← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 103

Sashe 73

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

           *_Typing........✍️✍️_*

  
               *_🅿️43_*

_shekaran jiya nayi page 41 jiya kuma zan saka page 42 na manta ban gyaraba number ba, na kuma yin posting da hakan page 41, dan haka yau nasaka page 43, idan kuka maida na jiya Page 42, na yau kuma 43, kar wasu su rikice, shiyasa nayi muku bayani_

_________gaba ɗaya an tada hankali acikin asibitin ana neman Dadyn Rasheeda, amma anrasa shi sama ko ƙasa,

Can gurin me kula da CCTV camerar asibitin a kaje inda Meer yasa aka saka masa daukar da akayi jiya,

matsalar da aka samu ba'a saka Camera a É—akin saida gaban É—akin da akwai, kuma sunga shigar wasu maza kuma fuskokin su duk arufe, ashema tun adaren ranar aka É—auke sa, bayan shigar su kuma sai wuta ta É—auke sai can kuma daga baya hasken ya dawo,

Nan aka fara tambayar me yasamu wutar asibitin ya akai har suka fita da ita batare da wani yaga loƙacin da akayi hakan ba, nan aka gaya musu can cikin dare ne dan yawancin ma'aikata kowa ya tafi gida, sai masu dutyn dare ne suka rage, kuma kowa ya rasa ta yanda akayi aka kashe wutar daga baya kuma aka dawo da ita,

Abun ya cakuɗaiwa Meer ya rasa ta inda zai ɓullowa lamarin, wunin ranar suna abu ɗaya amma sun kasa gano mafita shida Khalid, haka sukai tayi sai zuwa can yamma suka rabu Khalid yayi gida shi kuma Meer ya koma gidan nan da ya ajiye mutanen da yake kamawa,

Tunkan yaje ƙarasa gidan ya kira yaran Dady yace su haɗu dashi, sannan ya kuma kiran Sam yace su haɗu a can kuma su taho da Bossay, zaiyi musu wasu tambayoyi,

Bai daɗe da zuwa ba suma duk suka hallara a gidan, nan yayi musu duk wasu tambayoyin da zai musu kuma ya kuma ƙarin samun haske sosai akan binciken sa, daga nan ya sallame su shi da Sam da Bosaya suma suka fito, daman Sam da Bosaya tare suka zo a mota ɗaya da suka tashi tafiya sai yace su tafi kawai shima daman yana son zuwa can gidan gurin masoyiyyar sa, amma ba faɗa a fili ba,

Meer na shiri tafiya gida Khalid ya kirasa da daddaÉ—an labari yace masa yayi sauri yazo gidan ansamu inda Wayoyin nan suke, tare da wata akwati da amma arufe take sun kasa buÉ—e ta, saboda akwai password ajiki, harda wasu takaddu,

Meer yaji daɗin wannan maganar take ya juya kan motar sa ya nufi gidan tun kan ya ƙarasa ma yace masa dan Allah ya fito su haɗu a hanya ya karɓa yanzu dare yayi, zai dubasu idan ya koma gida,

Hakan kuwa sukayi a hanya suka haÉ—u yabasa komai, sannan shima yayi masa godiya suka rabu, da niyar gobe zasu haÉ—u, idan yasamu wani labari me daÉ—i....,

_____Suna ƙarasawa cikin masarautar, Sam ya ɗauka tare da Bossay zasu wuce part ɗin sa, sai yace masa shi ba part ɗin su zaije ba, yatafi kawai tunda ya kawosa yayi me wuyar, Sam kwa bai ƙara yi masa magana ba yayi gaba yabarsa  agun,

Shi kuma ya nufi Part É—in su Ameesha, da murnar sa yayi sallama cikin falon, Ameesha da Azeema dake zaune a falon suna cin abinci dan basu daÉ—e da shigowa ba daga makaranta ba akayi kira sallar magriba shiyasa suka bari saida sukayi wanka sukayi sallah sannan suka fito suke cin abinci, daman kuma su su kaÉ—ai ne a part É—in Dadda bata nan Papa kuma da Maama suna can cikin fada ana yin sallar magriba suka haÉ—u acan basu san me zasu tattauna ba, sude kaÉ—ai aka bari......

