Sashe 84
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaye suka hangota an saƙale ta ajikin bango an raba hannuwan ta an daure su ajikin wani ƙarfe, ƙafafunta kuma anɗaure su da sarƙar ƙarfe, kanta ya lanƙwasa yayi ƙasa kamar ma ba rai a tattare da ita,
Da gudu Abban Ameesha ya nufi wajen ta, yana zuwa ya ruƙota yana kiran sunan ta, suma duk ƙara sa shigowa sukayi, da sauri suka shiga kunce mata daurin da akayi mata, na hannu suka fara kuncewa sai kuwa ta faɗa kan Abban Ameesha saboda daman ɗaurin ya riƙeta batakai ga faduwa ba,
Riƙeta yayi sosai hawaye na ciko masa idanu, saida suka kunce mata na ƙafar, shi dake sarƙa ce har tayi mata shati a ƙafa,
da taimakon Meer suka kamata suka kwantar da ita ƙasa, dubata suka shiga yi amma kamar bata numfashi, can de Sam ya kuma dubata sannan yace zuciyar ta na ɗan harbawa, muyi sauri mukaita asibiti zata iya rasa ranta nan da wani loƙaci,
Cikin sauri duk irin girman ta haka Meer ya ɗaga ta da ƙyar sannan ya fito daga ɗakin suna biye dashi a bayan sa, har suka ƙaraso wajen motar Abban Ameesha yayi saurin buɗe mishi yasaka ta a cikin,
Wanda yake biye dasu ne yayi musu kwatancen inda babban asibitin su yake, shi ya fara gaba su kuma suka bi bayan su, inda Allah ya taimaka ma babu wani nisa, suna zuwa kuma likitoci suka hau kanta aka fara bata taimakon gaggawa,
Abban Ameesha ji yake kamar basa aikin su yanda yakamata, kamar ta yabuÉ—e ya shiga haka yake ji,
Sunkai wajen 30 minutes amma basu fito su Meer duk sunƙagaru suji ya ake ciki, sadaga bisani can sannan wani likita ya fito, yace "Alahamdulillah munsamu ta farfaɗo da ƙyar yanzu de tana buƙatar hutu sosai, dan yanayin da ta samu kanta harda na rashin bacci da kuma wuya, amma dai yanzu normal idan ta farfaɗo zaku iya shiga, yana gama faɗa musu haka yayi gaba,
Gaba É—ayan su babu wanda bai sauke ajiyar zuciya ba tare da furta alahamdulillah a ransa, Abban Ameesha kam harda kukan farin ciki,
Haka suka ci gaba da zama a asibitin sallah ce kawai take fita dasu, bawan Allahn da suke tare yayi yayi suzo yakaisu masarauta suci abin ci saboda ansan da zuwan su amma sukace baza su ba, saida daga baya de da sukaga zaman bana ƙare bane, sai suka ce yasa akawo musu nan suci anan,
Suna faɗa masa ya kira gidan ya faɗa musu, kan kace me har ankawo musu abinciccika lodi lodi, kala kala, fitowa sukayi waje a harabar asibitin suka zauna, masu ci suka fara ci Meer da Abban Ameesha sukace sun ƙoshi, amma Saida sukayi wa Abban Ameesha dole yaci,dan sun san dole yana jin yunwar shiyasa suka sa shi yaci,
Dadda de ba ita ta farfaɗo ba sa cikin dare, wajen ƙarfe biyu, dan haka dole suka kwana agarin kuma ba a kwana a asibitin dan haka babu yanda suka iya suka tafi can masarautar suka kwanta,
Da safe suka dawo wajen ta, suna shigowa É—akin suka ganta kwance ta É—aga kai sama alamun dai tunani take,
Har suka ƙarasa gurin batasan da shigowar su, Bossay ne yace "Dadda yafaɗa da ɗan ƙarfi.
