Sashe 5
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maama ta kalli ummy tace "To kinji abun da É—anki yace ko sai ki duba mana ita,
Ummy tace Allah Maama kina shagwaɓa yaron nan ƙiri idan yayi abu dai kinuna bashi da laifi saida azuba masa ido yaitayin abun da yaga dama idan ba dakatar da shi yanzu ba sai yaushe wallahi nan gaba nake tsoro aure fa zaiyi iyayen sa ma yana musu haka to yazai ƙare sa matar sa ai ba wacce zata iya zama dashi da wannan halin nasa wallahi,
Maama ta saki murmushi mai ciwo ganin su duk basu fahimci komai ba game da ɗan nasu, suna zaune dashi amma basu san abun da yake so ba sa wanda baya so basu iya karantar yanayin sa duk abun da yayi basa fahimtar sa daidai sai dai suyi masa wata fahimtar daban ahaka taya suke tunanin zasu iya gano sauƙin sa ko canzawar sa duba da yanda yake da zuciya da saurin fushi amma basa iya controlling ɗinsa bare har su fahimcesa su ɗorasa a hanyar da suke so zaman su kam da gyara dole sai ta tashi tsaye ta daidaita musu zaman su in ba haka ba za aitayin abu babu ci gaba, kina ganin da juya aiken sa nayi amma baidawo ma gidan ba sai yau kuma bashi ba aiken masa magana yayi min shiru, taya mutum zaiji daɗin zama dashi da irin wannan halin,
Kallon ummy tayi tace "Daga faɗar gaskiya aidai yayi ƙoƙari tunda de har ya faɗi abun da za ayi mata kallo ɗaya yayi mata yagane hakan ke kuma sai kiƙarasa sauran nidaman bansan kema likitan bace, maza duba mana ita yaro bashi da lafiya dole sai ansa shi yayi abun da baya so, kunji mun mutane ana dole ne shima dubawar yake buƙata idan kingama da ita kije ki duba min yaro duk kunbi kun saka shi gaba ke kiyi masa shima yayi masa, Ni wallahi gwanda ma da yake muku haka indan yabiye muku sai kusa mishi hawan ruwa ba gaira ba sabun ina dalili to wallahi ku fita ido na tun wuri kar musa ƙafar wando ɗaya samu ehe dan Mutum bazaiji daɗi ba,
Ummy kamar ta haɗiyi zuciya haka take jin kalaman Maama Abu kam da taƙaici ma ya ishe shi baigama jin karshen maganar ba ya fice daga falon dan inya tsaya yaci gaba da sauraron mahaifiyar tasa akan marar kunyar ɗanta zuciyar sa sa zata iya bugawa gwara yabata guri idan tagama yadawo,
Duk tana lure dasu aranta kama sai murmushi take, daman tanasane tayi musu haka, tasan daman Abu bazai zauna ba kuma daman haka take so,
Ummy ta buɗe baki zatayi magana, Maama ta dakatar da ita tace karki ce komai dan Allah kiyi ki duba baiwar Allah nan tana kwance ba lafiya kunzo kuna ta ɓatawa mutane loƙaci akan abun da bai taka kara ya karya ba,
Iya shaƙa ummy ta shaƙa bayanda ta iya cike da taƙaici dole ta tashi taje tafara duba daddar, juyowa tayi ta kalli Maama murya kamar zatayi kuka tace "Maama to damai zan dubata kayan aikin ma duk suna can gidan kuma yaje yaƙi ɗaukowa idan kaji yanayin da tayi maganar dole ta baka dariya kamar wata ƴar ƙaramar yarinya,
Dan haka kuwa Ummy ta shiga yi mata dariya tace kiyi mata da zanin ku ai jini ne kawai ki goge dashi,
Su Ameesha ma basu san loƙacin da suka saka dariya ba, cike da jin haushin su da taƙaicin maganar da Maama tayi mata ta kalli Ameesha "Tace munafuka ai hardake kema kina so ki koyi halin sa kinsan komai dan iskanci kinshigo kina kuka na tambaye ki amma kince min babu komai zankama kine wallahi kuma meya hanaki ɗauko kayan idan shi bai ɗauko ba ke meye amfanin zuwan ki tayi maganar cikin fushi kamar zata make Ameesha,
Shiru Ameesha tayi tana tunanin ashefa ance su ɗauko kaya ai wallahi ita tama manta abun da yakaisu gidan gaskiya sunyi shirme daga ita har shi ɗin ko da yake yanayin da suka tsinci kansu bana daɗi ba shi haddasa musu mantuwar abun da sukaje ɗaukowa dan ko gurin da tayi amai ga sun ɓata gidan amma babu abun da suka gyara suka fito,
Ummy ta ɗan daka mata wata ƴar ƙaramar tsawa tace ba magana nake miki kika min shiru kema rainanin zakiyi kenan,
"A'a a'a baiwar Allah bafa ita takar zomon ba rataya aka bata, ai ba ita tayi miki laifi ba malama da zaki huce akanta, kaina zaki zo sai ki huce taƙaicin ki, tunda ba kya son gaskiya Maama tana maganar tana mata dariya, agabana zaki taɓa ta itama ai jikata ce kar ataɓa min ɗaya daga cikin su duk wanda aka taɓa sai munyi Shari'a da mutum ehe dan bazan haƙura ba, mutum yabi mu yanda muke so ya zauna lafiya ina bahaka ba kuma muyi ta ƙunsa masa abun.....(hhhhh kai hajiya Maama baki da dama wai baƙin ciki shine aka sakaya ya koma abun)
