← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 103

Sashe 50

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

___Duk girman masallacin nan da É—umbun mutanen dake ciki, amma Saida wannan sanarwar ta isa kunnen kowa ana faÉ—a kuma gurin ya É—auki wani irin shiru É—if kake ji saboda abun yazo ba zato ba tsammani babu wanda yasan za ayi wani É—aurin aure,

Fitowar Meer da Khalid kenan daga cikin masallacin dan ko da akece a tsaya za ayi sanarwa yace bazai jiraba ya miƙe shima Khalid yabiyo bayan sa dan so yake yaje gurin Ameesha,

Saidai suna daf da shiga kunauwan su sukayi musu mugun ji, duk da Khalid baisan wacce aka daura auren da itaba amma jin sunan abokin sa yasa shi saurin juyowa a zabure yana kallon Meer da shima ƙamewar yayi,

Kallon kallo suka shiga yi a tsakanin su, Meer ne ya haÉ—iyi wani zafaffan yawu yaji ya haÉ—iye tare da jin wata faÉ—uwar gaba da saida tasa ya dafa jikin bango, yana shirin magana kenan Khalid ya rigasa da cewa, "Wai kaji kuwa abun da naji amma baka gaya min ba,

Tsaki Meer ya doka tare da cewa "naji mana ko ni kaÉ—ai ne Sameer zaka wani tsare ni da ido ko ji kurma ne, idan nine mai zai hana kaji ko kaga nayi maka kama da wanda za'a É—aurawa aure yanzu,

Cike da mamaki Khalid yace amma fa abun da mamaki gaskiya da alamar tambaya ya za'ayi ace komai naku iri É—aya taya hakan zata faru Sameer Sameer Sameer nidai kai ka É—ai nasani amma kuma itama yarinyar sunan mahaifinta da kakanta Sameer Sameer to wacece ita,

Wannan baya nin na Khalid shine yaƙara sa Sameer karkata wani tunanin tabbas da mamaki ace suna iri ɗaya kuma akusa da nan gashi kuma yarinyar ma, to amma abun tambayar shima da ta ɗaure masa kai wacece Khadija iya tunanin sa ya gano wace Khadijah yakasa ganowa, saurin kawar da tunanin yayi yasawa ransa bama shi bane saboda yasan ba tayanda za' ayi  hakan ta faru batare da sanin saba,

Juyawa yayi ya kalli Khalid da mamaki yagama kashewa gashi mutane har anfara fitowa wasu hannayen su ɗauke da goro da alawar daurin aure, wasu kuma na murmushi gashi yawancin mutane idan suka fito da fara'ar su idon wasu kuma akansu saidai babu wanda ya ƙaraso wajen su sai suga sunyi gaba mutane da yawa sun fito daga ciki ƴan waje kam daman wasu duk sun kama gaban su,

Meer ne yace"kaga idan kallon zaka tsaya ni inyi tafiya ta kasan dai bata yanda hakan zata faru za amin aure ne batare da sanina ba ko kuma akwai wanda ya isa yayi min auren dole ne,

Shiru Khalid yayi bai tanka masa ba har saida yaga Meer yayi gaba sannan yayi saurin binsa abaya zuciyar sa fal cike da mamaki saboda abun ba ƙaramin mamaki ya basa ba amma yaga shi Meer ko ajikin sa,

daman suna kusa da bakin gate ɗin saboda a ƙafa suka zo daman, dan haka saikawai suka shiga ciki, suna ƙarasawa gurin gate na biyu suka fara jiyo kiɗan ganga,

Shide Meer bai kawo komai ba, suka ƙara shiga, suna shiga suka fara bin mutanen gurin da kallo, ga mamakin su kuma sai kawai suka ga masu kiɗan nayowa wajen su tare da wasu mutanen, matsawa Meer yayi yabi ta gefe dan atunanin sa ko fita zasuyi amma yana yin gaba sai suka ƙara binsa abaya, cak ya tsaya yakasa ci gaba da tafiya jin abun da masu kiɗan suke cewa,

   "Takawar ka lafiya mijin sarauniya Khadijah takawar ka lafiya ɗan sarki jikan sarkin gobe sarkin mu na gobe Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon kwana Allah yasa kafi haka, Allah ya kawar da fitina acikin auren ku Allah ya kawar da sarrin mutane maƙiya da mahassada Allah ya tsare ku.....,

Wani maroƙi ya ɗora da "kaga na kadi angon kadi Allah yabar ƙauna mai ɗoreawa Allah ya kawo zuri'a tagari Allah ya kawo ƙazantar ɗaki da wuri, a haifo mana magaji...., Nan gurin ya ƙara kaurewa da ihu masu jiɗa suka ɗora daga inda suka tsaya anayi ana masa waƙar kirari,

Khalid da Meer yabari abaya ya ƙaraso gurin ta cikin mutane ya ratsa ya ƙarasa gaban Meer sai kawai ya tsinci kansa cikin farin ciki dan yagama karantar komai daga gani anyi hakane batare da sanin saba, hakan kwa ba ƙaramin daɗi yayi masa,

Ganin yanda Meer ya haɗe rai idon sa sun fara canza kala ya gama cika fal ƙiris yake jira ya fashe,

Khalid da yasan halin kayan sa sai yayi haƙuri ya tattara farin cikin sa ya ɓoye sa aràn sa yaje gurin sa, tun kan yayi magana ma, cikin wata iriyar murya da  shi kansa Khalid bai taɓa jinta ba daga gare sa duk da yasha yin ɓacin rai agaban sa amma bai taɓa ganin irin na yau ba,

