake sha inda har aka samo mana little Ameesha ko little Sameer, sai wata kulawa ta musamman Abban Ameesha yake bata,
A ɓangaren gidan su Azeema, ɗan su sarki Salahudeen ya gina musu wani gidan yayi musu part part shima ya tattara nasa iyalin duk da Papa ya hanasa amma haka yabawa Papa haƙuri ya kwashi iyalen sa suka bar cikin masarautar, ya koma can, ga iyalen sa ga iyayen sa hakan yafi masa daɗi da kwanciyar hankali.. amma yana shigowa sosai ya gaida su Papa, sa Fulani,
Saleema yana nan ƙalau inda yake ta aikin sa a hospital ɗin su, Sam wanda zuwa yanzu yaƙara samun babban matsayi, yana samun albashin sa me tsoka, gashi yayan sa ya ɗauke masa nauyin gidan su babu abun da yake siya, shiyasa kuɗin sa suke ta ta ruwa har yafara gina tamfatsetsen gidan sa na kansa, wanda ko matar da zai saka bai gama samu ba, amma ya kusan gama gida,
*********************
A ɓangaren su Rasheeda suna cikin wani hali na rayuwa, dan duk wani abu da Dady ya mallaka anƙwace sa, babu abuda suka tsira dashi, gashi sun koma gida amma saboda halin su yasa kowa sai janye abun da yake daga zarar sunzo zasu raɓe ka kowa sai yace ai da suna dashi wulaƙanci take musu, alhalin ba haka bane, batada hali dai me kyau amma kuma bata da rowa ko kaɗan,
Rayuwa kenan, gashi daman mahaifayar ta ta rasu, sai abun da tagani, daga ƙarshe ma da tsangwamar tasu tayi yawa, dan duk wannan ƙibar tata saida ta zazzage,
Rasheeda ta lallaɓa suka tafi ƙauye dan tana ganin can sai yafi musu daɗi akan nan, hatta wayoyin hannun su saida ƴan sanda suka kwace kayan jikin su kawai aka barsu dashi,
Rasheeda duk wannan gayun yanzu kamar ba ita ba, duk ta fara canza kamanni, satin su ɗaya a ƙauyen ta cewa uwar ta bazata iya zama ba, ƙauyen fa ko ruwan arziƙi babu, idan ma ansamu wata kala ne jajawur me ƙasa, ga ba wutar nefa indare yayi sauro ya ta cizon su ga wani irin zafi da akeyi a ƙauyen, da ƙyar mahaifiyar ta ta lallaɓata tayi satin shima wai a hakan akwai wani saurayi agidan yana zuwa cikin gari ya siyo mata ruwa da abin ci da yayi na kwana biyar kuwa yace ya gaji indai tanaso yaci gaba da siya mata saidai ta yarda ayi musu, aure shikuma zai siya mata kome take so,
Tunda ga ranar ko kallon inda yake bata ƙara yi ba, banda tsabar ya raina mata hankali wani gaja da shi baki duk kore ƙazami dashi zai wani haɗa kansa da ita, abincin hannun nasa ma da ƙyar take iya ci, dan akwai loƙacin ma da take ci abin ci kawai ya shigo yana ware mata baki yazo inda take taji warin jikin sa ya dakar mata hanci ta kalli bakin sa, ai saida ta dawo da abin nan gaba ɗaya, babu wanda ya iya zama acikin ta, da ƙyar taƙara kwana biyu a daddafe tana yi kuwa tace wallahi idan ta ci gaba da zama mutuwa zatayi haka ta tattaro ƴan kayayyakin ta ta dawo gidan su mahaifayar ta, gashi dangin mahaifin tama intace zata suma duk ɗaya ƴan ƙauyen ne hasalima bata taɓa ganin suba batama san garin da suke ba, ɗan uwansu ɗaya ta sani mahaifin Khalid kuma shima ya rasu, Khalid kuma ya tattara kayan sa yabar gidan batasan ma sanda ya tafi ba bare ta bisa......