Ummy da taji abun yafi ƙarfin ta bata ƙara gangancin furta wani abun ba taja bakin ta tayi shiru tana shaƙar abun kamar yanda Maama ta faɗa,
Tissue taje ta ɗauko tazo ta fara goge mata jinin da yaɓata mata fuska, da haɓo tas ta goge mata shi fuskar ta ta fito tsaf da ita ashe ba wani ciwo ajikin ta ko kaɗan iya jinin haɓonne ta gyara mata ɗaurin ɗan kwalinta sannan taje ta ɗebo ruwa ta shafa mata a fuska wajen sau uku har wajen wuyanta, tana gamawa kuma dadda ta sauke numfashi,
Afurgice tafara sunbatu dan Allah kuyi haƙuri wallahi bazan baku ba kar ku ƙwace na roƙe ku, ku bani ku bani ku bani tayi maganar hawaye na fitowa daga idon ta batare da ta buɗe idanun ta ba,
Da sauri Maama taje ta riƙeta tana kiran sunan ta gaba ɗayan su ma kanta sukayi suna kiran ta, tare da taɓata tun tana maganganun da ƙarfi har tafara yi a hankali sakamakon jin muryoyin su data ringa ji,
A hankali ta shiga buɗe idanun ta har ta ware su akan su ɗaya bayan ɗaya ta shiga kallon su, sannan tayi saurin tashi zaune, tashin ta yayi daidai da shigowar su Abu shida papa, dan haka sai suka ƙaraso ciki da sauri ganin ta tashi zaune,
Tana tashi zaune ta kuma fashewa da kuka, sai da ƙyar suka bata baki tayi shiru,
Sannan Maama ta tambaye ta suwaye waÉ—an da take magana akai kuma meya ya fitar da ita daga cikin gidan, ko wasune suka sace ta,
Maimakon tabata sai tasake sakin wani kukun tana tambayer suna ina ya akai yazo nan waye ya kawo ta a ina suka sameta,
Nan dai Maama ta fara bata labari "tunda safe muka nemeki muka rasa muka tashi hankalin mu gaba É—aga ko ina na gidan nan anduba ba asame ki ba har waje aka bata cigiyar ki to abun mamaki mai gadi yace shi baiga fitarki ba shiyasa mukayi tunani to kodai sace ki akai muna cikin binciken kuma sai kawai message ya shigo wayar ummukursum (Ummy) tana dubawa taga an rubuto,
_matar da kuke nema kuzo bayan masarautar ku ku ɗauke ta gata ban akwance idan kuka ɓata loƙaci kuma zaku iya rasata bissalam_
Tana ganin ta nuna mana munyi mamakin ta yanda akayi suka samu number ta muka kira layin kuma har ankashe shi, shiyasa bamu wani wahalar dakan mu mkasanar dasu mukaje gaba ɗayan mu inda aka kwantanta mana muna zuwa kuma kamar yanda suka faɗa muka tarar da ke akwance aƙasa ke ke kaɗai agun shine muka ɗauko ki, kinji ta ta yanda muka same ki daga haka kuma bamu san komai ba amma ke ya akai kika fita daga, gidan,
Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un nashiga uku na cewar dadda da tagama jin yanda akai, sannan ta ɗora dacewa wallahi kawo ni sukayi, kuma babu wanda ya fitar dani daga gidan nan da ƙafata na fita loƙacin da nafita me gadin inajin bai lura dani ba ko kuma yayi wani wajen saboda ƙofar abuɗe take na fita, mutane ma kuma duk basu fara fitowa ba saboda safiya ce, shiru tayi na ƴan sakanni tana share hawayen ta sannan taci gaba da maganar,
"Ba komai ne dalinlin fita ba face zuwa nayi Inna ɗauko kudaɗennan da takaddun sa, tunda Allah yasa ku iyayen sa kun baiyyana in ɗauko indamƙa muku amanar da yabarmin, dalilin da yasa ban sanar daku ba gudun matsala ta faru garin yin maganar wani yaji mu shiyasa nayi shiru da bakina batare da kowa ya sani ba na yanke shawarar inje nikaɗai in ɗauko ta batare da kowa ya ankare da fita taba daga gidan,
Nidai har na fita na nufi unguwar da na ajiye kuɗin daman agidan da muka zauna na ɓoye su suna cikin wata ƴar akwati na haƙa rami na ɓoye aciki,
Ina zuwa gidan yana nan yanda na barsa saboda daman namune siyansa mukayi kuma takaddun sama suna cikin akwatin duk na haÉ—a saboda gudun matsala, kar su sace takaddun su suyar dashi,
Da ƙyar na gano inda nayi haƙar acikin gurin da muke girki nan, dake da tukunya agidan da abun wuta na haɗa murhu na ɗan ɗumama gurin yanda zaimin saurin jiƙuwa, sannan nafara haƙowa, har nagama haƙowa na zarota na goge ƙurar da tayi sannan na samu wani mayafi na nannaɗe ta aciki sannan nasamu wani buhu nasaka, ina shirin fitowa kawai wasu mutane suka danno gidan, kuka ta fashe dashi tana goge hawaye tace "duk tsawon loƙacin da na ɗauka shakara da shekaru, amma mugayen mutanen ashe suna lure dani saida suka bini azzalumai bansan ya akai suka ga fita taba,
Suna shigowa suka ƙwace buhun suka zazzage sa suka buɗe akwatin suka fito da duka takaddun sukace sai nasaka hannu ajiki shine da naƙi sukai ta dukana ina roƙonsu amma sukaƙi barina daga nan kuma ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai yanzu, cikin raunin murya da hawaye da yake tayi mata ambaliya a fuska ta ƙara maganar,