Azeema ce ta samu damar amsa masa sallamar sa, Ameesha kam cak ta tsaya da cin abincin da take,

Ƙarasa shigowa ciki yayi yana faɗaɗa fara'ar fuskar sa, tare da cewa Baby irin wannan kallon kamar baki taɓa ganina na ba, yana maganar yana ƙarasawa inda take agefen ta ya zauna,yana karɓar cokalin hannun ta da take cin abincin,

Da Mamaki Azeema ta shiga binsa da kallo tana rayawa a zuciyar ta, me yake hakan kamar besan da aure akan taba, ya zauna kusa da ita,

ÆŠebo abincin yayi zai kaisa bakin ta, tayi saurin É—an matsawa ta kawar da fuskan ta,

Azeema ce ta yunƙura daniyar yi masa magana, sai wayar ta ta soma ringing hakan yasata dakatawa tare da saurin ɗaukar wayar, ganin me kiran nata, yasa ta faɗaɗa murmushin tare da ɗaukar wayar ai tuni tama manta da maganar da zatayi, tana karawa akunne, ta wuce ɗakin su, tana cewa "Hello sweetheart..........,

Bossay ne ya ƙara miƙa mata abincin akaro na biyu, tare da cewa wai fushi akeyi dani ne tun ɗazu sai faman haɗe rai ake, agaya min abun da nayi yanzu indurƙusa har ƙasa innemi yafiyar Babyna, kinji ko,

Hankalin sane ya fara tashi ganin hawayen da suka fara sauko mata kan kuncin ta,

Subhanallahi Babyna me ya faru, dan Allah kigaya min me nayi miki,

Turo ɗan ƙaramin bakin ta tayi gaba tare da cewa "Tambaya tana kake yi kenan kai baka san me kayi min ba, yanzu duk yanda muke dakai ace maganar auren ka ta taso amma baka sanar dani ba, saidaga baya nake ji shima da ba afasa inajin bazan taɓa ji ba, Wallahi hakan beyi min daɗi ba, ka ƙona min rai,

Yanayin fuskar sa ne ya canza cike da damuwa yace "kinsan dai ba sonta nake ba shiyasa ba wanda nagaya da baki na duk wanda kikaga yasan da auren to badaga bakina yaji ba, Wallahi Babyna bana son wannan auren Dady ne ya matsa dole sai anyi sa, amma bada son raina ba, biyayya kawai zanyi, sai kuma gashi Allah ya dubi zuciyata dake banda rabon wahala akanta, Allah ya kawo min mafita a ranar da bantaɓa tunani ba, amma kiyi haƙuri idan hakan ya ɓata miki,

Shiru yayi yana jiran tayi magana amma sai yaga tama juyar da kanta gefe, tana cewa ai dan baka É—auke ni da muhimmanci bane, shiyasa kakasa gaya min, kuma yanda na É—auke ka kai ba haka ka É—auke ni ba, kuma ba wani maganar baka sonta da bansan ku tare bane sai kagaya min haka in yarda, dan Allah ka tashi katafi kaje tunda anfasa da ita ai zaka iya zuwa ka kuma kawo wata ka aura, ni meye ruwana a ciki,

Ɗan murmusawa yayi tare da ƙara matsawa kusa da ita sosai, dan ya rarrashi a barsa yasan ta da saurin fushi, yanzu duk wannan bayanin da yayi mata inba Sa'a ba bazata haƙura ba,

Cigaba yayi da cewa "Haba Babyna ki tausaya min shiyasa tun kan loƙaci ya ƙure min nazo gare ki dan in bayyana miki irin tsatstsan ƙaunar da nake yi miki, Khadijah wallahi ina sonki sosai so bana wasaba, nadaɗe da sonki, ni babu wata wacce nake so bayan ke ke kaɗai nake so kuma dake kaɗai zan iya rayuwa ki kasance uwar ƴaƴana,

Juyowa tayi tana binsa da wani irin kallo wanda yakasa tantance wane irin kallo take masa,.

