← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 103

Sashe 26

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciyace ta kuma ɗiban Papa yaƙara caƙumo wuyan sa cikin ɗaga murya yace "su waye sauran kafaɗa min kai dasuwa kuke son ganin bayan mu! mai yasa! mai yasa!! nace mai  yasa zaka min haka mai na tsare maka? Kai da suwa waye...!!?

Shiru Waziri yayin da wani ɓacin ran yake taso masa daga ƙasan zuciyar sa, cikin ɓacin rai ya fara girgiza kai yana cije baki yace "kasake  ni.

Papa yace "baza a sake kanba, kayi abun da zakayi,

Maama da taga abun nasu yana shirin wuce gona da iri yasa tafara jan Papa tana cewa dan Allah maiye hakan da girman ku muje ciki mu zauna, abar maganar nan yanzu muji da maganar mutuwar yakamata ake ayi mata wanka a sallace ta, gawa tunjiya a ajiye kamata yayi afara gamawa da ita kafin ayi komai daga baya, kasake shi dan Allah,

Ƙin sakin shi Papa yayi saboda tunda yake baitaɓa jin ɓacin rai irin nayau ba,

Abdullah ne(mahaifin sam kuma ɗa ga waziri shine babban ɗansa) yaƙarada gurin shima yana jan Papa amma duk sun kasa raba su sai kallo yadawo kansu aka manta da gawar dake kwance agun,

abundai ba daÉ—in gani, dan wasuma har sunfara barin wajen daga cikin ma'aikatan gidan,

Abu dake gefe shima ya gama cika ƙiris yake jira ya fashe dan idan yatashi baza aji daɗi ba sai ran kowa yaƙara ɓaci,

___Cike da takunsa na isa da ƙasaita yake takowa gurin, jin ƙarar takun sa yasa wasu suka juya suna kallon sa,

Hannun wansa gaba É—aya acikin aljihun wandon sa, a hankali yake tafiya cike da kwanciyar hankali sanye akan fuskar sa, kamar baisan abun dake faruwa ba,

yana zuwa gurin ya nufi wajen su Papa kai tsaye, agaban su ya tsaya yana ƙare nusu kallo kamar bazai tanka musu ba, saidai yagama shan ƙamshin sa, sannan ya buɗi baki ahankali kamar mai ciwon baki,  murya ƙasa ƙasa yace "Papa minti biyu yayi maganar yana kai hannun sa kan hannun Papa yana ɗan jansa, Papa baisan loƙacin da yasaki she ba,

Yana ƙara haɗe rai, Meer ya kalli Maama da ido yayi mata alamar da taja shi subar wajen,  gyaɗa masa mai tayi sannan ta riƙo ɗayan hannun Papa,

Tunda Meer yazo wajen Waziri yake binsa da kallo sai yanzu wani abu ya faÉ—o masa arai,

Da sauri ya zura hannu aljihun gaban rigar sa zai É—auko wayar sa,

Meer ya matso kusa dashi tare da dafa kafaɗar sa kamar abun arziƙi sai yayi ƙasa da murya tayanda babu wanda zaiji mai yake cewa,

Can ƙasa ƙasa yace "ka makara maiyasa baka duba ba tun aloƙacin da yadace yanzu loƙaci ya ƙure maka, yanzu muka fara muzuba mugani waye zaiyi winner,

Yana kaiwa nan ya haɗe rai tare da matsawa daga kusa dashi sai kawai yajuya ya kalli Papa da shima   shi yake kallo ga mamakin Papa sai kawai yaga Meer ya ɗage  gira ɗaya yana jinjina kai, sai Papa ya mayar da kallon sa kan Maama sai yaga itama tana murmushi da jinjina masa kan,

Mamaki abun yabasa to mai suke nufi da hakan,

Maama da taga kallon da Papa yake mata shima sai ta jinjina masa kai,

Wata macece daga cikin ƴan uwan Hindatu ta ƙaraso inda suke tana wani binsu da wani irin kallon banza, tace "wallahi wallahi baka kashe banza ba sai munɗau mummunan mutaki akan ka, a daren nan,zaka ga abun da zai faru,

