← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 103

Sashe 68

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannuwan sa duka biyu yasa ya dafe kansa, ji yayi kamar ya rusa ihun taƙaici da baƙin ciki haka yake ji, a fili baisan loƙacin da ya shiga furta kalmar Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un yayi takai wajen sau uku, a zuciyar sa kuma yana tunanin anya kuwa shine ba aljanu bane suka shige da ko kuma wani abun aka bashi ya sha da yayi wannan abun, shi yakama taɓa mace da matsayin sa da komai, macen ma kuma ƙanwar sa, wacce yakewa kallon yarinya amma da ita ya kwanta guri ɗaya yana taɓata, wannan wacce irin mummunar rana ce agare sa, yanzu shikenan yarinyar nan zata raina sa,ta daina ganin sa da mutunci, daman ba wani tsoron sa take jiba bare kuma wannan abun ya faru, ai yanaga har zagin sama watarana zata iya yi,  

Babban tashin hankalin sama shine da wane idon ma zai kalle ta, har yasata wani abun, ga kuma idan gari yagama wayewa me zaicewa Æ´an gidan, dan yasan sai ta faÉ—a, wata iska me zafi ya firzar yana tunanin mafita, da yayi tunanin ko yabar gidan sai kuma ya tuna da case É—in Uncle É—in sa, da yadawo yau yau É—in nan taya zai tafi yabar maganar,

"Ya ilahi, ya kuma furtawa a fili yana cije lip ɗin sa na ƙasa kamar zai fasa shi, gaba ɗaya haushin kansa ne ya kamasa, jin ana niyar idar da sallar yayi saurin yin gaba ya buɗe wardrobe ya zaro jallabiyar sa ya zura ta ajiki tare da gajeren wando, yana ganawa ya ɗauki salaya ya shimfiɗa da an idar da sallah a masallaci saidai yayi tasa a ɗaki,

Yana idarwa yayi azkar yayi addu'o'in sa sannan ya koma kan gadon bin gurin yayi da kallo yanda duk shimfiÉ—ar ta ya mutse saboda kokawa da sukayi, wani wawan tsaki yaja, yana hararar gurin sai kace itace agun,

A haka ya kwanta yana rufe idon sa, sai kawai abun da yafaru tunda ga farko da tafara kunno sa, yafara ciwun ciki, da bata jangwalo sa ba ai da duk haka bata faruba,

Yanda ya dinga yi mata ne yake tayi masa yawo a ƙwaƙwalwa, baisan loƙacin da ya furta "wai daman haka abun yake? yana maida yanayin fuskar sa kamar yana tambayar wani akusa dashi,

Can ciki ciki ya kuma cewa so sweet yana faÉ—a yana lumshe idon sa, É—ayan filon kawai ya jawo ya rungume yana me sauke wani irin sanyayyen numfashi, dan jinsa yake garau, duk da in ya tuna abun kunyar da yayi yakan haushin abun, amma kuma idan ya tuna irin daÉ—in da yaji, sai kawai yaji ya manta da wata maganar abun kunya, shi son samun sa ma dama ya samu daÉ—i, dan har yanzu ji yake kamar wani abun nata yana jikin sa,

Yana cikin tunane tunanen bacci ne daÉ—i yayi gaba da shi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa yake baccin sa,

........ Ameesha na fita ta wuce É—akin su bugu biyu tayi taji ba abuÉ—e ba sai ta gwada murÉ—awa tana murÉ—awa taji ta buÉ—u da sauri ta faÉ—a ciki, tana shiga taga Dadda akan salaya tana sallah sai kawai tayi saurin shigewa toilet saboda bata sonma Dadda tayi mata magana,

Nan ma  da ta shiga wankan Saida ta zauna taci kukan ta ta more sannan tayi wanka tayo alwala ta fito tana ta faman sassada kai ƙasa, gashi kanta nayi mata wani irin ciwo gefe guda, haka tayi sallar a daddafe sannan ta rarrafa ta koma kan gado ta kwanta, Allah ya isa kam ta jawa Meera ita ba adadi, gaba ɗaya ta gama cika da jin haushin sa, jitayi ta tsanesa ma gaba ɗaya,

Itama wahalallan ba ci ga É—auke ta,

Duk wani motsin ta Dadda nasane da ita ta rabu da ita kawai, saboda daman suna sane ita da Maama suka tura ta kuma taga alamun kamar, burin su ya ciga, dan ta fahimci wani abun ya faru tsakanin su tunda ta ganta da asuba haka, tasan dai ba babban abun  ya faru ba, tunda ta ganta tana tafiya da kanta ta.......,

Bayan gari ta waye sosai har ankawo musu breakfast gaba É—ayan su har su Abban Ameesha, ko da akazo cin abincin babu Meera babu Ameesha suna can suna bacci, su kuma su Ma'ana dake sun san me suka shirya, sai suka rabu dasu babu wanda ya tashe su, acewar su basu samu bacci ba shi yasa suke baccin wahala,, aka barsu dan kansu sa tashi,

Ameesha nata tashi amma sai ta kasa fitowa tayi zaman ta aɗakin, har ɗaki Dadda ta ta kawo mata abincin ta, harda su lallaɓata, ita abun har mamaki ma yaso yabata gashi basuyi maganar komai b, kuma Dadda nata rawar ƙafa,

