← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 103

Sashe 95

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har lumshe ido yake loƙacin da ta juya baya yabi bombom ɗin ta da kallo, yaga yanda suke yawo ta cikin hijab ɗin ji yake kamar suna jansa, har saida ta wuce ciki sannan ya daina kallon ta, daurewa kawai yayi ya tashi ya shiga wankan.....

Koda Ameesha ta gama shiryawa kasa fitowa tayi daga gurin saida ta loƙa taga baya nan sai tayi sauri ta fita, dabarar neman muƙullin ta shiga yi,

Wajen tasa wardrobe É—in taje ta fara bubbuÉ—e su tana dubawa amma bata gansa ba, É—akin taci gaba da duddubawa,

Rasa inda ta ya ajiye tayi kamar ance mata ta É—aga filon kujerar dake É—akin tana É—agawa ta gansa cike da murna takai hannun zata É—auka taji anriga ta É—aukewa,

"Kassh ta faÉ—a tana dafe goshin ta, cike da jin haushin rashin dubawar da batayi ba tun farko, da tuni ta É—auka ta fita,

"Haka mukayi dake farautar sa kike daman, kasa É—augowa tayi ta kalle sa, saboda taji kunyar ka matan da yayi, ga kuma yanayin da yake daman bazata iya kallon sa ba,daga shi sai towel,

Hannu yasa zai É—ago fuskar ta tayi saurin matsawa baya,

"Hmmm kawai yace sannan ya nufi wajen drawer É—in sa, jallabiya kawai ya É—auka yasaka,

Sannan ya É—auko prayer mat ya shimfiÉ—a musu, sannan ya hau, yace "kizo muyi sallah,

Daman tayi alawala sai kawai ta taho, sallar isha'i yafara jansu sannan ya ɗora da nafila bayan sunyi, yace ta matso gaba, ƙin motsawa tayi da farko Saida ya haɗe rai zai nuna mata asalin kalar sa da tafi sanin sa da ita, sannan tayi saurin matsowa, dafa kanta yayi kamar yanda yake a musilin ce yayi mata addu'o'i sannan ya ɗora mata sa wasu tambayoyin, tana ta kunbure kunbure da turo baki da haka take basa amsa har suka gama,

ÆŠan satar kallon sa tayi taga dai har yanzu ransa a haÉ—e kamar de yanda tasan shi ada haka ya koma yanzu badan bama da tace yaso yafi daÉ—in, tana mamakin sa, mutum sai kace me aljanu kamar bashine É—azu ba,

A bincin ya jawo musu a gaban ya ajiye su sannan ya buɗe ledar take away ɗin yafara buɗewa me ɗauke da fried rice da take ƙamshi, sai ya buɗe wata ledar me ɗauke da banƙararrun kaji, ɗauka yayi ya ɗora akan abincin sannan ya ɗauko holondia ya zuba shi a cikin cups ɗin, sannan ya tura mata su gaban ta, ko uffan baice mata ba,

Itama kuma bata É—auko ba kuma bata ce komai ba,

Wayar sa ya ɗauka ya shiga daddanawa, wajen 5 minutes sannan ya ajiye wayar tare da ƙara kashe ta gaba ɗaya, sannan ya ɗago ya kalle ta, yana ɗagowa kuma suka haɗa ido, arashin sani itama ɗagowar ta kenan da niyar taga me yake sai kuma suka baɗa ido dashi, sai tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, saboda wani banzan kallo da ya watsa mata loƙacin da suka haɗa idon,

Cike da muryar isa da taƙama irin dai tasa ta asali, yace "baki ga abun da na ajiye miki bane ko so kike sai na ƙara maimaita niki, to wallahi kar ki bari naƙara maimai ta miki, ki ɗauka ki cinye gaba ɗaya sannan kicire wannan hijab ɗin kafin ki fara ci, nagama magana yana faɗar haka ya tashi daga gurin ya koma kan kujerar kusa da ita,

ya sake haɗe rai, badan tana so ba haka ta cire hijabin daman wasu riga da wando ne ajikin suma kuma masu kwauri ne wandon har ƙasa yake,

