← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 103

Sashe 47

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannun sa ta kamo tace taso in taimaka ma ta faɗa tana jan hannun nasa, yunƙurawar da zaiyi kenan ya jawota gaba ɗayan ta, ta faɗo kan ƙijrjin sa,

Da sauri yace "aashh yana damƙe idon sa da karkaɗa kansa saboda faɗowar da tayi ya dakar masa ciki,

Da sauri itama tace wayyo Allah na dan Allah yi haƙuri tana maganar tana ƙoƙarin tashi daga kansa, sai kawai taji hannu wansa duka biyu akan bayan ta ya ɗora su akai,

Ƙara yunƙurawa tayi akaro na biyu amma sai tajidai still ya riƙeta bata ankara ba kawai yayi wani juyi da ita ta dawo ƙasa shi kuma ya dawo saman ta, zaro dara daran idanun ta tayi waje take taji wata iriyar faɗuwar gaba taji gaban ta ya fara fat fat, ɗan ƙaramin bakin ta ta fara motsawa tana so tayi magana motsi kawai yake ta kasa furta komai sai karkarwa yake,

Bakin nata ya zubawa ido yana kallan yanda yake motsi, wani irin abu yaji ya fara yi masa yawo akai, hannu sa ya zaro daga bayan ta dan ji yayi kawai yana sha'awar shafa lips É—in da yaga yana ta motsi kamar bulunboti,

A hankali ya fara tafiya dashi zai sauke sa akai saidai yana daf da saukewa kenan kawai su kaji ance SAMEER...!!!

Jin muryar Abu yasa shi saurin dawowa hayya cinsa a razane ya tashi daga kanta, yana mai mamakin ganin sa a kanta muƙewa tsaye yayi sai kuma yarasa abun cewa gaba ɗaya tunanin sa ya tsaya cak,

Ameesha kama yana É—aga ta itama ta tashi cikin rikicewa,

Shima Abuu cikin ɓacin rai ya fara takowa yana nuna sa da yatsa yana so yayi masa magana amma taƙaici da ɓakin cikin abun da yagani ya hana sa magana, sai kawai baikai ga ƙarasawa wajen saba sai kawai ya juya, dan bashi da bakin magana,

Fita yayi kawai tare da banko ƙofar da ƙarfi,

"Get out of my room..!!! yagaya mata cikin daka mata tsawa, yana nuna mata ƙofa,

Ai tun kan yakai ƙarshen maganar ma ta kwasa aguje ta fice daga ɗakin tana kuka,

"Oh My God ya Allah what wrong with me, Oh my God sai mai mai tawa yake ya rasa inda zai tsoma ransa ji yake Kamar ya tsaga ƙasa ya shige ciki, taƙai da haushin kansa da kansa duk yafi ya cika sa, kawai tunanin sama wai duk ina hankalin sa ya tafi har yake shirin wani abu Allah ma ya taimake sa baikai ga ƙarasa abun da ransa ya raya masa ba, ga kuma Abuu ya gansa yanzu wane irin tunani yakeyi yaga ya fita cikin fushin,

Zama yayi a bakin gado, yasa hannuwansa duka biyu akansa yana dafewa shidai tunda yake bai taɓa shiga irin wannan yanayin ba nayau, yau abun ya haɗar masa goma da ashirin ga halin da ya tsinci kansa da baitaɓa tsinta ba na wani irin azababban ciwon ciki da ya rufe sa loƙaci kamar zai kaishi lahira, ga kuma abun ya faru tsakanin sa yarinyar gashi Abuu yagan su, ji yayi wata tsanar yarinyar da ya kamasa dan a ganinsa duk ita taƙara dagula komai dan da bata shigo ɗakin ba abun baikai haka ba,

Miƙewa yaƙara yi cike da taƙaici sai faman sakin tsaki yake, ya nufi toilet yana shiga batare da ya cire kayan sa ba kawai ya sakarwa kansa ruwa tare da rufe idon sa, yana rufewa kawai sai abun da yafaru ɗazu ya shiga dawowa masa da sauri ya buɗe idanun sa yana ƙara sakin tsaki akaro na babu a dadi, haka yayi tsaye agun ruwa na zubo masa akai, saida yayi wajen 30 minutes a haka sannan ya kashe shower ɗin ya fito a haka da kayan jikin sa jiƙaƙun yana fitowa kuma idanun sa suka ƙara sauka a inda ta faɗo kanta ya juyata ƙasa ɗan ƙaramin bakin ta da yaso taɓawa ɗazu shi ya kuma gaɗo masa, da sauri ya rufe idon sa yana kawar da kansa gefe tare da sakin tsaki mai ƙarfi,

Sauri sauri ya shiga cire kayan jikin sa ya É—auko wasu riga da wando yasanya sannan ya nufo hanyar falo so yake yabar gidan amma baya so ya haÉ—u da kowa musamman Abuu, Ameesha kam ya tama cin mutuncin da zai yi mata, fasa fita yayi sai kawai ya koma É—akin ya É—auki wayar sa number Khalid ya lalubo ya danna masa kira,

"Hello" daga can ɓangaren Khalid yayi magana,

Meer yace "ya kana ina?

"Ina gida"

"Ok mu haÉ—u a wannan gidan yanzu,

"Ok, Amma yanaji muryar ka haka bakajin daÉ—i ne?

