Sashe 33
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri mamy ta jawota ta rungume ta itama tana kuka kamar ransu zai fita, ganin hakan yasa duk suka bawa kowa tausayi, ummy ce tace ta riƙe su tana basu haƙuri sannan tace momma tayi haƙuri yanzu za'a kira mata shi,
Ƙin shiru momma tayi ta cigaba da sun batunta saboda gaba ɗaya tagama susucewa bata cikin hayyacin ta daman ga damuwar Sam datake ciki kuma wannan yazo yaƙara faruwa shiyasa ta fice hayyacin loƙaci guda,
Da ƙyar da wayo da dabara akasa tayi shiru amma kallo ɗata zakayi mata kasan ba normal take ba.....,
"Papa da idanun sa suka kaÉ—a sukayi jawur tsabar tashin hankalin da yake ciki dan tashin hankali zai kira abun, yana zaune da mutane ashe duk da makiyan sa yake zaune kowa ashe da manufar sa akansa suna cin dunduniyar sa,
Kamar marar laka ajiki haka yake tafiya yazo har gaban ta ya tsugunna cikin wata iriyar murya da bazaka iya fassara tsantsar adadin damuwar da take tattare da ita ba, yace "me yasa SA'ADATU mai yasa me nayi miki arayuwa zaki cutar min da ahalina, daman duk zaman danke dake da zuciya ɗaya ke ba haka bane awajen ashe kina da mugun ƙudiri akaina, mai yasa zakuyi min haka mai na tsare muku, ɗan dakatawa yayi da maganar jin muryar sa na neman ɗauke wa,
Miƙewa tsaye yayi idanun sa na cikowa da ƙwalla cikin sanyin murya yace "mata ta wacce na muƙawa dukkannin yardata, ƙanina na wanda muke uwa ɗaya uba ɗaya, daku za ahaɗa baki a cutar dani wane irin son zuciya ne wannan,
Maama guri ta samuma ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido saboda daman tayi zargin wasu abubuwan da dama shiyasa koda hakan ta faru batayi wani mamaki ba abun da take zargine ya zama gaskiya dan haka yanzu saidai ta tazama Æ´ar kallo,
Itadai Ammah kanta na ƙasa bata ɗago ba bare tasan halin da wasu suke ciki saboda tsabar mutuwar zuciya ko ɗigon ƙwalla babu a idon ta,
Abdullah shima da kunya ta kamasa bai iya É—agowa ba saidai shi yaji zuciyar sa ta karaya,
Hajjaju kuma ko akwalar rigar ta batayi nadama ba babban baƙin cikin ta shine rugujewar auren ƴarta da za ayi dan tasan babu shi tunda asiri ya tonu,
sauran mutum biyun kuma bata su ake ba daman babu wanda yayi musu magana saboda rashin matsayin su acikin gidan, ɗaya namiji ne wanda yake matsayin mai gadin gidan a zahiri a baɗini kuma su yakewa aiki, sai ɗayar macen kuma jakadiyar Maama ce (Gimbiya sabreena) wacce itama duk dangin su Ammah ne matar ƙanin tace da ya mutu sai kawai suka ɗauko ta suka ɗora ta tafara yiwa Maama aiki da da ita suke ta amfani gurin cikar buri kansu, shi kuma mai gadi saboda shige da fice shiyasa duk abun dake faruwa idan antambaye sa sai yace shi baiga fitar kowa ba alhalin kuma yasan komai, shi kuma amintaccen bawa ne agidan dan mahaifin sama anan ya mutu anan aka haifeshi son zuciya tasa shi suka rinjaye sa ya shiga cikin su akan idan komai ya kammala zasu ƴantashi kuma zasu bashi dama yafita yaje yayi rayuwar sa awani gurin tare da bashi maƙudan kuɗaɗe......,