Shikuma yana sane yayi musu haka sai yake sai ta horu sosai, dan duk yasan halin da suke ciki yana tausaya musu, kawai dai yafiso sai sun fara gane kuren su, da kuma abun da mahaifin su yake aikatawa, sai yazama izna akansu,
Gidan ɗaya daga cikin ƙawayen take ta bata labarin duk abun dake faruwa tace ta taimaka mata, ta kira mata sauran su san yanda zasuyi da ita, amma koda ta kirasu kowa sai yanuna mata bashida kuɗi wasuma ƙarya sukayi mata wai basa gida saboda karma taje,
Wacce taje gidan suce ta barta tayi kwana har biyu, daga nan tace taso ta tafi iyayen sunyi mata magana, da zata tafi ta bata kaya kala biyu, ta bata dubu É—aya tace ta hau mota,
Haka Rasheeda ta tafi har da su kuka tana ta tuna rayuwar da tayi dasu wasuma ita take biya musu kuÉ—in makaranta babu abun da suke nema agurin ta su rasa komai yi musu take, idan bikine ya tashi ita zatayi musu anko duk wani abu idan ya tashi ita take É—aukar nauyin su, ko kayan ankon bikin ta saida ta É—inka musu set biyar biyar, amma yanzu saboda rayuwa tayi mata haka suka yi mata haka,
Nan gidan su mahaifayar tata ta dawo kawai ta kama ɗaki ta ci gaba da zaman kaɗai ci gashi bata gama makaranta ba batasan ya zatayi ba, haka take wuni a ɗaki tana kuka daga nan bacci ya ɗauke ta, idan ta tashi ta fito cikin gidan, haka wanda yaga dama ya tsakura mata abin ci wasuma ko kallo bata ishe su, wataran kuma kakan ta yabata haka take rayuwa cikin ƙunci da damuwa........,
*********************
A ɓangaren su Dadyn Bossay, tunda Ayuba ya samu sauƙi suka ƙara komawa garin Abuja inda aka tattauna maganar karagar mulki,
Nan suka sauka akaje harda su Papa akan maganar wanda ya dace a ɗora da farko baban Bossay suka ce ya hau, amma sai yace shi gaskiya bazai iya barin kasuwancin sa ba saida abawa Hamza tunda shima ai ya riga da ya manyanta, sai kuma akayi maganar aure sai yace shi gaskiya yanzu baida matar da zai aura wacce kuma yake jin zai aura ɗin karatu take saidai in za ajira nan da shekara biyu, sai ayi inkwa ba kaba saidai a naɗasa da haka, dan bazai taɓa auren matar da baya so ba,
Rasa yanda za ayi dashi akayi saboda taurin kansa ya riga ya kafe yace shi wallahi baza'a aura masa wata ba, sai ita akace yafaɗi wacce yake so acikin waɗanda suka tafi makarantar yace abari idan sun dawo aji, Hamza taurin kan sa yayi yawa, in ya kafe akan abu babu wanda ya isa yasa shi, ga kuma isa da taƙama da kai, ko dayake jinin sarauta dole saida hakan,
Papa ne yace abari to yanzu kawai wanda yake kai ya hau shima daman nan da shekara biyun shima akwai abun da ya shirya in sa rai da lafiya, sai ayi naɗin masa tare da aura masa, kuma ya lalubo ɗayar kafin loƙacin dan mata biyu zai aura,
Daga nan suka juyo suka dawo gida, shima Hamza yanzu ba sosai yake zaman can masarautar ba, yafi zama anan gidan yayan sa gurin Bossay, zaman sa kuma yasa Bossay yaɗan fara sakin jiki ba kamar da, dan har yanzu sonta bai fita aransa ba, dan kawai ranar ma da yaji ita yake son gani kawai ya shirya ya tafi har can Abujan yaje ya tsaya a wajen makarantar su,tun safe, saida yaga zuwan ta sannan shima ya fito ya shiga cikin makarantar fuskar sa arufe ya ringa binta daga nesa yana kallon har suka tashi saida yaga tafiyar ta sannan ya haƙura ya juyo gida, batare da tasan da zuwan nasa ba har ya tafi.....
Meer kam ko shekara baiyi ba a ƙasar su yadawo suka ƙara shiri tare da su Ummy da Abu harda Maama Papa ne kaɗai bai tafi ba saboda kula da fadar,
Tun kafin suje Ummy ta kira ta sanar da gidan su inda akai ta É—okin zuwan ta bayan shekaru da suka É—auka basu ganta ba,
Koda taje sun samu tarba me kyau harda gurin mahainta, daman yace sai ya kawo dangin sa sannan zai kulata, yanzu kama ta cika, ta kawo masa, kowa sai nan da nan yake dasu, tare da zuwa gurin dangi dangi ana gaisawa,
Saida aukayi sati biyu sannan suka juyo cike da kewar juna, tare da farin ciki, fal ranta ta na ganin Æ´anuwan ta,
Suna dawowa kuma Meer yaƙara komawa amma watan sa uku ya juyo maimakon ya dawo gida sai kawai ya wuce Abuja, aje yaci gaba da gudanar da aikin sa, bare da sanin kowa ba, duk sunyi tunanin yana can,
Kuma duk idonsa nakan su Ameesha, su kansu basu sani ba, kuma duk abun da sukayi ana gaya masa, inda Allah ya taimake su ba ataɓa zuwa ance masa angansu da saurayi ba, shiyasa yasa yvara bi dasu, amma ƙiris yake jira yaji sunyi wani yace su tattara kayan su, su koma gida,dan sun gama karatun, amma sai tsallake wa suke wanda shi agurin sa bahaka yaso......, (Hmm saboda mugunta nacinka ko kuwa saboda me?)
************************
*AFTER 4 YEARS LATER*
____Sannu Sannu bata hana zuwa saidai a daɗe da aje b.......🤗🤗
Gudu Gudu sauri sauri...💃💃💃💃
Please sorry gobe zan ɗora akan wannan page ɗin, dan har yanzu page ɗin ba ƙare ba,........
[27/11, 12:15 am] #yaya Azeema#: Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â
     ragowar page ɗin jiya.....
     ************************
     *AFTER 4 YEARS LATER*
____Sannu Sannu bata hana zuwa saidai a daɗe da aje ba.......🤗🤗
Gudu Gudu sauri sauri...💃💃💃💃
 ***Sakanni na gudu su bada mintin, mintin na gudu subada awanni, awanni na gudu su bada kwanani inda kwanaki ke gudu suna bada satittika, satittika su bada watanni, watanni sukam bamu shekaru, a haka har munkai shekara huɗu,
A shekara huɗun nan abubuwa da dama sun faru, baƙin ciki da farin ciki, haka rayuwar take daman, yau daɗi gobe ba daɗi,