← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 103

Sashe 24

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waziri yace "Allah yaya mutanen nan yanzu bazan ƙyalesu ba dan sunga anyi musu shiri shine suke samun damar yiwa mutane wulaƙanci to wallahi anzo gaɓar da bazan yarda ba kamar ni mainayi musu maiye ruwana acikin abunsu, amma tunda har sukace haka zasuyi to muzuba mungani,

"Wai su waye suwa kake magana akai kuma mai akayi maka kamin bayani ya anda zan gane mana duk kabarni cikin duhu me yake faruwa acikin gidan nan,

Kallon sa Waziri yayi ido cikin Ido yace "yaya su rasa wanda zasu ɗauke sai Hindatu matar nan babu ruwanta saliha da ita tunda na aureta babu da wanda suka taɓa samun saɓani har yau saboda bata shiga sabgar kowa amma shine jiya daddare aka samu wani yaje ya sace ta agidan nan kuma anfita da ita kaf cikin gidan nan babu inda ba aduba amma ba aganta ba, wannan abun fa yayi yawa yakamata ayi gaggawar dakatar da komai akawo ƙarshen abun nan yanzu abun da zasu shigo dashi kenan sace sacen mutane,

Papa "yace wai da gaske kake an rasa Hindatu agidan nan amma to garin ya akai haka kai kana ina har kayi sake hakan ta faru,

Wazriri yace "ina wajen surayya mana, saida safen naje sashenta akece min wai ai bata kwana agidan ba kuma wayoyin ta duk na kira a kashe bataje gidaba gabaÉ—aya duk inda akasan zata iya zuwa anje ba asame taba,

Tun É—azu ake bincike cikin gidan nan bata ciki,

Su Maama ma sallallami suka shiga yi suna jajan ta masa da mamakin irin satar da sukeyi ba akansu,

Papa ne yace "Subhanallah kai mutanen na me suke so ne da baza subar mu cikin kwanciyar hankali ba sudai burin su kullum suga kanmu a tarwatse to Allah ya toni asirin su a duk inda suke, yanzu muje aƙara bada cigiyar ta sannan a ƙarfafa bincike,

Maama tace "ni fa abunma kamar da ranin hankali ina mamakin ta yanda ake fita da mutum daga cikin gidan nan amma ace wai ba aga loƙacin da aka fita dashi ina masu tsaron gidanan kuma waye yake buɗe musu ƙofar fita wannan abunfa dole da sa hannun wasu daga cikin gidan nan, kuma da sannu zasu bayyana kansu da kansu, in sha Allah Allah ya kusan tonuwar asirin su,

Waziri jin addu'ar ta aransa saida ya dara saboda tuna maganganun bokan su, shinan wani irin kallon loƙacin tafiyar ku ya kusa dashi yake binsu,

Daganan Papa yasa suka fita har Maama Dadda ma saida ta bisu suna gama fita, su Azeema suka kwashe da dariya suna tafawa da cewa Allah yaƙara Allah yasama ta mutu, kowa ya huta sudai ɓatan ta ba ƙaramin daɗi yayi musuba,

Ameesha tace besty ai ba abarmu abaya ba muje muma muganewa kanmu kar show ya wuce mu, kinga yanda yake magana kamar zaiyi kuka ashe ba daɗi shi matar sa kawai ce amma ji yanda ya tashi hankalin sa ina kuma a ƙwace masa kowa nasa har ƴaƴan inajin da sai ya haukace,

Azeema tace ɗan isakan ba tsohon banza tsohon hofi ma yaudari waya sani ma ko yanzun ma haɗin nasu ne wata manaƙisar suka shirya, wannan mutumin wallahi ba mutumin arziƙi bane, ni har tsoroma yake bani wallahi,

Ameesha tace wallahi hakane ai babu abun da bazai iyaba tunda ya ci amanar É—an uwansa ma wanda suke uwa É—aya uba É—aya suka fito ciki É—aga to waye ma bazai iya cutar wa ba,

Azeema tace "hmmm Allah dai ya kyauta ai asirin sa ya kusa tonuwar tunda de anada hujjar kamasa dumu dumu ai zance ya ƙare,

Ameesha tace wallahi hakane....., Nan dai sukaci gaba da tattaunawar su sannan suka fita waje,

Meer dake bakin ƙofa daman jiran fitar su yake, yana ganin kwa sun fita ya fito da sauri, yayi hanyar kitchen ɗin falon buɗe ƙofar barander yayi, sannan ya dawo cikin ɗakin sa, a bargo ya nannaɗe ta bayan ya yaƙara shaƙa mata abun suma, sannan ya ɗauko ta ta hanyar ya fito da ita yana fitowa inda yasa aka ajiye masa mota gurin babu kowa dan haka, yana zuwa aka buɗe masa gaba yasaka ta sannan ya shiga motar shima ɗayan da ya akawo masa motar wannan abokin nasane, shine yasa masu gadi suka barsa ya shigo da motar bayan yagaya musu tawaye sun san shine dan haka yana zuwa ya shigo kansa tsaye, ya tsaya a inda Meer yayi masa kwatance,

Yana sakata aciki Meer yace yaje zai zasu ƙarasa maganar a waya,

Jan motar yayi ya fita dake daman baidaɗe da zuwa ba kuma tun kan zuwan sa aka sanar da ɓatan nata dan haka babu wanda zaiyi zargin zai fita da wani abun,

