← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 103

Sashe 42

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

Shiyasa da ya kirani nazo dan in tona asirin kowa yaji hakan ma tsari ne, daga nan kuma sai abu ya taɓaɓɓare rishe ya juye da mujiya, dan a loƙacin so nayi ingudu sai kuma hakan bai yiyuba........,

Tana gama rufe bakin ta, Kande tace "wai wa kike nufi kice min, kina nufin É—ana yana gidan nan dan Allah akira min shi, inganshi dam Allah kukirashi,

Meer ne ya tambaye ta sunan É—an tagaya masa tayi shi kuma ya nufi hanyar fita, sannan yasa wani yace yaje ya kirawo masa Hamza,

Ba aɗau wani loƙaci ba, sai gashi an shigo da Hamza cikin gurin,

yana shigowa ya É—auke kai daga gurin Hajiya Sarah saboda baya son ganin ta har yanzu haushin ta yake ji,

Gaban Papa ya ƙarasa tare da tsugunnawa agaban sa ya gaida shi saboda duk a tunanin sa ko akan batun Sam ne shiyasa aka kirasa,

Bayan sun gama gaisawa, Papa ya kirasa sunana sa, sannan ya fara sanar da shi abun dake faruwa tare da basa ɗan taƙaitaccen labarin tundaga farko har zuwa ƙarshe amma da aka gama bashi labarin aka nuna masa mahaifar sa, sai ya nuna ko in kula da jin nasa labarin idan ka kalle sa bazaka gane farin ciki yake ba ko baƙin ciki,

Hakan da yayi kuma ba ƙaramin mamaki yabawa wasu ba, har Saida Maama tayi masa magana akan baiji me akace bane yace yaji, kawai baida ra'ayin komai shi kawai arabu dashi yanda ya taso shi kaɗai zai ci gaba da zaman sa, a haka baya buƙatar wasu dangin na cikin masarautar sune dangin sa kuma zai ci gaba da zama dasu, mahaifayar sa kuma itama tasha bai taso da ita ba kuma bazai zauna da ita ba dan haka bai ɗauke ta matsayin uwa ba, tunda har ta nuna son zuciyar ta ta rabu dashi yataso cikin garari bata neme saba, dan haka shima baya nemanta yanzu acikin rayuwar sa, saboda acewar sa inda har da gaske ne badan son zuciya bane ai da tasan yanda tayi tagayawa wani halin da take ciki ai dole za'a kama ita Ammah ɗin amma tayi shiru da bakin ta suka ci gaba da zalintar mutane, idan kayi wani tunani ma gaba ɗaya kusan itace silar komai da batayiwa tifkar hanci ba tun loƙacin da ta gane gaskiya da ta dakatar da ita ta sanar da mutane abun dake faruwa da duk haka bata faru ba,

Dan haka shi ba wani farin ciki da yayi da hakan, ana gama maganar ma ya tashi yabar cikin fadar, uwar tana ta kuka tana kiran sa amma ko waiwaiwayon tama baiyi ba, ya fice abun sa, su papa ma babu wanda ya dakatar dasu sun rabu dashi zuwa wani loƙacin zasu kirasa suyi magana,

Kamar ranta zai fita haka Kande take kuka, tayi da nasani yafi cikin kwando ji take kamar tayi hauka ita bataga wani cigaba da ta samu a rayuwar ta ba ta rasa mijinta ta rasa ƴaƴan ta gashi ta tashi a tutar babu, babu wani cigaba da tasamu gashi ta jawa kanta zaman gidan yari na har abada, wannan masifa da mai tayi kama ga ɗanta yana gudun ta ko nuna yaji da daɗi ma da ganin ta baiyi ba, ya tafi yabarta tana roƙon sa amma yaƙi sauraron ta, haka ta ringa tunani kala kala, ita kaɗai,

Daga nan kuma aka rufe taro da addu'a kowa yakama gabansa su kuma aka kwashe su aka kaisu can gidan ƙasa kowa aka raba masa ɗaki babu wanda aka haɗa da wani,

_*Washe gari*_

Fulani ma ta koma sashenta babu wani hukunci da aka ƙara yi mata saboda duk abun da ya faru bayin kanta bane, shiyasa aka rabu da ita, inda Saida ta jira akayi masa gyare gyare aka dawo dashi tsaf kamar yanda yake ada sannan ta koma dan cigaba da sabuwar rayuwa,

momma ta koma nata part ɗin inda ta tara su twins ɗinta ta basu labarin komai sannan ta rungumi ƴaƴan tare da miƙa lamarunta ga Allah, Allah ya kawo mata sassauci akan abun dake samun ta, Sam kam shima ta ajiye batunsa a gefe tunda anyi neman duniya an rasa shi, wayar sa ma kuma bata shiga, amma bayan ko wace awa sai ta ƙara gwada Number ko zata shiga amma bata sa'a,

Sannan tun a ranar aka sa aka fito da komai na part É—in Ammah, zuwa gobe za azuba wasu kayan aciki,

Papa da Maama suna sun koma nasu part ɗin inda suka yiwa Allah godiya da ya nuna musu ƙarshen maƙiyan su, yanzu basu da wata damuwa kuma sai neman baban Ameesha amma yanzu sun gama da cikin gidan saura kuma waje zasu fara bincika, hankalin su yanzu ya ɗan kwanta, saboda duk wani ma'aikacin gidan marar gaskiya saida aka kamasa aka ƙulle,

