Sashe 82
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ameesha damƙe idon ta tayi tana ƙara sakin kuka dan har yanzu gani take kamar daddar tata ake yiwa haka, duk ta ƙudundune kanta ajikin Maama, jikin ta sai karkarwa yake, Maama ce ta miƙe da ita, da ido tayiwa Ummy alamu tazo su fita, atare suka fita,
Dan wasu ma bazasu iya kallon abun da Meer yakeyiwa wannan matar ba, dan duk wanda yaga bazai iya ba É—aya bayan É—ayna suka ringa ficewa daga ciki har Papa ma fita, abudai kamar wasa sai duk aka fara watsewa É—aya bayan É—aya, musamman matan mazan kwa basu wani tausaya mata, zaman su suka yi suka ci gaba da kallon Meer abun da yake, koda wani irin kuka da take fitar wa na ban tausayi, indai ba dakakkiuar zuciya ce da kaiba, baza iya zama ka saurari kukan da take ba,
Sosai yagama fitar da ita daga cikin hayyacin ta, taji jiki koda azabar kan yabar ta, ai ba shiri ta faÉ—i inda take ashe tana can gidan da aka É—auko Meer a Gombe,
Sai loƙacin Meer ya rabu da ita, sauran kama inbanda shiga tashin hankali babu abun da suke, ɗayar matar kam harda suma dan tsabar tsoron da take ji tunkan a zo kanta,
kan Dady suka koma shima shida, Sam da Bosaya da suka, taya shi, Bossay daman da biyu yake dukan sa, saboda haushin sa yake ji akan auren da aka so ayi masa Allah ya tsare sa,
Basu rabu da shi ba saida suka karya masa ƙafa ɗaya, ne makon Meer ya kira Khalid sai, Abuu yabasa number wani soja, yace azo a tafi da su, aje ai ta basu horo me tsanani wanda baza su mutu ba, daga ƙarshe kuma za a miƙa su koto, bayan anyi shari'a da su, za'a garƙame su a kurkuku,
Adaren saida aka gama komai domin ha har wasu dake cikin gidan su Ammah har su Meer ya haÉ—a aka tafi dasu wajen sojoji, dan yace baza ayi shari'a da su ba sai kowa ya gane Allah É—aya ne sai an ladaftar da su,,
Kafin kuma atafi dasu saida akasa suka faɗi duk wata dukiya dake hannun su da kuma filaye ashe harda wani Company da yake shirin buɗewa duk suka haɗa suka handime, gidaje kam sunfi biyar ga filaye wajen shida ahaka ma duk sun siyar da wasu, bankin sa kam kuɗaɗen da suka ci baza su irgu ba, duk an kwace komai daga hannun su hatta gidan da kowannen su yake zaune nasa ne, duk wani ma abu da suka mallaka duk nasane basu da ko tsinke, wanda ya rage mallakin su, illa jikin su, shi kaɗai ne yazama mallakin su, shima kuma yanzu yana hannun sojoji sai yanda sukayi dashi dan kullum sai ya karɓi gashin duka,
Da farko Abban Ameesha dagewa yayi akan sai sunje can wajen Dadda wai kar suje kafin safiya aka shata ko kuma wuya ta kashe ta, kamar yanda tace, da ƙyar aka lallasheshi ya haƙura zuwa gobe, yace kuma tunda asuba zasu tafi aka ce masa anyarda, sannan aka samu lafiya, amma da a tubure musu,
Ko abinci aranra babu wanda yaci na dare ana tashi daga nan kowa makwancin sa yayi,
Ameesha kuma daman tana gurin Maama suna ɗaki tun tanayin kukan har ta lallaɓa ta tayi bacci, tunkan su gama abun ma,