Meer kam tun kan ta tashi ma shi ya tashi babu wanda yagansa ya fice daga gidan ma gaba É—aya, sakamakon kiran da a Khalid ya kirasa, .......,
[15/11, 10:53 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                         *_🅿️41_*

...........Tun adaren jiya su Dadyn Bossay suka dira a garin kano inda direct suka wuce da Ayuba asibitin su Sam, cikin mawuyacin hali,

Nan danan lokitoci suka rafar masa aka fara basa taimakon gaggawa, dan halin da yake ciki yana daf da rasa ransa,

Koda gari ya waye ma bai farfaÉ—o ba, sun rasa gane kansa,

Saida Meer ya shiga gurin da aka kwamtar da shi ya shiga yi masa nasa duban, amma har gari yafara haske bai Ayuba, bai farfaɗo ba, amma dai ansamo kan matsalar ƙwaƙwalwar sa ce ta bugu inda ake sa ran koda ya farfaɗo ba lalle bane ya farfaɗo cikin hankalin sa zai iya samun wata matsalar daban......,

Cikin masarauta kam da wajen ta, maganar bayyanar Abban Ameesha ta gama bazuwa wasu na ta zuwa suna ganin sa, ƴan cikin masarautar kam kowa sai kulawa ta musamman ake basa, Ameesha ma, zuwa yanzu ta ɗan saki jikin ta, tana gurin su Amra ma, suna hira tare da Azeema da tunda taji labari ta iso gidan tundan domin taya ƙawar ta murnar bayyanar mahaifin ta, suna zaune harda sumy da har yanzu bata koma gida ba, itama saboda momma ta hanata tafiya,

Fulani kam saboda farin cikin ganin Abban Ameesha, kunsan ta zauna da shi tana matuƙar sonsa, saboda shima, take son Sam har ta dawo dashi part ɗin ta yake zama, saboda ta rasa, Abban Ameesha, dan a loƙacin ma kusan kullum yana gurin ta saboda soyayyar da take nuna masa,

To har yanzu soyayyar tana nan dan haka ta roƙi Allah Annabi ya dawo part ɗin ta, da zama zata basa kulawa marar misaltuwa dan bataso yaƙara nesa da ita, yanda take jin ƙaunar sa aranta, ji take kamar ita ta haife sa,

Ba jayayya kuwa Maama ta kuma aminta da ita akaro na biyu, shima kuma Abban Ameesha, ya yarda saboda yanda yaga tana nuna yanda take son sa sai yaji shima matar ta kwanta masa ya amince zai koma, daman É—akuna biyu ne aciki, daga na Sam sai extra bayan nata da take dashi a can ciki,

Nan ta ɗau alƙawarin zata sa a canza masa komai na ɗakin ya faɗi kalar da yake so,

Su Dadda da Maama suna cike da farin cikin tarkon da suka haÉ—awa musu, kuma nan suka sake yanke shawarar nan da sati É—aya zasu tattara su a ware musu part É—in su daban, koda gina musu ne, sai ayi, sai kuma Papa ma yace kawai za'a kwashe kayan part É—in Ammah dai su kuma can, tunda yanzu babu kowa aciki,

Su Maama kam sunji daÉ—in hakan, tun aranar suka fara shirye shiryen yanda za a fara gyaran part É—in,

a ranar wunin dai wuni sukayi suna hira, amma ba Meer dan har yanzu bai dawo ba, ita kuma Ameesha tana can part É—in su Amra,

Amma sauran duk suna tare, Fulani, Dadda, Papa, Maama, ummy, Abuu, sai Abban Ameesha da suka saka a tsakiya, kowa yana kallon sa cike da so da ƙauna......

labarin Ayuba baizo musu ba sai can da yamma Sam ya dawo cikin masarautar yake sanar dasu duk abun dake faruwa da accident ɗin da Ayuba yasamu, dan duk atunanin su accident yayi ba bugesa akayi ba, anan shima yake jin labarin bayyanar Abban Ameesha,  ya nuna farin cikin sa sosai,

Bayan anyi sallar magriba suka tattara gaba ɗaya suka je suka duba sa, har zuwa loƙacin bai farfaɗo ba,

.........Wuni guda da Meer ya fita suna tare da Khalid amma hakan nan sai ya tsinci kansa da kasa basa labarin abun da yafaru tsakanin sa da Ameesha amma loƙaci zuwa loƙaci takan faɗo masa arai da tuna moment ɗin su na daren jiya,

A gidan da suka ajiye mutanen da suka kamo loƙacin da ya tura su Ameesha nan, yaje ya ƙara lugudar su tare da sawa aka tura su can police station ɗin su Khalid,

Tare da Khalid suka tafi shikuma ya tsaya a gidan bai bisu ba,

  Mutane  biyun kuma da ya kamo daga gidan su Rasheeda yaran Dady, su kuma yaja su wani ɗaki suka tattauna game da abun da suka sani akan sa, amma ga mamakin sa sai suka ce masa kawaidai idan ƴarsa tana son wani abun ko kuma wani abun yasamu ƴarsa, ko kuma idan yana son akawo masa wani, to sai suje su ɗauko masa, shikenan aikin da suke masa, amma dai suma kansu sunsan da abun da yake yi marar kyau kuma yana da wasu yaran bayan su, wanda su kuma basu san aikin da suke masa ba,
Chapter 68 · 0% Book details