"Meer ne ya tako zuwa tsakiyar falon ganin kowa baya cikin hayya cin sa saboda taɓa zociyoyin wasu da abun da yafaru kowa kagani ba nutsuwa a tare dashi,
Ɗan gyaran murya yayi tare da bin kowa da kallo, sannan yace "silent please, yanzu ba loƙacin kace nace bane yakamata kowa ya nutsu, zamu bar maganar zuwa gobe daman shiyasa na taraku anan saboda kowa yagani da idon sa, ba sai anyi masa dogon bayani ba, gani da ido yafi abaka labari,
"yanzu dare yayi ba loƙacin da zan baku zuwa gobe za'a sake zama, kowa zai iya tafiya yanzu sai zuwa gobe,
Da farko wasu sukace su zasu kwana anan saboda koda sun tafin ma ba iya baccin zasuyi ba gwanda kawai yai komai yanzu, saidai Meer yace musu hakan bazai yiyu ba kawai suyi yanda yace, basu san me yake shirya wa ba dole suka haƙura zama ya tashi, wasu suka kai kansu wasu kuwa saida aka kaisu dan bazasu iya tafiya su kaɗai ba,
Su Ammah na zaune a inda suke babu wanda ya iya motsawa saida suka ga kowa ya fita sannan suka É—ago zasu fara magana basu san Meer na gaban su ba hakan yasa sukayi shiru suka fasa faÉ—ar abun da zasu faÉ—a,
Fadar ta rage daga shi sai a bokin nan nasa wanda yayi shigar boka, suka É—aine aciki,
Meer nakan zaune akan kujerun daje ciki ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ɗagowa yayi ya kalli abokin nasa, da shi kuma hankalin sa yana kan waya,
Sunan sa yakira, yace "KHALID"
ÆŠagowa yayi yana kallon sa tare da cewa "da girman kujerar ka,
Hararar sa yayi, baice masa komai ba yayi masa alama da ido kawai,
Hakan yasan ya Khalid miƙewa ya fita daga cikin fadar yana fita kuma ya ƙullo ƙofar ta waje, bai daɗe da fita ba sai gashi ya dawo,
Sai gashi yadawo tare da tiso ƙeyar Waziri da matar sa, turo su yayi ma suka ƙarasa ciki tare da faɗuwa aƙasa gaban su Ammah,
Yana zubesu yaƙarara fita, still dai bai daɗe ba yaƙara dawowa, hannu sa ɗauke da wata ƙatuwar jaka, ɗakin dake cikin masarautar ya shiga da jakar ciki zuge zif ɗinta yayi ya fito da wasu kwalabai ya ajiye su agefe, sannan yazaro wata leda da farin abu ajiki, sannan ya ɗauke jakar ya fito da ita tare da ledar mai farin abu aciki,
Yana fitowa yace "Sarauta gaba da baya sai kayi ko ba kaso, komai yazama daidai,
"Wai yaushe nafara wasa dakai ne bana son fa raini kasani ko,
Khalid yace "to sarki nayi shiru ayi haƙuri kar asa fadawa subi takaina,
"Hmmm kawai Meer yafaɗa yana miƙewa tsaye, yana naɗe hannun rigar sa,
Kallon sa yayi yace "step 1,
wasu mugayen bulale Meer ya É—auko daga gefan sa wajen guda shida, sai ya jefawa Khalid guda uku ya É—auki guda, uku cafewa Khalid yayi sannan ya ajiye ledar agefe,
Tun kan su ƙarasa kansu suka tarwatse cike da tsoron abun da zasuyi musu, amma tun kan suyi wani yunƙuri suka rafar musu,
kan kace mai kawai sun fara sauke musu kawai kan me uwa jawabi suka fara yi musu wankan jego da bulalen duk inda suka samu duka suke,
basu wani dake su sosai ba suka rabu dasu saboda a kwai step 2,
