← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 103

Sashe 79

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Abban Ameesha ya shiga wasiwasi, amma bai nuna hakan ba a fili yunƙurawa yayi zaiyi magana,

Meer yayi saurin dakatar dashi, sannan yace "Uncle kayi shiru ka saurare ni da kyau duk wannan maganar kake yi bamai yiyuwa bace, dan baza'a taɓa barin taba kamar yanda kake so, kabari zangaya maka hujjoji na, idan nagama sai ka yanke hukuncin da kaga ya kamata..

"Da farko a labarin da ka bamu da kuma yanda kazo kana tambayar ina sauran suke, alamu sun nuna bakasan da mutuwar matar kaba, saɓanin nata labarin da ta bayar tace loƙacin da ake neman ka za'akashe ka, loƙacin haihuwar yarinyar ku ta rasa ranta wajen haihuwa,

A zabure Dadda ta ɗago zatayi magana yace "kimin shiru kar nasake jin bakin ki, har sai nagama faɗar abun da zan faɗa idan kuma ba haka ranki zaiyi mummunan ɓaci,

Yanzu kam Abban Ameesha kasa cewa komai yayi,

Meer yaci gaba da cewa, "na farko kenan, sannan na biyu, me yasa mutanen da tace suna neman ku suka kama kowa amma ita basu iya kamata ba? Me yasa basu kashe yarinyar ba tsahon loƙaci har suka bari ta girma bayan kuma tace neman ta suke ido rufe sannan duk inda taje suna sane da ita, taya har suka san da ita amma basu san da yarinyar ba,

Taya kike ciyar da gidan ke da ita, kama daga sutura kayan sakawa abinci abin sha, wutar nefa, kuma me yasa duk wanda ya raɓeki zai taimaka muku baki yarda,

Sannan kuma me yasa bayan dawowar ta kano har ta ita kama gida ta zauna basu taɓa zuwa wajen taba, ta akai shi da akai kashi Prison daga baya kuma ya kasance a wani gidan, da ban, me yasa idan sune suka ɗauke shi me ya hanasu kashe shi, tunda sunzo yayi musu signing ɗin takkaddun sun samu abun da suke,  ɗan dakatawa yayi  yana kallon su, kafin yaci gaba cewa.....

"Hmmm duk bama wannan ba meye dalilin ki na sa ƴarsa tafara aikatau agidan wanann mutumin alhalin kuma kince mahaifin ta yabaku dukiyar sa domin ku kula masa da ƴarsa, kusa ta makaran ta tayi karatu domin ta ceto sa, amma sai duk bakiyi hakan ba, kika ce kin ɓoye masa, sannan kince dukiyar sa tana ajiye kin ɓoye tsawon shekaru nan,to amma shi kuma yace loƙacin da yake can gidan ansha kawo masa ita ya buɗe yaƙi buɗewa saidaga baya aka kawo masa ita har anbuɗe, alhalin kuma yace duk kunsan password ɗin sa, dan haka ke da take hannun ki ke kika buɗe ta kenan?

Sannan bisa ga dukkan alamu sun nuna akwatin nan batayi kama da wacce aka binne acikin rami ba tsawon shekaru, an killace tane a guri me kyau,

A aranar da kika fita kikace kinje ki ɗauko dukiyar sa da kika ajiye ƙarya kike duk shirin kine, ƙarewa ma number da kikayi amfani da ita wajen kira number wayar kice, saboda aloƙacin bamu daɗe dawowa ba ba tayanda za'ayi ace wani daga waje yasamu number ta amma sai ki ɗauki number Maama, tunkan ki fita sannan da kika kira ki kashe wayar gaba ɗaya, dan kar ta shiga, 

Tun daga wannan rana nafara saka miki ido, har na gano bakin ku ɗaya da wannan mutumin, ta hanyar mutumin da kika sa ya shiga mota ta, da na tambaye sa yaban number matar da takirasa, ina dubawa kuma sai naga number da aka kirace loƙacin da kika ce kinje ɗauko dukiya, kuma yace mace shiyasa na fara ganowa baki da gaskiya, sannan kika ɗauki hotona kika tura masa, sannan kika sa aka shigo har cikin nan aka shiga mota ta, saboda aranar da na shirya fitar, idon ki yana kan mu, saboda kin tambayi jikar ki ta gaya miki abun da muke shiryawa, aka hanata sai ki saka ido akan ganowa, loƙacin da nafita daga gidan nan keke kaɗace a falo kuma da na fita na ƙara dawowa ke kuma kikasan yanda zakiyi wani yashigo cikin mota ta,

Tambaya ta ƙarshe kince wayar sa wasu ta faɗi a asibiti, to me ya kawo sim ɗin sa cikin akwatin sa, kuma ajiya da muke cikin bincike, na saka layin ana ta zare kuɗaɗe daga ciki, alhalin kuma ATM ɗin sa yana hannun ki....,

Bari intsaya anan, ina buƙatar waɗannan amsoshin kafin in cigaba, idan kin faɗe su nafasa yin sauran, zan barki, namiki alƙawarin bazan ƙara magana ba,

Shiru yayi yana kallon ta, ita kuma tayi ƙasa da kanta,

Abban Ameesha kam inbanda wata uwar zufa da take tsatstsafo masa babu abun da yake jikin shi kam take yaɗau ɓari ya rasa inda zai sa kansa daga tsayen da yake yayi zaman dirshen a ƙasa,

