← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 103

Sashe 36

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nidai ba kowa bane illa É—aya daga cikin bayin gidan nan, ni É—an mai gadin gidan nanne tun shekarun baya bayan mutuwar sa kuma sai nafara aiki tun kafin tsohon sarki ya hau mulki, bayan ya hau ne, wata rana ina zaune a bakin gate sai akace min UWAR BIYU (sunan da suke kiran ta dashi kenan abaya can) na kirana da sauri na tashi naje, har É—aki aka jani na shiga,

Bayan shiga nagansu su su biyu na tsugguna na gaida su daga nan kuma sai UWAR BIYU take cemin wani aiki zata sakani akai indai har zanyi to bani da matsalar komai bazan ƙara neman abu in rasa ba daga ƙarshe kuma idan kaomai ya tafi daidai za a sallame ni daga masarautar tare da kuɗaɗe masu yawa inje inyi rayuwata a duk ƙasar da nake so, ina jin haka banma ji wane aiki bane kawai nace na yarda zanyi ko wane irin aiki ne, shine tace "aikin da zanyi musu shine duk wanda zai fita daga cikin gidan ko kuma yashiga babu ruwana koda antambaye ni kar nasake nace nasan wani abun, nace na yarda zanyi, daga nan suka sallame ni,

Tun ina ganin abubuwa da yawa har abun naga yayi yawa sai na fara bincike saidaga baya nagano ashe so suke mulkin yadawo hannun su shiyasa suka fitar da gimbiya da iyalanta, da na nuna zan tona asiri shine suka ƙara bani ƙwarin gwiwa sannan nadawo cikin su komai muka fara yi tare,

Itadai UWAR 2 da farko tana da nata ƙudirin akan Papa da bansan dalilin ba, abundai da nasani shine anaso masarautar ta lalace ta ta zama kawai mugunta ake acikin ta bama aso ɗaya daga cikin jinin Sarki Muhammad yayi sarauta, sarauta zata bar asalin gidan za a ɗauko wani daban a ɗora shi, yayi mulkin rashin gaskiya idan akayi hakan shikenan burin ta zai cika, idan mukayi nata haka zata sallami kowa,

Bayan wannan loƙacin da muka rasa ta yanda zamu bi a ɗora wani daba jinin gidan ba, sai kawai mukaje wajen boka muka gaya masa buƙatun mu, shine yabamu tabbacin saidai muje mu samu ɗayar matar da ta yarda ayi cikin ƙarya sai a rufewa kowa baki idan loƙacin haihuwa yayi sai aje asibiti a samo ɗan, idan yaso in ya girma sai yazama sarki,

Da haka muka baro wajen da muka dawo kuma sai tace zamu nemo wacce zataje gurin Fulani tayi mata zancen dan ba aso tagane mune, shine mukabi ta hanyar ƙawarta Hajiya Sarah itama muka biyata shine taje.....daga nan yabasu labarin da su Hajiya Sarah suka bayar kwanaki ta yanda suka samo Salahudeen har yazama sarkin daga nan kuma akasa ka musu mugunta da zalunci a zuciyoyin su ta hanyar asiri da akayi musu sannan kuma akace Fulani ta ringa kai kuɗi cikin ɗakin anan idan takai ta ajiye kuma sai musa jakadiyar ta taje ta kwaso kuɗin takawo mana,

Ana cikin haka kuma komai yana tafiya yanda yakamata, to bamu san ya akai waziri yagano ba, sai yayi mana barazana akan zai tona mata asiri sai loƙacin ta shiga tashin hankali taringa basa haƙuri tana so tasan hanyar da zata kauda shi, sai kawai yace zai rufa mata asiri amma shima yana da nasa ƙudurin akan sarki idan ta yarda kuma zata basa haɗin kai burin sa ya cika shima to zai rufa mata asiri,

Ta tambaye sa maiye nasa ƙudurin shine yace mata, yana so ɗansa yazama sarki, akori su fulani daga cikin gidan a ɗora ɗan sa(baban Sam) akan mulkin sarautar ta dawo hannun su, indai akai haka babu wata matsala da zata faru dan yayiwa ɗan sa alƙawarin zama sarki tunda suka gano Salahudeen ba ɗan masarauta bane, daman da nasu ƙuddurin akai sun rasa ga inda zasu fara ne sai kuma ga dama ta same su, shiyasa sukayi amfani da ita dan ganin cikar nasu burin,

Sai tace "masa hakan ai bazai taɓa yiyuwa ba amma dai akwai wata hanayar bazata ɗora ɗansa akan mulki ba saidai ɗansa shima kuma da sharaɗi zai auri ƴar ƙanwar ta, (ƴar hajjaju) inyaso Sarautar zata dawo hannun su gaba ɗayan su saboda gimbiya Sabreen baza ta sake dawowa ba ta tafi har abada dan haka shikuma jinin Muhammad (papa) bazai taɓa ci gaba da mulki ba,

Shima sai ya yarda da hakan, da tsarin shekarun murabu sa ɗin sarki Salahudeen nayi idan suka sauke sa zasu ɗora Sameer akai(Sam) tare da matar sa ƴar gidan Hajjaju,(ina fatan kun fahimci inda zancen ya dosa, dalilin da yasa ake so ahaɗa Sam da ƴar hajjaju aure, saboda shine Sarkin gaba kuma ta hakan aka ƙara samun haɗin kan sauran duk suka Amince daga baban Sam ɗin har ita hajjajun)