Juyawa tayi ta kalli Sauran ƴan uwanta tace "ku ɗaukota muje gida ayi mata sallah, dan naga gaba ɗayansu neman wulaƙan tamu suke, kuma babu wanda zamu ɗagawa ƙafa daga shi har su, zamuyi shiri na musamman,

watama taƙaraso gurin tace yaya wai kina nufin ahaka zamu tafi murabu dashi idan kuma ya mutu ba ai wallahi dashi zamu tafi daga nan sai station dan wallahi sai munyi shari'a dashi baikashe banza ba,

Waziri da yayi wuƙiƙi da ido yana raba ido ya kalle su ya kalli su Papa da suna jin abun da ake cewa amma basu iya cewa komai ba, koda yake ba laifin su bane duk wannan abun laifin Meer da shi ya shirya masa komai kuma gashi sun gani bashi da damar kare kansa, baida bakin magana, dole ya amshi duk hukuncin da sukayi masa kafin gaskiya ta bayyana, kuma yayi alwashin sai yaci mutuncin Meer sai ya wahalar dashi sai yarama wannan wulaƙancin da yasa akayi masa agaban mutane, anci mutuncin sa,

Yana wannan tunanin bai gama
ba yaji saukar naushi ta bayan sa, da sauri ya juya yana kallon mai dukan nasa, maza biyun nanne suka rufar masa suka fara dukan sa,

Da sauri Meer yacewa kowa nagun yabar wajen da kan kace mai kowa yabar wajen gudun ɓacin rai saboda yanda yayi maganar kowa zaiyi tunanin idan bai tafi ba zai iya hucewa akansa,

su Papa ma tuni Maama tajasa suka bar wajen daman Æ´aÆ´an sa sun daÉ—e da barin wajen,

Waziri tun yana jurewa yagadai basu da niyar barinsa sai yafara ƙoƙarin ƙwatar kansa, amma yakasa,

Saida sukayi masa dukan tsiya har ba ya iya tashi amma duk da haka sunƙi rabuwa dashi,

Meer dake gefe ya haɗe hannuwan sa yana kallon su so yake sai ya tabbatar da sundake shi sosai dukan ya ratsa shi sannan zuwa loƙacin maganin da yabata zai saketa, ashe duk kulane ma basu yi ba amma tana numfashi sama sama amma tashin hankali da kuma yarda da videon da suka gani ya hanasu gane hakan,

Daman burin Meer kenan so yake sai yafara wulaƙan tashi yasa angalabaitar dashi yarama abun da yayi masa na allurar da yayi masa shiyasa shi kuma ƴa ɓullo mishi tanan ba shi zai dake shiba amma yasa andake shi kuma yasa kowa yadai na ganin sa da mutunci an wulaƙantasa agaban mutane, Meer baima yi zaton abun zaikai haka saima kuma yaga har yafi yanda yake tunanin abun ba ƙaramin ƙayatat dashi yayi ba,

Suna cikin jibagar sa matan suna ƙara zugasu,

loƙacin kuma da Meer ya ɗauka sun cika dan haka yataka a hankali yaje kusa dasu tare da janye waziri daga gurin su, suka ƙara binsa zasu dake shi, Meer ya daka musu tsawa yace "ya isa haka kada wanda yaƙara taɓa sa saboda bashi yakashe taba!