Meer "a'a am fine, kawai dai na ɗanyi ciwon cike na ɗazu amma yanzu ya daina, da tunima na kiraka ɗazu sai kuma Ab...., yayi saurin kawar da maganar yace "Oh kagane naji sauƙi tun ɗazu, mu haɗu kawai anjima kasame ni acan zanyi gaba,

"Hmm Khalid yace sannan ya ɗora da cewa "kaga malam nasan halinka babu abun da zaka ɓoye min amma dai idan mun kagaya min sai anjima,

"Mtsw uwarka zan gaya min bana son sa ido bana ce ya daina ba nagaya maka amma zaka wani kawo min maganar banza,

ƙitttt... Khalid ya kashe wayar dan bayason jan zancen shiyasa ya kashe idan sun haɗu sa yita su ƙare face to face,

___Ameesha na fitowa daman babu kowa a falon dan haka ta wuce É—akin su da gudu ta kuwa ci sa'a Dadda bata É—akin sai ta rufe ta faÉ—a kan gado sai kawai ta fashe da kuka da ita kanta bata san dalilin yin saba.....,

Abuu ma da ya fito baibi takan kowa ba kawai ya fice ransa a ɓace ya nufi part ɗinsu da saƙe saƙe kala kala aran sa shi kaɗai yasan abun da yake shiryawa,

***Bayan gama wayar su Meer ya ƙara tashi yaɗan gyara jikin sa, sannan ya lallaɓa ya leƙo waje saida yaga babu kowa sannan yayi sauri ya fito daga ciki, ya fita daga falon, yana fita waje ya canza tafiya ya dake kamar bashi ne me tsoron fitowa ba, har wani taku na musamman yake saboda gwaiwar da yake samu ta mutane da dama duk wanda ya gansa sai ya tsugguna har ƙasa ya gaida shi wasu kuma suna masa kirari, a haka har ya ƙarasa gurin motatar, yana zuwa bai jira wata wata ba ya shiga ya tayar da motar tare da janta yana tashe ta ya kwasa aguje yabar gidan......,

*************************

______Wani ƙungurumin daji ne tafkeke da baka jin motsin komai sai ƙarar tsuntsaye dake shawagi aciki amma babu wani alamun bil'adama agun shiru kaji ɗif,

Can na hango wani tsoho ya fito daga cikin wata Æ´ar bukka.

Cike da tashin hankali gaba ɗaya ya rikice a kiɗime yayi bayan bukkar yana leƙe leƙe ya ƙara danna kai cikin dajin, da ƙarfi ya ɗaga murya ya fara kiran DEEYA ! DEEYA !! DEEYA!!! Sauna da yake ta amba ta kenan yana tafiya ko gaban sama baya kalla kawai kiran ta,

yana cikin tafiya can nesa ya hango ta cikin wani ƙaton ruwa saura kaɗan ta nutse ta tsaya a tsaye ruwan yana shirin shanye ta gaba ɗayan ta dan har yazo wuyan ta saura kaɗan,

Da gudu ya kwasa yana cewa "a'a DEEYA ki dakata ki dakata amma ina kan ya ƙarasa ruwan har shanye ta,

Ƙarfin gudun sa yaƙara yana zuwa yayi sufa cikin ruwan daidai inda take yayo sama da ita yafara tafiya da ita acikin ruwa, har ya kawo ta bakin ruwa ya kwantar da ita nan yafara danna mata ciki yana kiran sunan ta yana jijjigata amma ko gezau batayi ba,

ÆŠaga hannun ta yayi ya saki sai yaji hannun ya faÉ—i asake alamun dai kamar rai yayi halin sa, "a'a a'a Deeya kar ki min haka ki tashi Deeya deeya DEEYA.......!!!!!!!!!!!!!
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

  
                        *_🅿️28_*

   
     'Ɗaga hannun ta yayi ya saki sai yaji hannun ya faɗi asake alamun dai kamar rai yayi halin sa, "a'a a'a Deeya kar ki min haka ki tashi Deeya deeya DEEYA..!!!!!!!!!

"Tashi yayi tsaye duk yanayin girman jikin ta dan a ƙala zata iya kaiwa shekara 38 ko 39  amma da haka ya cicciɓeta ya nufi inda yabaro,

Abakin ƴar bukkar ya kwantar da ita akan wata tabar ma, yana kwantar da ita ya shiga cikin bukkar ba daɗewa ya fito da wata jaka sai ɗan ƙaramin ƙoƙo da ruwa aciki,

gaban ta ya zauna nan ya ɗauko wani ƙullin magani ya zuba acikin ƙoƙon ya jujjuya sa sannan ya fara goga mata shi ajiki yana murzawa daga yagama da wannan sai ya ɗauko wannan ya saka mata, haka yai tayi mata tsawon loƙaci yana gabanta, amma har yanzu bata kawo numfashin ba, har ya fara cire rai da farfaɗowar ta yabayar ta mutu kawai, sai can yaga hannun ta yayi motsi wani irin farin ciki ne ya kamasa nan yaƙara ɗauko wani magani kamar ganye, ya saka mata shi a wuya nan da nan numfashin ta yafara dawowa amma bata buɗe ido ba, sauke numfashi ta shiga yi a hankali,

Farin ciki ne ya lilleɓesa ya ɗaga hannu sama yafara yiwa Allah godiya sannan ya mayar  da duban sa gare ta, a hankali yace "Deeya Deeya!

Motsi tafarayi da idanun ta sannan ta shiga buÉ—e su a hankali har ta gama ware su gaba É—aya akan tsohon dake gaban ta,
Chapter 47 · 0% Book details