shigowar Papa yasa ta fara tunanin ta yanda zata fitar da ita, sai kuma tayi tunanin ko ta kira Azeema tazo ta fita da ita, amma tuna yanayin da take ciki sai taji bai kamata a tashe ta ba kuma dole tana buƙatar me kulawa da ita koda ta farka cikin dare, sai ta rabuda ita kawai da niyar idan Meer ya shigo sai ta kirasa ya ɗauke ta,
Meer kam bai shigo ba sai wajen ƙarfe 11:pm yana shigowa kuma ya wuce ɗakin sa, bai zauna ba saida yayi wanka yayi sallah sannan ya zauna abakin gado ya ɗauko kayan zaƙin sa da yasaba sha,
Hankalin sa kwance yake shan su da yau jinsa yake sakayau kamar an kwashe masa wani abun daga kansa, da dede yake jin sa duk a cunkushe gaba ɗaya baya samun sukuni, amma yau shikaɗai yasan yanayin da yake ciki na farin ciki, yau finally yayi handling ɗin duk wani bincike daga yanzu babu shi babu tunani koda yaushe, ada kullum tunanin yanda zaiyi wannan yanda zai kama wancen waye da hannu aciki waye babu, komai dai yanzu yazo ƙarshe babu wani criminal da yarage masa,
Yanzu abu biyu suka rage masa kuma shima zuwa gobe zai gama daga ɗauko dadda sai yaje ya lalubo wancen tsohon da baisan dalilin sa na ɓuya ba ranar da yagan sa, kawai ya rabu dashi ne saboda muryar macen da yaji amma yasan yana gurin dan ya riga yaga jakar sa ta fata dake saƙale ajikin mashin ɗin sa, haushin matar ce yasa yakasa yi musu komai ya fito tafi, sannan yasa wanda zasu kula masa da gurin kuma anbashi daddaɗan labari cewar angansa, daman ya ayau yayi niyar zuwa amma sai wannan abun yafaru shiyasa baije ba, amma gobe zaije da zarar sundawo daga Gombe zai wuce can, da ya matsu yayi yayi komai ya gama, dan yana kammala su zai bar ƙasar dan bazai iya cigaba da zama ba ta isheshi badan faruwar waɗannan abubuwan bama da suka hanasa tafiya da tuni yatafi,
yana zaune yana ta shan abunsa yana ta tunane tunane abubuwan da suka faru wasu su bashi mamaki wasu kuma subashi haushi wasu kuma su bashi nishaɗi kamar ɓangaren wajen da suka sakawa su Waziri karara da zuma, suka sauya musu halitta yana jin nishaɗi in ya tuna hakan,
yajiyo bugun ƙofar sa yayi, amma bai amsa ba kuma bai tashi ba Saida yagama cinye abun hannun sa, sannan ya miƙe a hankali ya shiga takawa kamar baya so, zuwa yayi ya buɗe tare da ɗan leƙa kai sai sukayi ido huɗu da Maama, ƙarasa buɗe ƙofar yayi gaba ɗaya yana kallon ta, cike da wasa dan yanzu jinsa yake sakayau bayajin haushi baya damuwa da komai,
"Murmushi ta sakar masa, zatayi magana shikuma yayi saurin cewa meye kuma zaki biyo ni, ko kinzo ki takura min ɗin da kika saba, to koma inda kika fito, yafaɗa yana wani harar ta kamar mace harda taɓe baki da girgiza kai,
Tsaye tayi tana kallon sa da mamaki kamar bashi ne ɗazu yagama dukan baiwar Allah ba, amma yanzu kalle sa kamar babu wani abu da ya faru dashi yau duk wahalar da yasha, ita ji tayi yama bata tausayi akan yanda yake ɗawainiya da jajircewa akan duk abun da ya taɓa su, shi kaɗai yayi musu maganin duk wata matsalar su da damuwar su, amma taga shi ko ajikin sa hakan baya taɓa damun sa ko nuna gajiyawar sa, daga yayi yanan sai yayi can shine kullum akan hanya......,