Duk saranda sukayi jin abun da yace suna binsa da kallon ƙarin bayani,

Shima suÉ—in yake kallo yace "eh abun da kukaji gaskiya ne bashi ya kashe ta ba,

Ɗaya daga cikin su da ta fola dashi saboda bazawara ce kallo ɗaya taji yayi mata, a hankali tace "bashi yakashe taba to waye ya kashe ta bayan gashi a video ƙiri ƙiri shine kace bashi bane,

Sauran ma suka hau kansa da surutu suna kinfara baki sai yayi banza dasu yaƙi basu amsa saida suka gama surutun nasu sannan yasaki waziri daga ruƙon da yayi masa,

Ya nufi gurin da take yana zuwa yaye abun da suka rufa mata, sannan ya wuce gurin motar da aka kawota ya buɗe ya ɗauko ruwa, ya dawo ya yayya fa mata shi a fuska take ta ajiye wani nauyayyen numfashi, ƙara watsa mata yayi taƙara sauke wani numfashin saida yayi mata haka sau uku sannan ya rabu da ita,

Gaba É—ayan su sukayo kanta suna mamakin wannan abun al'ajabin daman bata mutuba to duk shiri ne kenan amma yasa suka kamasa da duka, maiyasa yayi hakan,

A hankali ta shiga buɗe idon ta saboda ciwon da yake mata gaba ɗaya, dan baƙaramin duka taci ba adaren jiya,

wani irin farin ciki Æ´an uwanta sukaji harda masu hawayen murna Æ´ar uwarsu na raye,

tana buÉ—e idon ta data gansu sai kawai ta sakar musu kuka,

Babu wanda yabi takan Meer ko tambayar sa ya akayi mai yasame ta duk sun manta dashi, wasu kuma tsoron tunkarar shi suke saboda yanda ya haÉ—e rai kamar marar imani,

ÆŠagota sukayi babbar yayar su ta rungume ta tana goge mata hawayen ta, nan suka fara murnar ganin ta, daga nan suka É—agata tsaye suka ce amatso da mota su tafi gida, daga yau tagama zaman gidan saidai ya biyota da takaddar ta,

Suna miƙewa zasu shiga mota Meer yasha gaban su, gaba ɗayan su da mamaki suka ɗago suna kallon sa,

Malam lafiya kasha gabanmu mai kuma kuke so mu tsaya muyi muku, anan,

Wani irin banzan kallo Meer ya watsa musu mai cike da tsana, sannan ya É—auke idon sa daga kansu waya ya É—auka yayi dialing É—in wata number ana É—agawa yace, shigo,

suna gurin basu motsaba saiga wata mota tashigo cikin gidan aguje tana zuwa kusa dasu aka taka burki da ƙarfi agaban su, ko kashe motar ba ayi ba, nacikin motar ya fito hannu sa da bunduga tare aunka a a ɗayan hannun jikin sa kuma sanye kayan ƴan sanda,

U are under arrest, yafaɗa yana ƙarasowa kusa dasu,

Gaba É—ayan su cike da furgici suka shiga kallon junan su,

Meer yace mai kake jira,

gaban Hindatu yaje ya tsaya, yana nuna mata aunka ɗin kuka tafarayi tana girgiza masa kai tace ƴallaɓai Wallahi ban aikata komai ba kar ka kamani dan Allah na roƙeka kayi haƙuri wallahi zan faɗi duk gaskiyar abun da nasani amma karka bari yatafi dani kodan zumuncin dake tsakanin mu, nifa matar mahaifinka ce kuma nawa laifin ma aciki kaɗan iya azabar dakayi min jiya ta isa haka, kayi haƙuri dan Allah kamin rai ka rufamin asiri wallahi sharrin sheɗanne, duk nema take ta fita a hayyacin ta, dan har tafara jin daɗi zasu tafi gida sai kuma gashi wani bala'in yaƙara kunno mata,

ko sauraron ta baiyi ba, yakama ta yasaka mata sarƙar yana janta suka fara hauka zasu ruƙota Meer ya buga musu tsawa, hakan ya sasu dakatawa,

Yana kamata ya buɗe bayan motar ya turata ciki sannan yaje ya ɗauko waziri da yana kwance yakasa taɓuka komai, shima ciki ya jefasa......,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣
Chapter 26 · 0% Book details