← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 103

Sashe 6

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan tace "Wallahi kuma ina tunanin duk waɗannan mutane da suke bibiyata tun ba yauba duk tsawon loƙacin nan acikin gidan nan suke tunda daga ƙarshe sun dawo suna tambayata ingaya musu inda mahaifiyar Sameer take, nace musu bansan taba bantaɓa ganin taba, shiyasa  suka haƙura suka daina tambayata, kuma ina da tabbacin ɗana Sameer yana hannun su saboda ba yanda zasuyi da takaddun nan Saida sa hannun sa ajiki wataƙil shiyasa suka ƙwace daga gurina zasu je wajensa yasa ka musu hannu,

Tunda tafara magana suke binta da kallo babu wanda yace mata komai har saida ta kai ƙarshen maganar,

Abu ne yafara magana da cewa "wannan ai ba abun ɗaga hankali bane dande kuɗi suje suyita ɗauka kuɗi bashine matsalar muba, indai zasu sako mana shi mu sai muƙara musu ma fiye da wanda suka karɓa da kin faɗama kafin kintafi ai da ba abarki kin tafi ba, da sai kibar su suyi tazama agun, ai daman kema kinyi ganganci tafiya ke kaɗai ai ganganci ne Allah ma ya rufa asiri basu kashe ki ba sun barki da ranki, amma ko ba yauba ki kiyayi fita ke kaɗai a irin wannan loƙacin da muke ciki idansu sunyi yawa akanmu kowa yanzu hankalin sa yana kanmu babu abun da bazasu iya yiwa kowa ba idan suka samu dama, ware war mu kuma shi zai basu damar cinma duk wani ƙudurin su akan ɗayan mu, dan haka sai mun kiyaye fita ɗaiɗai batare da tsaro ba,

Maama tace "Nimadai abun da nagani kenan ke da muke zaune ai baikamata kifita ke kaɗai ba da kinyi shawara da wani da duk hakan bata faru ba, amma dai yanzu tunda komai yazo da sauƙi shikenan Allah ya kiyaye gaba,

Gaba dayan su suka amsa da "Ameen" tare da tofa albarkacin bakin kowanne su, basu san Meer yana gunba saiji sukayi kawai yace, "Aban number da aka kira, ya faɗa yana samun guri ya zauna, yana kallon su, ba musu ummy ta zaro wayar tace "bari in faɗo maka ka rubuta nima daman saving ɗin ta nayi dan dole agano number saidai ayi bincike akanta nasan za a iya samun diddiginta, (oh ɗa da uwa sai Allah har ta manta da abun da yayi mata😂)

Faɗo masa tayi ya rubuta saboda yasanma baza ta shigaba shiyasa baima, kiraba aloƙacin kawai yayi saving ɗin ta yanayi kuma ya tashi daga gurin baice musu komai ba ya koma ɗakin sa,

Da kallo kawai suka bishi sannan sukadai ƙara bawa dadda baki da rarrashi har tasaki ranta saida suka ga ta fara dawowa normal sannan ummy ta taimaka mata ta koma ɗaki dan tayi wanka ta canza kayan jikin ta ta samu hutu,

Sukuma daga nan suka shiga tattaunawa akan lamarin sannan papa ya fita daga sashen ummy da Abu suma suka nufi can part ɗin su daman ɓatan dadda ne ya kawo su yanzu kuma tunda komai ya daidaita suka koma, inda suke,

Falon ya rage daga  Maama sai su Azeema, kaɗan kaɗan suna ɗan hira jefi jefi saboda su hankalin su ba anan yake ba yana gurin Meer so suke kawai suje sugaya masa tunkan gari ya waye yasan komai,

Kamar Maama tasan abun da suke buƙata, sai kawai ta miƙe tsaye tace bari taje ta ɗan kwanta, bacci bacci taji yana fisgarta, shiyasa tayi musu sallama ta tafi ɗakin ta,

Tana tashi suka miƙe tsaye suma cike da murna Azeema ta kalli Ameesha tace "besty to ga dama sai kiyi sauri ki shiga,

Kallon ta Ameesha tayi tace wane irin inje kidai zo muje tare dan Allah, dan wallahi nikaɗai banajin zan iya shiga, Please besty muje, 

Wata uwar harara Azeema ta watsa mata tace "dalla Malama banason shashanci meye hakan kike yi kina so har wani yaji kanmu kenan to ki zauna ki ɓatawa mutane loƙaci ke daman ba a abun arziƙi dake sai kinyi wa mutane cikas,

Ɗan marairaice fuska Ameesha tayi tare da langwaɓar dakai tace nidai naji koma me zaki ce kice amma dai kizo mu shiga tare ni na yarda ma zanyi maganar amma dai mushiga tare dan Allah,

"Allah ranki zai ɓaci wuce muje, tafaɗa tana turata wajen ƙofar har suka ƙarasa bakin ƙofar tasa, sai kuma suka ja burki suka tsaya,

Azeema tace wai meye hakan bazaki shiga ba, matsawa Ameesha tayi daga jikin ƙofar tace Allah kuwa ni bansan me zance masa ba kawai mubar shi ba kin tura masa ba ai zai gani a wayar sa kawai mubarshi wallahi idan yagani ko ba abasa labari ba zai gane komai ai,