dawo da hankalin ta tayi gare sa tana kallon sa,
Abban Ameesha ne da yaga har yanzu bata ankare dashi ba, yasa shi cewa "Umma,
Sauran maida kallon ta tayi ga inda taji sautin muryar sa dan ko a mafarki taji muryar sa zata gane sa, idon na sauka akan sa taga de da gaske shine, da sauri ta miƙe zaune tana kallon sa cike da mamakin ganin sa,
Matsowa yayi kusa da ita sosai sannan yace "umma ya jikin naki,
Dadda ta rasa wane irin yanayi ta tsinci kanta, har yanzu bata gama yarda da abun da take gani ba,
SAMEER..!!!
ta kira sunan sa, ganin tana kamar ta shiga ruÉ—ani, yasa Abban Ameesha saurin yi mata bayanin wani abun,
Me Dadda zatayi inba kuka ba, nan ta shiga rera kuka, da ƙyar suka samu tayi shiru har ta fara nuna tsatstsan farin cikin da ta tsinci kanta,
Duk guri suka samu suka zauna, tun aloƙacin duk suka kwashi komai suka bata labarin duk abun da yafaru da bata nan tundaga farko har ƙarshe, wasu tayi farin ciki wasu tayi kuka wasu kuma tayi dariya, itama ta basu labarin baƙar wuyar da taci,
Godiya tayi musu gaba É—ayan su dan kowa ya taimake ta arayuwa duk sun bada gudun mawa ta ko wane fanni,
Daman taji sauƙi dan haka suka nemi sallama, daga nan suka tattara insu insu suka ɗauki hanyar kano, nan ma suna tafiya suna hira, Dadda akwai surutu wuya bata hana ta magana, sai gashi kamar ba ita ba, sai zance suke da Abban Ameesha,
Wajejen ƙarfe huɗu suka sauka, a kano, daman ba motar su ɗaya da Meer ba da suka zo wata hanya shi da Sam ne a mota ɗaya, sai kawai sukayi wata hanyar dan yafiso yayi suprise ɗinsu, shiyasa duk wannan abun da ake baice komai ba akan su,
Tafiya kaɗan ta kawo su, cikin masarautar, bayan sunyi parkin, Abban Ameesha ne ya fara fitowa sannan ya yasa hannu ya fito da Dadda, tare suka jera, Dadda gidan ta ringa kallo sai ta tuna loƙacin da ta fara shigowa neman shalelen ta, tana ta kallon gidan har suka ƙarasa part ɗin su Maama, da sallama suka shiga, ciki, babu kowa a cikin falon dan haka suna shiga, Abban Ameesha yaɗan ɗaga murya yace Maama Papa gamu mun dawo ku fito kugan ta,
Dariya Dadda tayi tace "kai ya zaka fara kira min wasu al'umman daban, to ba wanda zangani, jikalle kawai nake son gani ba wasu tsaffi ba, da bansan dasu ba,
Bossay da ya shigo yanzu yaji abun da take cewa yace "Ke kuma gajen haƙuri to ai jikar taki bata nan kamar kura ta cinye ta, kwanaki da wasu maza suka fita da ita ai basu dawo da ita ba, dan haka sai kalli waɗanda ba kyaso ɗin ko kuma mu mayar da ke inda muka ɗauko ki, in bazaki iyayiwa mutane shiru ba, ke bakin ki kullum haya haya,
"Yo inajin dai ba da bakin Aminatu nake suruntun ba, kuma bakai ka dawo dani kaida a tunanin ka idan takaine zan yarda indawo ai da inbiyo ka mu dawo gwanda inmargaya, dan haka kaja bakin ka kamin shiru kaga nifa karka ƙara yi min magana, ina farin ciki baza ɓatan raiba, kuma bakin ka ya sari ɗanyen kashi na me jego mutuwa saidai kaga anayin ta agidan ku amma ba anan ba, saidai idan gyatumar ka kurar tacinye, kaji mu da ɗan banzan yaro watakon har yanzu baka canja hali ba to wallahi ka fita daga idona tun kan na zubawa idon barkono,