Sai gashi abu yana daf da cika burin kowa zai cika sai kuma muka tashi da karyewar asirin da duk mukayi acikin gidan nan loƙacin hankalin mu yatashi ganin faruwar hakan, saboda boka yabamu tabbacin duk ranar da jinin gimbiya yataka cikin gidan da ƙafar sa to ranar komai zai karye, saidai kuma nisan yanda zamuyi, to shine ranar da abun yafaru muka fara bincike acikin gidan dan gano wanda ya shigo cikin gidan anan mukayi tozali da wata yarinya mai kama da gimbiya sak, nan muka tabbatar da itace jinin ta, dan haka sai muka saka Abdallah ya ringa ganin duk wani takunta har muka ci sa'a suka fita shopping shine nida Abdallah muka bi bayan su har loƙacin da suka ƙarasa inda zasu, sai muka ƙara kiran wasu yaran mu masu yi mana aiki suka ɗauko ta, suka kawo ta cikin masarauta,

Mukuma muka shiga gurin muka gana da manajan gurin muka bashi kuÉ—i mai yawa ya goge duk wata É—auka sannan muka hanasa faÉ—awa kowa idan anzo yin bincike,
Daga nan bamu ƙara ganin yarinyar ba, da muka tambaye ta sai tace taje taga yarinyar kuma tasa a fita da ita daga cikin gidan aje akashe ta, wataƙil ma ankashe tan, tunda ga nan muka ƙara kwantar da hankalin mu sannan muka fara tunanin samo wata mafitar bamu samu ba kuma ashirin Fulani ya tonu Hajiya Sarah ta tona mana asiri dan mu ta tonawa ba Fulani ba tunda ita bata san komai ba kawai muna amfani da itane ta yanda koda wani abun zargi yafaru ita za akama, ba wanda zai zargi Ammah,
nan Æ´akarasa musu labarin har zuwa ranar yau da suke zaune agaban su.......,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

     
     'shiru fadar ta ɗauka kowa da mamaki yake kallon Ammah da ta durƙufar dakai,

Babu wanda yasamu damar yin magana saboda al'ajabi yagama kashe su,

Meer da ya nuna É—ayar baiwar yace "saura ke ke kuma nawa akace za abaki, wane aiki kike mata,

batare da ta É—ago ta kalli kowa ba ta jawo mayafin ta ta rufe fuskar ta sannan tace "nima kuÉ—......., Meer ne ya dakatar da ita tare da daka mata tsawa yace ta buÉ—e fuskar ta sannan ta É—ago ta kalli kowa, kowa ya kalle ta,

Cike da jin kunya ta ɗago da kanta, tana ɗan ƙifƙifta ido tana kallon wani wajen daban, sannan taci gaba da cewa, ni matar ƙanin tace kuma wallahi duk abun da nake bada son raina bane tirsasani akeyi tunda mijina na ya mutu suka koreni daga tasu masarautar tare da yarana saboda suna tunanin wai ni na kasheshi hakabnuke zaune cikin wani hali ni da yara na saboda ni marainiyace auren ma da ƙyar suka bari akayi dande yanaso shiyasa suka bari akayi da ƙyar shima kuma tunda mukayi nake fuskantar abubuwa har Allah ya ɗauki ransa amma sai akace nice shiyasa suka koreni,

Ina cikin wannan halin watarana tazo har gidan da nake ta kawo min tayin aiki acikin gidan nan nayi mamaki jin tayin aikin da ta kawo min awata Masarautar da bata su ba kuma itama ba acikin ta take ba, da na tambaye ta dalili sai tace zata gaya min amma ba yanzu ba, yanzu tana so inshiga gidan in fara aiki zata nema min hanya kuma idan nashiga aiki zanyi mata, zata biyani kuɗi masu yawan gaske nikuma ganin babu abun da nake bana sana'a kuma bansamu wani mijin ba ga kuma halin da nake cikin na ƙuncin rayuwa sai kawai na amince mata duk da banji wane irin aiki zanyi mata ba na yarda da haka,

Ko sati ɗaya ba ayi ba na shirya komai ƴaƴa na kuma daman duk maza ne susu biyu sai tace zata sa a kula dasu, ahaka muka rabu dasu ta turo ni gidan tare da wani namiji tace angama komai aiki kawai zan fara duk inda aka bani inkarɓa zamuyi magana daga baya  nace mata to, daga nan nazo nafara aiki a sashen  Fulani nake da zuciya ɗaya nake zaune da ita tsakanina da Allah,

to saidaga baya kuma loƙacin da gimbiya tana da ciki wanda ita kanta gimbiyar batasan tana dashi ba saboda a loƙacin gaskiya banji ana cewa tana da ciki ba amma bansan ya akai ita tasan dashi ba, nayi mamaki sosai amma ban nuna mata hakan ba, sai SA'ADATU ta kira ni awaya ta neme ni tace ince zanje gida mahaifiya ta batada lafiya, haka kuwa mukayi na shirya naje na sameta a gida,
Chapter 36 · 0% Book details