Azeema bata tanka mata ba dan taga idan ta biye mata sai su kwana agun, dan haka saikawai tayi nocking ɗin ƙofar shiru ba amsa, hakan yasa ta muraɗa handle ɗin kai tsaye kuma tajisa a abuɗe ɗan tura ƙofar tayi yanda bata hango ɗakin sannan ta tura Ameesha ta ƙarfin tsiya tana shiga taja ƙofar ta rufeta aciki,

juyawa Ameesha tayi tana niyar buɗe ƙofar amma taji ƙam Azeema ta riƙe ta ta waje,  juyawa tayi ta shiga bin ɗakin da kallo sai taga babu kowama aciki amma taji motsi abanɗaki dan haka sai ta sauke ajiyar zuciya ganin ba yanan sannan ta ƙara juyawa bakin ƙofar tana ja murya ƙasa ƙasa tace "besty baya nan fa yana banɗaki ki buɗe min na miki alƙawari wallahi zan dawo anjima da kaina Allah da gaske nake saboda tana tsoron ko wanka yake kar taje kuma ya fito ba tare da kaya ajikin saba shiyasa ta tsorata take gudun kar ya fito tana cikin ɗakin,

Azeema najinta tayi banza da ita tana mata dariya ƙasa ƙasa tayi ma kamar bata gun,

Sosai Ameesha ta shiga roƙon Azeema akan ta buɗe mata amma taƙi haushi ne da ta ƙaici ya isheta da yasa ta saki handle cike da gajiyawa ta bayanta dan taji ko yana daf da fitowa,

Saidai kuma abun da bata sani ba ya daɗe da fitowa har ya ƙaraso inda take ta bayan ta basan yazo ba, juyowar da zatayi kenan taci karo da mutum agaban ta, wata iriyar mummunar faɗuwar gaba taji, take zufa suka shiga karyo mata ta kowacce mafakar gashin jikin ta, ji tayi kamar ta nutse agun karo da tayi da faffaɗan ƙirjin sa mai kwance da ita wasu siraran gashi ɗaiɗai ku da zama ka iya irgasu saboda rashin yawansu agun dan basu hana bayyanar hasken fatar shi ba,

Saura kaɗan numfashin ta ya ɗauke tayi saurin runtse idon ta jikin ta yafara rawa dan baƙaramin tsorata tayi dashi ba tasan shikenan tafaru ta ƙare yau ranar cin ubanta ta kama yau zai sauke mata duk tara tana da yake,

Baki na karkarwa tace P...lea...se I'm so sorry nashigo maka batare da izinin kaba wa...lla....hi ba......n....., shiru tayi bata ƙarasa ba sakamakon tsinkayo muryar sa da tayi yana cewa "shhhhhhhhit........✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By uu
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                         *_P4,_*
          
Bakin ta na karkarwa tace P...lea...se I'm so sorry nashigo maka batare da izinin kaba wa...lla....hi ba......n....., shiru tayi bata ƙarasa ba sakamakon tsinkayo muryar sa da tayi yana cewa "shhhhhhhhit.......,

Ɗif tayi bata ƙasa maganar, kuma bata buɗe idon taba ta ƙulle sa ba,

cikin daka tsawa yace mata "me kika shigo yimin É—aki sa'an kine ni da zakishigo min É—aki kai tsaye ba "eh!

kai ta shiga girgiza masa hawaye na zubowa daga idon ta,

Yace "I'm asking u kina girgiza min kai, baki da baki ne?

Bata daddara ba yanzu ma ta ƙara girgiza masa kai,

Tsaye yayi yana kallon ta yana mamakin yanda akai ta raina sa har yana mata magana amma still ta ƙara girgiza masa kan, ji yayi kamar ya ɗauke ta da mari sai kuma wata zuciyar ta hanesa da hakan har yafara tunanin ko muhimmun abune ya kawo ta ganin yanda ta tsora, ga kuma maganar da yaji tanayi, tunanin hakan yasa ya ɗan sassauta murya tare da ɗan matsawa daga kusa da ita,

Ɗan sassauta muryar sa yayi cikin sanyi kamar yanda take yace "open ur  eyes.

jin baiyi mata komai ba yasa ta ɗan ji daɗi ganin yamatsa daga kusa da ita,  a hankali ta shiga buɗe dara daran idanun ta har ta gama ware su gaba ɗaya tana buɗewa kuma idanun ta suka sauka akan sa ganin sa daga shi sai towel ɗaure a west ɗin sa yasa tayi sauri ta juya masa baya tana kallon ƙofar ƙara gwada buɗeta tayi sai taji ta buɗu cike da murna ta jawo zata bar ɗakin tana ɗaga ƙafar ta, yace "idan kika ɗaga ƙafar ki daga nan sai ranki yayi mummunar ɓaci, come here,

Wani ƙatoton wani abune yazo mata wuya ya tsaya na baƙin ciki, cak ta tsaya tare da juyowa ahankali ta kallesa sai taga bama ita yake kallo ba hankalin sa ma kamar baya kanta yana kan shirin da yake yi, mamaki tayi ya akaima yasan tana niyar fita alhalin kuma ba ita yake kallo ba,

Tana cikin kallon sa ta kuma ji yace, "idan kingama kallon nawa sai kizo kiran da nake miki,

Saurin kawar da kanta tayi tana wasa da hannun ta tana tunanin bayan gata gashi kuma wane irin zuwa zatayi duk maganar da zai mata ai zataji, dan haka aranta tace ita ba inda zata daga inda take,

Har yagama shafe shafen sa yasaka kaya ya bata motsa daga inda take ba,
Chapter 6 · 0% Book details