Khalid ne yace saura step 2 ko miƙo wannan ledar,
Wani kallo ya watsa masa mai kama da harara "yace waye zai taɓa wannan ledar bayan ka gama ban labarin ta kuma saikasaka ni in taɓa sude shiga daga ciki gaba ɗayan su sai ka aiwatar tunda kai kasan kan abun,
Dariya yayi masa yace matsoraci kawai, kuma wallahi idan baka bini a hankali ba sai nasaka maka wataran dan haka ka kiyaye,
"Hmmm inbaka fasaba, yanzu ma zaka iya ai,
Khalid zaiyi magana kenan, Meer yace kaga bacci fa nake ji banason surutu muyi abun da ya kawo mu,
"angama ranka ya jiƙe,
Bai kulasaba daga nan suka tusa su suka shiga cikin É—akin nan, da mamakin su sai suka ga babu komai a É—akin wayam ankwashe komai,
Duk zama suka yi aƙasa,
A hankali Khalid ya buÉ—e wannan ledar saiga wani farin gari aciki,
A hankali yabi ta bayan su ɗaya bayan ɗaya ya zuba musu shi ajikin su, su kan su basu san mai yayi musu ba, yana gama zuba musu ya ƙulle ledar ya mayar da ita yanda take bai bari ko kaɗan ta taɓashi ba,
Bakin ƙofa ya koma kusa da Meer yana dariya yana kallon agogon hannun sa, tun kan loƙacin da ya ɗeba ma su cika, suka fara soshe soshe tun sunayin abun kaɗan har ya fara yawa nan suka shiga hauka suna juyi matan kam tuni sun cire mayafan su da ɗan kwalayen su,
Duk sun fara fita hayyacin su saboda mugun ƙaiƙayin da suke ji sai gashi babu babba ba yaro wannan ya miƙawa wannan bayan sa wannan ya miƙawa wani yana cewa "kuso sa min ku sosamin,
Shide Khalid inbanda dariya da yake musu babu abun da yake yi shima kansa Meera abun yabashi dariya amma saboda shi shine yayi ɗin yake gani da asara haka yayi gum da bakin sa yaƙi darawa,
Haka sukai tayin haukan ƙaiƙayin da suke ji, kuma shi ƙaiƙayin nan ko mai zasuyi bazai daina, saboda abun da ya zuba musu, garin karara ne (wani abune da ake samo shi a gona mai shegen ƙaiƙayin masifa dan gaba ɗaya yake fitar da mutum cikin hayyacin sa, sunan shi KARARA nasan wasu zasu iya sanin shi wasu kuma basu sanshi ba)
Khalid ya kalli Meer yace "nagama nawa saura step 3 nakane wannan,
matsawa yayi yabasa guri, yanda zai samu damar yin nasa step 3 É—in,
Shikuma Meer kwalaban da Khalid ya ajiye guda biyu su ya ɗauka saida yaje wajen bakin ƙofar sannan ya kunce murfin tare da kwantar da kwalbar aƙasa,
.yana ajiyewa zuma ta fito daga ciki, ɗayar ya ƙara ɗauka ya buɗe ta itama sannan ya ajiye ta, yana ajiyewa suka fita daga ɗakin da sauri tare da rufowa suka ƙulle su a ciki tare da zumomin,
Tun kan subar falon suka fara jiyo ihunsu ga zafin ƙaiƙayin karara ga kuma zafin cizon zuma da suka fito da yawa suka fara cizon su,
Suna jiyosu suka tattara kayayyakin su sannan suka fice daga ciki tare da rufe ƙofar itama duka ƙofofin saida suka rufe su, sannan suka tafi part ɗin Maama suna ci gaba ta tattaunawa akan abun da sukayi musu, ransu tas ko ajikin su daɗin su kawai suke ji musamman Meer da shi abun ya shafa, shi duk da haka gani yake yayi musu mai sauƙi kawai tunanin abun da zaiyi musu gobe yake, da haka har suka ƙarasa ciki........,