Wunin ranar haka akai ta cigiyar matar Waziri,

Zuwa wajen ƙarfe sha biyu na dare Meer yagama setilling ɗin komai ya gyara video ɗin nan da yafara ɗaukar su dashi wanda sukayi masa abunnan har ya shaƙeta ta faɗi kamar ta mutu ashe duk shirin sune shine shi kuma zaiyi musu nasu shirin,

Yana gama sai tashi kawai yasake shi a social media sannan ya lalubo wasu nombobi da yasa aka nemo masa na Æ´an cikin gidan har dashi Wazirin kansa saida ya lalubo number sa, da kuma wasu masu hannun akan lamarin duk ya haÉ—a nombobin su suma ya tura musu wasu ta WhatsApp wasu kuma ta message.......,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️Yaya Azeema❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                        
_____Waziri yana zaune a cikin mutanen sa na ƙungiya acikin wani ƙaton falo inda daman yawanci haɗuwar da suke agurin suke to yauma ɓatan matar waziri yasa suka haɗa zaman tun wajen ƙarfe sha ɗaya,

Kowa yana mamakin ta yanda akayi ta ɓata dan basu yarda Meer ne ba saboda dashine dole zasu sani tunda sun saka ido akansa sosai da hakan ta faru da tuni sun samu labari to amma abun da yake ƙara basu mamaki waye zai ɗauke tan abun ba ƙaramin ɗaure musu mai yake ba, sunyi wajen minti talatin agun suna tattaunawa amma sun kasa samun mafita,

Suna cikin wannan halin Waziri yaji kira awayar da sa sauri ya zaro wayar tare da suba kan wayar yaga mai kiran da sauri ya É—aga ganin sabuwar number ke kiran sa ne a tunanin sa ko wanine yake kiran sa ya gaya masa ansamu inda take,

Yana ɗagawa daga can ɓangeren yaji ance ga matarka a hannun mu mune muka sa ceta, amma dai kafara duba wayar ka akwai saƙo anturo maka ta WhatsApp idan kuma ka gani kayi gaggawar kare kanka daga nan zuwa safiyar gobe yanzu wasan yafara nabarka lafiya yana shirin kashe wayar Waziri yayi saurin dakatar dashi.......,

Da sauri Waziri yace "kaiɗin waye idan ka isa ka bayyana kanka ina kakai min mata Wallahi idan wani abun ya sameta sai na ka.......,bai ƙarasaba yaji ƙit ankashe wayar,

Sauke wayar yayi yana matseta da hannun sa,

Gaba É—aya sauran kansa sukayo da kallo tare da tambayar waye ya kirashi,

Ƙasa amsa musu yayi daida suka ƙara tambayar sannan ya gaya musu abun da mai kiran yace,

Sannan ya ɗora cewa "waye shi waye daga ina yake wannan ba muryar yaron da muke zargi bane wata Muryar ce daban zagaye falon ya shiga yana girgiza kansa dan yafi zargin Meer aciki amma yanzu yagane bashi bane ransa yayi mugun ɓaci hakan yasashi fita daga gurin taron nasu ko buɗe wayar ma baiyi ba, duk da kallo suka bisa, suna jinjinawa ala'amarin suma basu daɗeba taro ya watse tunda wanda ya haɗa ya tafi, suma dole su tafi kowa yakama gaban sa,

Zuwa daidai loƙacin da Meer yasaki videon nan kowa yana part ɗin sa wasuma sun fara bacci waɗanda basuyi bacci ba ƙalilanne videon ya riske su har inda suke,

Waziri da yabar gidan ma gaba É—aya ya tafi can wajen da zai haÉ—u da bokan sa, yagaya masa inda matar sa take,

Tun a daren waÉ—anda sukagani suka fara magana magana tun anayin ta kaÉ—an maÉ—an har tafara fitowa da yawa waÉ—an dama basu gani ba saida akasasu suka gani,

Tun adaren dangin matar sa suma da videon yaje musu ta yanar gizo, wasu suka kwaso ƙafa suka nufo gidan sarki, zuwan sune yaƙara tayar da wasu kan kace mai magana tayi ƙarfi sosai Waziri ya kashe matar sa da kansa gashi kuma anduba ko ina ba asame saba,

Papa ma ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba jin abun da yake shirya wa akansu wanda ya ɗauki yarda ya basa ashe da muguntar da yake shirya masa, wannan wacce iriin rayuwa ce da yazɓi yaudara ɗan unwasa wanda suka fito ciki ɗaya mai yasa Waziri zaiyi msa haka mai ya nema ya rasa gata kuma martaba duk yabasa amma dashi za a haɗa baki a cutar dashi,

gashi kuma yaƙarawa kansa laifi, daganin hakan daman yasan ta'asar da yayi amma shine yazo yakewa mutane kunfar baki, maiye ribar sa nayin hakan, shi kisan da yayi ma yafi komai ɗaga masa hankali, hankalin sa bai gama tashiba saida yaga zuwan ƴan uwan ta gidan,

Gida ya naimi ya hargitse ga dare yayi, sosai kowa yana mamakin abun da waziri yake aikatawa yana zaluntar É—an uwansa ga kuma kisan dayayi ya kashe matar sa da hannun sa ya kuma fitar da ita daga gidan yazo yace ansace ta,

Ƙarfe ɗayan dare har ta wuce amma idan ka shigo gidan nan sai ka rantse ba dare bane saboda yawon mutane da kuma surutai da ake ta faman yi akan wannan videon,
Chapter 24 · 0% Book details