Sannan Papa yace "aje a lalubo wanda ya buge Maama shima sai ankama sa duk dade bada son ransa bane, amma shima yana da laifi na ƙoƙarin kisan kai da yayi,

Nan aka shiga neman sa amma aka rasa, da Maama batayi niyar faɗa ba saidaga baya tace tasan inda yake amma tana neman alfarmar a rabu dashi ta yafe masa saboda ba da son ransa yayi ba, kawai dai akirasa a haɗa da da ƙanin sa, su sasanta kansu, su san junan su, inyaso daga baya su tattara suma su koma can gidan su, su karɓi sarautar su,

Hakan kuwa akayi akaje aka kirawo baban Bossay sannan aka sanar dashi duk abun dake faruwa duk da yasan wasu abubuwan wasu kuma bai sani ba, da kuma abun da ake so suyi, aka haÉ—asa da Hamza aka gabatar dashi agaban sa, yanzu ba laifi Hamza yaji daÉ—in ganin yayan nasa yanzu bai nuna rashin amincewarsa da hakan ba,

Atake agun har suka ɗan saba Dadyn su Bossay ya nemi da su tafi tare su zauna acan gidan sa kafin komai yayi stalling, suje can garin nasu, A loƙacin dai ba ba samu damar hakan ba, Papa yace masa ba yanzu ba, shima kuma Hamzan bai amince ba yadai ce zaizo amma yanzu ba,

Haka Dady ya haƙura ya koma gida tare da tara gaba ɗaya iyalensa ya sanar dasu komai babu abun da ya ɓoye musu, nan suma suka shiga jin daɗin jin asalin mahaifin su,

Bossay kam saboda jin daɗi a loƙacin ya taho masarautar yazo wajen Hamza inda suka ringa tsokanar juna Hamza yace Bossay ɗan sane dan haka dole yace masa baba ko kuma yace masa uncle shi kuma bossay yace bazai faɗa ba Hamza zaici inyaga dama ya amsa inbaiga dama ba kuma kar ya amsa, hala sukai tayi, daga ƙarshe suka shiga hirar Sam yanda za'ayi anemo sa dan sun tausayawa mahaifiyar sa,

Bossay bai bar gidan ba saida yaje wajen Ameesha suka sha hira sannan yatafi gida,

Khalid ma tun ajiya bayan gama komai ya wuce gida,

Ya daÉ—e da dawowa amma baije gidaba sai yau, tundaga wajen gidan yake binsa da kallo sai yaga kamar ancanza komai na gidan haka yaci gaba da driving É—insa tare da yiwa mai gadi horn aka zuge masa gate ya shiga ciki,

A parking lot yayi parking sannan ya buɗe motar ya fito, tundaga sama har ƙasa yake ƙara bin gidan da kallo,

A tsanake ya shiga takawa zuwa falon gidan saboda yana so yayi musu surprise shiyasa bai sanar dasu dawowar saba,

Murɗa ƙofar yayi ya tura kai ciki ya shiga falon ba tare da yayi sallama ba,

zaune yaganta ta juya baya akan dinning tana cin abinci, ƙarasawa yayi inda take ta bayan ta yatsaya tare da zura hannuwansa ya rufe mata ido ta baya yana haka kuma ta gane shine saboda shi kadai tasan yana mata irin haka,

Cikin muryar mamaki tace Yaya!

Tafaɗa tana ɗora hannun ta akan nasa, tana milewa tsaye, sakin ta yayi ta ta ƙarasa juyowa,

Cike da farin ciki ta rungume shi tana cewa irina wannan zuwan bazatan haka, Ni ai nazata bazaka ƙara dawowa ba ai ka koma can,

Sakin shi tayi sai taƙara rungume sa duk ta rasa inda zata tsoma ranta saboda jin daɗin ganin sa,

Shima yana dariya yana jan hancinta yace "ya fitina da rashin ji andaina ko har yanzu tana nan,

itama dariyar tayi tace tofa kadawo kenan ko hutawa bakayi ba zaka fara halin naka,

Zaiyi magana taÆ´i saurin dakatar dashi tare da kamo hannun sa tace yanzu dai duk ba wannan ba muke kayi wanka kazo kaci abinci,

Kallon ta yayi yace ammaa dai abari infara gaisawa da masu gidan "ina Dady yake ko baya gari,

"ÆŠan murmushi tayi tace yana gari amma dai ya fita tun É—azu muje ka gaida mom tana É—aki sai kazo kayi wanka ka huta nasan ka kwaso gajiya,

"To ƙanwata wai yaushe kika ƙara hankali haka kodan auren yazo kusa shiyasa kika ƙara nutsuwa fari tayi da ido tace haba yaya au baka da masaniya aure tun yaushe aka fasayi da wancen yanzu nagano wanda yafi dacewa dani kai yaya baka gansa ba kykkyawane sosai ga kuɗi,

",Uhm wai Rasheeda yaushe kika koma haka ko kunya na bakyaji kike gaya min wannan zance, to ni abar ni haka bari inje ma in fara sauke kayan nan da ko kitayani dasu amma sai zuba kika iya,

Rasheeda tace "to meye abun jin kunaya yaya kaine fa babban yaya
na idan ban gaya maka wa kake so infaÉ—awa, tsaka nina dakai ai ba wata kunya wallah............,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣
Chapter 42 · 0% Book details