Bossay zaiyi magana, Abban Ameesha yayi saurin cewa Dadda ki kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa ya ɓata miki rai rabu dashi, jikar ki ta nan babu abun da yasame ta lafiyar ta ƙalau, wataƙil suna makaranta shiyasa baki gansu anan ba, amma nasan suna kan hanya, yanzu zasu shigo,
"Allah Abba itace da wata magana matar nan fa ba'a iya mata maimakon tayi shiru ta jira anuna mata komai amma sai tayi gaba gaɗi, nifa dama anbarta ta lulu mutum ya tsufa sai ƙin mutuwa,
"Kai kai wallahi ka kiyaye ni kaga zo ka fita daga gurin nan,daman haka kake bantaɓa sani ba, to wallahi akanta zamu ɓata da kai, zo ka fita, cewar Abban A,
Dadda harara ta watsawa Bossay tace "ai indai wannan ne kaɗan ma kagani, wallahi kaf duniyar nan babu yaron da ya raina ni irinsa, duk maganar da yaga dama gayan yake saboda bashi da ta ido wallahi kaide bakayi gadon arziƙi ba irin na ƴan uwanka, wai me yasa ma kake cigaba da bibiyata, ka fita harkata tunkan jikinka yagaya maka, dan zansa wannan basumuden ya karkarya min kai,
"Ah ah Oyo Oyo suka jiyo muryar Maama tana faɗa tana faɗaɗa murmushin ta, ta ƙaraso gurin, sannu ku da zuwa kunsha tafiya, sai yau tun jiya muke zuba idon ganin ku,
Murmushi Abban Ameesha yayi yace wallahi bamu samu damar dawo wa jiya ba, sai yau ta samu lafiya,
Itama Dadda sakin fuskar tata tayi sannan suka gaisa, tare da komawa kan kujeru suka zazzauna,
Dadda de duk a ƙage take ta ga shalelen ta dan haka ta kasa haƙuri tace "wai ni sai yaushe zata dawo ne nifa in ba yanzu zata dawo ba ku kaini inda take ni inje inganta, dan wallahi ita kaɗe nake son gani,
Maama ce tace "ai yanzu hakama suna kusa da gida yanzu zaki gans......., Shiru tayi sakamakon maganar su da tajiyo, sai tace to kinji suma sun dawo,
Da sallama Azeema da Ameesha suka shigo cikin falon,
Dadda ce ta riga kowa amsawa da "wa'alaikissalam shalele na,
Cikin mamakin ganin ta da zaro ido Ameesha tace DADDA..!!!!
itama Daddar meƙiwa tsaye tayi tace "shalele na, ina kika tsaya ne tunɗazu na dawo nake jiran ki,
Da gudu Ameesha ta kwasa tare da yin cilli da duk wani abu dake hannu ta, ta tafi gurin Dadda tana zuwa ta faɗa jikin ta, Dadda saboda murna da farin cikin ganin ta, bata san loƙacin da tayi sama da Ameesha ba, ko nauyi bata jiba, harda suyin juyi da ita,
Sannan ta sauke ta, nan suka shiga sauke nufashi, Ameesha tace DADDA nayi missing ɗin ki irin over ɗin nan, gaba ɗaya duniyar bata min daɗi da ba kyanan babu wanda yake kula dani kowa baya sona kamar ke har auren......., Sauri tayi ta rufe bakin ta bata ƙarasa ba, idon ta ta mayar kan Bossay sai taga yana kallon waya wata ɓoyayyir ajiyar zuciya ta sauke da Allah yasa bata ƙarasa ba,
Sadda kam itama zayyano mata yanda tayi kewar ta ta shiga yi, kuma batayi tunanin komai ba akan maganar auren da tace,
Azeema ma ƙarasowa tayi suka gaisa da Dadda cike da farin cikin ganin juna, nan suka rikice da zance wannan yace wannan, wannan yace waccen ko gajiya da surutu basayi, kowa kaga fuskar sa ɗauke take da farin ciki da annuri marar misaltuwa......,
________MEER