Ji yayi gaban sa yayi wani irin bugawa, tsoran shi ɗaya kar tace masa bata sonsa, marairai ce fuska yayi kamar zaiyi kuka yace "dan Allah ki fahimci irin son da nake miki, naƙi gaya miki tun aloƙacin baya saboda karatunki shiyasa amma yanzu naji bazan iya haƙura ba shiyasa na yanke shawarar sanar dake yanzu, Dan Allah kice min kin amince zaki karɓi soyayya ta sannan kiyi min alƙawarin duk runtsi duk wuya zamu kasance tare bazaki taɓa bari na, wallahi idan ban aure kiba inajin kamar bazan iya ci gaba da rayuwa ba.......,

Kukan Ameesha ne ya fito fili hakan yasashi dakatawa da maganganun da yake mata, tunda yafara take zubar da hawaye, jin maganganun nasa sunyi yawa yasa kukan nata yaƙara ƙarfi, ita ba komai yafi saka ta kuka ba face yanda yake maganar tasan baida labarin auren da akayi mata, gashi takasa sanar dashi, dan batasan halin da kuma zata ƙara jefasa, shiyasa kawai take kuka, tare da tausayin kanta, itama dan itama ba ƙaramin so take masa ba dan har tanajin tama fi sonsa akan yanda yake cewa yana sonta, ita da sonshi ta taso tun bata kai haka ba, tun loƙacin da ta fara ganin sa take son sa, amma gashi ana ƙoƙarin rabasu, aikwa dole tasan abunyi a warware wannan auren ta auri wanda take so,

Yana tayi mata magana batajin sa harsaida ya riƙo hannun tayi saurin dawowa tare da saurin janye hannun ta daga nasa tana cigaba da kukan ta,

Gaba ɗaya hankalin sa yagama tashi yanzu ma kamar zaiyi kuka yace "Dan Allah kidai na kukan haka indai magana tace take saki zubar da hawaye wallahi nayi shiru bazan ƙara cewa komai ba kuma bazan miki dole ba idan bakyaso na shikenan zan haƙura, amma dan Allah kidai na kukan nan, wallahi har cikin raina nake jin sa bana so dan Allah kidaina, muci gaba da zaman mu kamar yanda muke kar ki sauya min dan Allah saboda nayi miki wannan maganar, najanye magana ta indai hakan zai faran ta miki rai,

maimakon tayi shiru saima ƙara volume da tayi,

Rasa inda zai tsoma ransa yayi, duk wani abu da zaiyi dan yaga tayi shiru amma taƙi yi, kuma taƙi yarda ya taɓata, kuma taƙi tashi, dan har ce mata yayi ta tashi ta tafi to amma sai ta maƙe masa kafaɗa, shide ya rasa yanda zai yi da ita,

Wani tunanine ya faɗo sai yayi saurin zaro wayar sa ya buɗe tare da shiga gallery ɗin sa, hotunan da yasa Ammi ta ɗaukar masa, folder su da ya ware ta musamman, ita ya shiga, hoton su da sukayi su biyu Abban Ameesha da mahaifiyar ta, shi ya shiga wai duk dan ya faranta mata yasan bata taɓa ganin taba,

Yana shiga yace Baby kinga mahaifayar ki, kamar ku É—aya,

Cak ta tsaya da kukan tare da saurin juyowa tana kallon sa, shi kuma ya nuna mata wayar, yana jinjina mata kai,

Tana ɗora idon ta akai tayi saurin fusge wayar daga hannun sa tana miƙewa tsaye, tama kasa magana kawai ta ƙurawa matar jiki ido ko ƙifatawa batayi,
Chapter 73 · 0% Book details