"Hy, yafaÉ—a yana saka hannu sa asaitin fuskar ta, É—agowa tayi cike da tausayin sa tana kallon sa,
"Ya akai ne me yake faruwa gaya min to, naga zakiyi kuka danna ce ki tafi, to maida hawayen, shigo ciki badan halin kiba,
Hawaye ne ya tarar mata a ido tayi saurin maida su tare da sakin murmushi ta kamo sa ta rungume tana me ƙara jin ƙaunar sa har cikin ranta, cikin sanyin murya tace Allah yayi maka albarka yanda kake ƙoƙari akan dangin ka kaima Allah yabaka masu yi maka, Allah ya albarkar ci rayuwar ka, Allah yabaka zuri'a ɗayyiba, Allah yasa ƴaƴan ka suyi koyi dakai amma banda zafin zuciyar nan taka, wallahi murɗewar nan taaka tayi yawa, mutum kullum sai baƙin....., Shiru tayi tana sakin sa tare da ƙara faɗaɗa murmushin ta ganin kallon da yake mata, hancin sa taja, tace to da wasa nake mutum sai farin hali, haka zance"
Shima sakin tasa fuskar yayi shima yana jan nata hancin yace "Allah ya taimake ki da kin ƙarasa da ni kaɗai nasan me zan miki adaren nan,
Yanzu kam dariya tasaka, sannan tace ai sanin hali shiyasa na fasa faÉ—a, kar yanzu inga kaina babu gashi ancire min su da hannu....,
"Hmmm ai ba iya gashin za a cire ba har kan zan haÉ—a incire su gaba É—aya, kinga nifa kigaya min me yake tafe dake na gaji da tsayuwa in kuma ciki zaki shigo ki tsayani kwanciya, naga kamar missing É—ina kike yau, yana faÉ—ar haka ya juya zai koma,
"Tace Allah ya kiyaye in rasa wanda zanyi missing sai kai, ba kwanciyar da zan tayaka kazo muje ka É—auko matar ka sai ta tayaka daman itace ta kawoni,
Jin abun da tace saida yasashi faÉ—uwar gaba tare da tsayawa cak, amma kuma ya kasa juyowa,
"ko bakaji me nace maka bane" ta ƙara nanata masa,
sai yanzu ya juyo yana facing É—in ta, sannan yace "to ke baza ki iya É—auko taba, ki É—auko ta kikai ta É—akin su ku shi mijin naki yakaita, ni yanzu ciwo ne a hanuna, bazan iya É—aukar ko cokali ba bare mutum,
Harara ta watsa masa sannan tace wallahi ban yarda ba, meye dalilin ka da baka son ɗauko ta ɗin saikace ba matar kaba, bansan ka da ƙarya ba, kasan yanayin da ta tsinci kanta dole tana buƙatar wanda zai kula da ita, kuma bata da wanda ya fika, maza zo muje, kasan de Papa ba wani ƙarfine dashi ba bare kuma ni, dan haka oya huce muje ka ɗauko ta,
Kamar kar yaje haka yaje ji amma rashin abun da zai faɗa ya kare kansa a gunta ta yarda hakan yasanya shi saurin basarwa kar tagane sone bayayi, sai kawai yace "da wasa nake miki, kin taɓa ganin miji yaƙi matar sa, kodan daɗin da zakaji ma ai dole kaso mace.....,
"Me kake cewa ne ni ba jinka nake ba, Maama ta tambaye sa,
Shafa ƙeyar sa ya ɗanyi hana kallon ta sai kawai ya ɗage mata gira ɗaya, yace "ya wuce ki, baki da rabon ji, daman komai saida rabon ka in ba rabon ka bane ko ka ɗaga murya mutum in baida rabon ji bazai ji me kace ba,
zatayi magana yace "shittt muje in ɗauko ta, kar inje tsohon can ya dora Mata ƙasusuwa akai ya cuce ni,