Sauran mutanen kam babu me bakin magana kowa yayi shiru yana sauraron sa,

Shiru da tayine yasa ta fara fusata, cikin daka tsawa yace "answer the question I asked you, DON'T LET ME REPEAT IT AGAIN...!!!!!!
[21/11, 9:22 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                    *_🅿️47_*
                  

..........Duk wannan tsawar da yayi mata bata iya ɗagowa ta kalle sa ba, tadai yi ƙasa da kanta kawai, tana muzurai da idanu, dan bata san da kalaman da zatayi amfani da su ba wajen kare kanta akaro na biyu,

"Bazakiyi magana ba! Meer ya kuma nanata mata,

Ɗagowa tayi ta kalle sa, ido cikin ido tace "amsar me kake buƙata, bayan ka faɗi komai to ni banda wani dalili na, nayin hakan kafaɗi duk abun da nayi, kayi daidai, dan haka sai kayi min duk abun da zakayi min, ta faɗa tana sauke masa harara, cike da rashin danasani ko tsoro atattare da ita,

Saida kowa yayi mamakin jin furucin ta,

Basu san da farkawar Ameesha ba, sai ganin ta kawai sukayi a gaban ta,

Tsugunnawa tayi a gaban ta tare da riƙo hannun ta tana me ƙurawa fuskar ta kallo kamar zata cinye ta, ko kuma yauce ranar da ta fara ganin ta,

Cikin daskarewar murya, ta kira sunan ta cikin wani irin yanayi, tace "Dadda...!

Dadda kasa É—agowa tayi ta kalle ta, saboda yanayin da ta kira sunan ta Saida taji sa har cikin ranta,

"Dadda me yasa? me yasa? me yasa Dadda zaki min haka, dan Allah kice da wasa kike, Dadda jinake kamar zata fashe zafi take, Dadda zafi take min Dadda ciwo taɓa kiji, Dadda kece komai na kece farin ciki na, dake na taso dake nake rayuwa banda wani sama dake a faɗin duniyar nan, please Dadda...Dadda ki gaya min ba gaskiya bane kifaɗi gaskiya ko zuciya ta, zatayi min sanyi, Dadda kisanya shalelan ki ciki farin ciki kamar yanda kika saba, kar ki canzan sabuwar rayuwa, rayuwa ta dake ta saba, bazan iya jurar zama a haka,

Sosai Ameesha take kuka tana riƙe mata hannu, kukan da take kamar ranta zai fita, cikin wani sabon kukan ta kuma cewa "Please Dadda ta karkiyi min haka kinji kaka ta kinga fa kece kika haifa min mahaifiya ke nake kallo kamar uwat..........., Ɗifa tayi ta tsaya da komai babu kukan kuma takasa ƙarasa maganar da take, sakamakon ture tan da Dadda tayi,

Da yatsa ta nunata tace "keda duk atunanin ki zaman da nake dake zaman tsakani da Allah nake, to kin yaudari kanki, kuma ni ba kakar ki bace kar ki sake kirana, da kakar ki, domin kakar ki ta daɗe da tafiya domin nadaɗe da  aikata inda uwar ki ta tafi ita da mijin ta,

Saura kaɗan Ameesha ta faɗi jin kalaman ta, saida Meer yayi saurin riƙo ta,

Duk da shima daurewa kawai yayi baije ƙasan ba, domin furucin Dadda ba ƙaramin sakasu a ruɗu yayi ba, duk kan ilahirin mutanen wajen babu wanda be shiga sabon tunani ba, (kamar de yanda nima ta barni cikin tunani....,

Da sauri Abban Ameesha ya taso yana kallon ta kamar zai cinye ta, yace "me kika ce, harara ta watsa masa, sannan tace"abun da kaji na faÉ—a,

Shiru ya ƙara yi tare da ja baya dan lamarin nata yafara basa tsoro,

Meer kam a fusace yayo kanta zai sauke mata kwandon bala'i, Papa ya dakatar dashi cike da takun sa na manyan ta ya shiga takowa zuwa inda suke,

"Kallon Meer yayi yace "Babana samu guri ka zauna, ka kamata ku koma gefe, kaima nemi guri ka zauna ya faÉ—a wa Abban Ameesha, sannan ya kalli kowa yace ya isa ayi shiru kowa ya nutsu, yayi maganar da babbar murya,

Kowa guri ya samu ya zauna kamar yanda ya umarce su,  sannan ya maida duban sa ga Dadda da tayi wani ƙeƙam kamar ƴar sanda, sai faman huhhura anci take,

Gyara tsayuwar sa yayi yana kallon ta da kyau sannan yace "Baiwar zaki iya zama,

Kwarjinin sa yasa bata iya musu dashi ba, tasamu guri ta zauna,

"Tom bama son ɓata loƙaci muna buƙatar bayani daga gare ki, me kike nufi da maganar da kika faɗa inso kiyi mana gamsashen bayani yanda kowa zai fahimta, ina fatan kin gane ko? dan gwanda kiyi bayani tun kan kijawo kanki,

yana gama faÉ—ar haka ya koma gurin sa shima ya zauna,

Shiru gurin ya ɗauka na tsawon mintina ba tare da kowa ya ƙara magana ba, haka itama batace komai ba,  har saida Abuuu ya kuma yi mata magana sannan,

......ÆŠagowa tayi tana kallon wani wajen daban, sannan tace "kamar yanda kukaji na faÉ—a hakanne, niÉ—in ba wacce kuka sani bace, shiru ta kuma yi sannan tace,

  "ME AND HER WE ARE TWINS.......!!!!!
Chapter 79 · 0% Book details