Cikin daka musu tsawa da ɗaga murya Meer yace "YA ISAH!!  "ENOUGH!!! I told you that everyone should visit this place before I kill you all..!!! yafaɗa yana tattoshe kunnu wansa yayin da idanun sa suke a rufe,

Kowa Saida ya tsorata ɗif kake ji babu wanda ya ƙara koda motsi,

Shiru wajen yayi na ƴan loƙuta sai kawai Meer ya ƙara jin wani kiɗan, a fusace ya buɗe ida nun sa da suka koma kamar garwashin wuta ya sauke su akan su da tunanin sa basuji garga ɗin da yayi musu ba shine suka ci gaba,

Amma sai da ya buÉ—e idon sa sai yaji kiÉ—an badaga su bane ta bayan sane, da sauri ya juya dan ganin wane isasshen da mai ne yake kuma yin kiÉ—an bayan yace baya so,

Wasu dandazon mutanen ne suke tunkaro inda suke waÉ—an nan kuma harda mata suna ta guÉ—a dan mutanen yanzu ma sunfi na nan gurin yawa,

Baigama É—imaucewa ba saida yaga Maama ce akan gaba fuskar ta É—auke da wanni sanyayyen murmushi, tunda ta taho kuma idon ta akansa,

Kamar meson gano wani abun ajikin ta ko kuma wanda bai taɓa ganin taba haka shima ya kafe ta da idanu ko kaɗan baya ƙiftawa, har ta ƙaraso inda yake,

Wani murmushin ta ƙara saki ba yanzu har haƙoran ta ake ganowa loƙacin da tazo daf dashi tare da kamo hannun wansa tace ango kasha kasha ƙamshi ko baka sa turare ba ƙamshi kakeyi,

wani irin kallon tuhuma ya ringa binta dashi, jin abun da take cewa,

Maama sarai tasan halin da yake ciki kuma tagane kallon tuhumar da yake mata,

Meer na so yayi maganar amma ta maƙale saboda tsabar ruɗanin da yake ciki zuciyar sa neman daina aiki take,

Maama data gama karantar sa gudun kar ya tona musu asiri agaban mutane ya basu kunya yasa ta ƙara faɗaɗa fa'ar ta ta kamo hannun sa batare da ta bari sun ƙara haɗa ido ba, sai kawai taja hannun sa, ta hanasa damar magana,

Suna juyawa ta juyo ta kalli mutane ta sakar musu murmushi tare da kaÉ—a kai tace sauti mana....,

Nan take makiÉ—an suka fara kiÉ—an suka É—ora daga inda suka tsaya sunma manta da wani kashedun da yayi musu suka bi bayan su masu kiÉ—a nayi masu rawa nayi,

Maimakon Meer yaga sun tafi part ɗin Maama sai yaga sun nufi part ɗin Ummy, kamar wani ƙara min yaro haka yake bin momma abaya har suka ƙarasa cikin falon, suna shiga Meer yaga su ummy acikin falon,

Suna shiga Meer ya fusge hannun sa daga hannun Maama, tsayawa Maama tayi tana kallon sa,

Cikin ɓacin rai yana kallon Maama ido cikin ido yace "Maama wai me yake faru mai kuke nufi dani kuyi min bayani waye ya shirya hakan, me yasa zakuyi min ni zakuyiwa auren dole aure kamar ni, ni zakuyi wa batare da sanina ba mai nayi muku da na fuskanci wannan hukuncin Maama Ummy! Ku gaya min mai yasa!?

yayi maganar kamar zaiyi kuka, saboda ransa yakai ƙololuwar ɓaci,

Suma kansu saida suka sha jinin jikin su dan sun san ba'a kyauta masa ba yakamata a gaya masa koda bayaso ayi da haka,

"Kunyi shiru gaba É—ayan ku ina muku magana ku ban amsa Maama wace kucakar kuka aura min daman harda kwai wacce ta kai matsayin da zaku iya aura min ita acikin garin nan,

To wallahi kuyi gaggawar kunce wannan auren da kuka É—aura, idan na baku warware ba ni da kaina zan warware sa yanzun nan sai ku gayawa mutane kamar yanda kuka sanar da auren sai ku sanar da sakin koma wace jakar ce,

A zabure Maama ta ɗago tana kallon sa cikin tashin hankali tace "dan Allah kar kayi haka na roƙe ka kar kabari mutun cin mu yazube a cikin mutane mun san bamu kyauta maka ba amma nasan hakanne kawai mafita bamu da wata hanayar da ta wuce wannan ina mai baka haƙuri akan yin hakan batare da sanin ka ba amma dan Allah karka sake furta kalmar zaka sake ta dan Allah, ta ƙarasa maganar cike da raunin murya, dan muryar har karkarwa take tasan ayanda ya ɗauki abun da zafi zai iya yin komai ma, ga bata da iko dashi bare ta dakatar da shi ta hanyar tsoratar wa,

Juyawa tayi tana kallon Ummy da itama ranta baiyi mata daÉ—i saboda ko ita ba agayawa ba saida aka É—aura, ita ba haÉ—in auren ne yabata haushi ba, kawai rashin sanar da itan da ba ayi ba tun farko, amma zuwa yanzu dake tana da saurin fahimta ta sauko, saidai bata da bakin da zatayi masa magana tasan daman hakan zai faru fiye da hakan na zai iya aikatawa shiyasa tayi shiru,

Maama ce tace "Ummu Kulsum (ummy) kiyi masa magana kar ya furta abun da yake shirin yi,
Chapter 50 · 0% Book details