Inda Allah ya taimake tama, tana jin yunwa da batasan ya zatayi ba, cokalin ta É—auka tafara cin abincin, ba laifi ta É—anci da yawa duk dade bata cinye duka ba, kazar ma ta É—an ci kaÉ—an,

Tana gamawa itama bata ce komai ba ta ture abincin gefe,

Jinjina kai yayi sannan ya sauko yana cewa ko kefa yafaɗa yanzu kuma cikin sakin fuskar sa, yana sane yayi mata haka yasan da lallaɓata yayi baza taci ba taurin kai zata tsaya yi masa,

guntun nata ya ɗauka ya hau ci, tas ya ƙarasa shi sannan ya miƙe, daga gurin banɗaki ya shiga ya wanko bakin sa sannan ya fito,

Kusa da ita ya dawo ya zauna, yana naɗe ƙafar sa, sannan yace "Lily taso muje mu kwanta bacci nake ji, kema naga alamar kamar baccin kikeji ko,

Ta ƙasan ido ta kalle sa ita yanzu abun nasa tsoro tsoro mamaki mamaki, takasa gane kansa, ji yanda yake magana kamar bai taɓa yin faɗa ba ko jin haushi,

jin tayi shiru yasa ya miƙe daga gurin tare da kamo hannun ta ya miƙar da ita tsaye, sannan yaja ta har kan gadon kasa zama tayi, dan bazata iya kwanciya guri ɗaya dashi ba,

Please ki kwanta ni ba abun da zanyi miki inma kina tunanin wani abun, magana zamuyi,

Saida taji hakan sannan ta zauna, sai yace kwanciya zakiyi ba zama ba,

A hankali tace idan na kwanta a ina kai zaka kwanta,

"A sama, yabata amsa cike da gatse,

Shiru kawai tayi ta kwanta, sannan yaja mata blanket yazagaya É—ayan gefen ya kwanta a kusa da ita baya,

"Ki juyo nan,

Maƙe kafaɗa tayi tare da cewa "ba kyau haɗa numfashi,

"Ok to ni bari in matso, yana faÉ—a ya matsa kusa da ita tare da saka hannu ya jawota jikin sa sosai,

Tana jinsa tayi masa shiru batayi yunƙurin hanasa ba yanzu,

"Lily ya kirata a hankali,

"Wai baka san sunan bane me yasa kake kirana da wannan sunan?

A bun da yafaÉ—a mata a kwanakin baya ko ince a shekararun baya, shi ya kuma maimai ta mata yanzu ma,

Sauke wata nauyayyir ajiyar numfashi Ameesha ta sauke sannan tace "kaine kenan a loƙacin baya kake turo min saƙo sannan kake kirana awaya ko?

"Of course, yabata amsa,

ÆŠan juyowa tayi kaÉ—an tana kallon sa,

Lumshe idon sa yayi tare da ƙara buɗe su duk a loƙaci ɗaya,

"Why?

Because kinshigo rayuwa ta a loƙacin da banshirya hakan, ba, yau zangaya miki duk abun dake raina, kuma kema ina son kigaya min baki ra'ayin, kinsan halina kuma kinsan ko waye ni kinsan abun da zan iya kinsan abun da bazan iya ba,

A shekara huɗu baya ba haka halina yake ba amma shigowar ki rayuwata hakan yasa na canza hali gaba ɗaya ni kaina har mamakin kaina nake yanda akai na sauya loƙaci ɗaya, ada bana son mace banga abun so ajikin taba banga me zaisa inzubar da ajina agun mace ba, mata kwata kwata basa gabana kuma bana tunanin su ko kaɗan, ni kaina ina mamakin yanda banjin komai game da mace bansan me akejiba, bansan meye felling ba, kodan bana sawa raina hakan ban saniba, a wata rana kwatsam na fara mafarki a kanki ke kaɗai nake gani indai zanyi mafarkin kuma shima bawai normal mafarki ba, saidai inyi munayin wani abun....

Shiru yayi saboda yanda yaga ta juyo da sauri ta kalle sa,

Ciga ba yayi da cewa "kina mamaki ne, of course mafarkin da nake na kudanci ne tsakanina dake, abun mamaki kuma tun amafarkin nafara jin daɗi sai inji inmuna tare banson in tashi daga mafarkin, kuma kullum na tashi da abun nake ganinki, ana haka kuma yawan tunanin abun yasa nafara jin ciwon mara, ranar da na fara kuma ranar kika shigo ɗakin nan, da na ganki kuma sai ciwon ya ƙaru, sai na ringajin kamar a mafarkin shiyasa nayi miki wannan abun har abu yaji haushi yasa ya yanke hukuncin haɗa auren mu,

Bazan ɓoye miki ba a loƙacin ji nayi kaf duniya babu wacce nafi tsana sama dake, shiyasa zakiga ina tayi miki wasu abubuwan da baki jin daɗin su, amma kuma da na kwanta zanyi mafarkin da nasaba.......

Loƙacin da na fara jin kinwanta min, tun loƙacin da kika kwanta a falo na mayar dake ɗaki na, daga nan kuma sai nafara tunanin abun dake faruwa a mafarki, hakan yasa nafara tausayin ki harna baki magani, da kikayi bacci kuma kikaƙara sanya min ciwon mara hakan yasa na fara yi miki wasu abubuwan, ana naji daɗin ma yafi wanda nake ji a mafarki, a haka nakasa haƙuri har kika farka kika sameni...

To tundaga wannan rana na fara tunanin ki har takai ta kawo hakan nan nakanji ina son ganin ki, ke kuma saima kika dawo ƴar ɓuya dani ganin ki na min wahala,

Abun yaɗan fara ban mamaki yana sani yawan tunani, sai na samu Khalid nake gaya masa abun dake faruwa dani, sai yace ai sonki na farayi nikuma na ƙaryata hakan har faɗa mukaso muyi, to banyar da da hakan ba har sai ranar da wannan yaron yazo, kika ringa wasu abubuwa anan naji zuciya ta kamar zata fashe shiyasa ma nabar ƙasar, ni da kaina nace anema muku makarantar ku a Abuja saboda in ringa sa ido akan duk wata shige da ficen ki, batare da sanin kowa ba,

A loƙacin ne nake aiko miki da saƙonni na duk dan ingwada hankalin ki da ace kin amince da tuni na rabu dake dan bazan iya zama da mace da tana da aure akan ta amma hakan bai hanata kula wasu ba,

Khalid na kira yaje har can muka yi magana dashi ta fahimta, anan duk ya ganar dani abubuwa da dama, duk tsawon loƙacin da na ɗauka na ɓata sane wajen koyon a bubuwa da yawa saboda bansan wasu abubuwan ba, na koyawa kai na haƙuri da rage zafin zuciya, dan har wani malami na samu yaban addu'ar da zata sanya min sanyin zuciya in rage abun da nake game da mata, nashiga gurare da yawa wajen gano yanda ake komai kuma ake gudanar da rayuwa, Khalid ma ya taimaka min sosai wajen ɗorani a hanya, shi yace inbarki har sai kingama karatu kin ƙara girma, daga nan kuma sai in fara nuna miki abun dake raina, Lily nasha wuya a kanki wallahi ban taɓa tunanin rayuwa ta zata dawo haka ba, sai gashi na canza kamar bani ba,

Kuma ba kowa ya canza ni ba sai ke, duk kece silar komai saboda daÉ—in da nake ji idan.......,

Ya ƙarasa maganar yana ɗan mintsinin ta a ciki,
Chapter 95 · 0% Book details