← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 103

Sashe 64

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk buɗewa suka shiga yi suna sauke sa akan sa kafin idon wasu ya zama ya koma kan Abban Ameesha dake tsaye agaban ta idon sa akanta ko ƙiftawa bayayi,

ai kafin wani yayi magana tuni Dadda tayi zunbur, muryar ta cike da É—unbun mamakin da ya kusa zautar da ita tace "SAMEER ÆŠANA...!!!!!!!!!
[15/11, 10:53 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                         *_🅿️38_*

____ai kafin wani yayi magana tuni Dadda tayi zunbur, muryar ta cike da É—unbun mamakin da ya kusa zautar da ita tace "SAMEER ÆŠANA...!!!!!!!

Su Papa ma ba shiri duk suka miƙe tsaye jin sunan da Dadda ta kira wanda ke gaban su,

jiki na karkarwa Dadda ta ƙara so inda yake tuni idon ta har ya jiƙe da hawaye, tana zuwa hannun ta na karkarwa ta ɗaga ta taɓasa dan ji take kamar ko ba shi bane,

Tana taɓashi tace "Sameer kaine kodai mafarkin ne dan Allah idan mafarki nake kar ku tashe ni, dan Allah Sameer katsaya karka ƙara tafiya kabarni, sai surutu take kamar zararriya, sai tattaɓashi take,

Shima hawaye na zubo masa shima yariƙota yace "Umma nine ba mafarki kike ba,

Ƙara rikicewa jin muryar sa, rungume juna sukayi tana kuka shima na yana zubar da hawaye,

Da sauri Dadda ta sake shi, ta juya tana kallon Ameesha da ta gama daskarewa agun takasa koda motsi, tunda ya shigo jikin ta yabata mahaifin tane to amma shiga ruÉ—ani ya hanata motsi bare ma magana,

Kamo hannun ta Dadda tayi tace shalele kinga mahaifin ki wannan shine mahaifin ki kitaso kizo gare sa kinji mahaifin kine,

Sameer kaga Æ´arka ta girma ko gata nan kullum burin ta ta ganka anemo mata mahaifin ta sai gashi yau kadawo gareta,

kamar marar laka ajika haka Ameesha ta koma har yanzu takasa yarda da abun da kunnuwan suke jiyo mata daga, takasa gasgatawa kawai ji take kamar a mafarki,

Ganin hakan yasa Meer matsowa kusa da ita yana zuwa ta ɗago tana kallon sa, tana so taƙara tabbatar wa kanta ba ita kaɗai take ganin abun dake faruwa ba,

jinjina mata kai yayi tare da ɗan lumshe idon sa ya buɗesu a loƙaci guda, yayi alamun tabbatar da abun da take gani tare da nuna mata mahaifin nata da hannu yana ƙara jinjina kai,

A hankali ta miƙe taje kusa dashi sai kuma ta tsaya tana ƙara kallon sa,

Buɗa mata hannuwan sa yayi alamun tazo garesa, da sauri ta faɗa kansa ta rungume sa ƙam shima rungumetan yayi tare da rufe idon sa saboda yanda yaji son ta da ƙaunar ta suna shiga jikin sa, itama ƙaunar mahaifan natane yake shigar ta, sosai take yin kuka ajikin sa, shi kuma yana ɗan bubbuga bayan ta, dan baƙarmin taƙaicin jin kukan nata yake ba acikin jikin sa,

Sun ɗau tsawon loƙaci ahaka kowa yakasa sakin kowa kamar su kaɗai agun, har saida Abuu yayi musu magana dan shima ya matsu yaji ɗan uwan nasa akusa dashi,

Maama ta ƙosa taji ɗumin ɗan nata amma taga alamun bashida niyar zuwa gurin ta, (kunsan dai ƙaunar da take masa har tafi sonsa akan Abuu amma saboda baisan ta ba sai gashi baije gare ta ba)

koda yasaki Ameesha kawai leƙen inda zai gano matar sa da Baba yake amma baigan suba saboda baisan su Papa ba, ammadai su Bossay sun basa labarin su amma baisan su a fuska ba,

Saida Dadda ta nuna masa su Maama tare da ƙara gabatar masa dasu da nuna masa matsayin kowa agun sa,

Tsaya wa bayya na yanayin da kowa dake gurin ya tsinci kansa ɓata loƙaci ne, kowa zai iya imagine ɗin halin da kowanne su zai kasance. Nan guri ya ƙara kauraye wa da hayaniya kowa da koke koken daga baya kuma aka koma farin ciki, sannan su Bosaya suka bada labarin abun da suka sani har suka taho dashi Kano.

yanzu kowa na gurin na zaune shima Abban Ameesha ansamar masa guri na musamman ya zauna, dan kowa yana ji dashi idan kana gurin saika kasa sanin waya fi son shi a tsakanin mutanen nan, tsakanin Dadda,Maama,Papa, A. . buu, Gwaggwo da kuma Meer da Ameesha, kowa sai nan da nan yake dashi, Ameesha kam tana katarar sa ta maƙalƙake masa, Meer kuma yana ɗayan gefen sa shima baiyi nesa dashi ba, Dadda kuma tana gaban sa duk sun wanin zagaye sa sai kace zai gudu....

Duk hankalin Abban Ameesha bai gama kwanciya ba saboda baiga Noorin sa ba da kuma Baba amma yaga alamun ba'a da niyar yi masa bayani akansu, ji yayi bazai iya jure wa ba dole ya kalli Dadda, yace "Umma,

Da na'am Dadda ta amsa masa gaban ta na faɗuwa dan tasan ta tsuniyar bazata wuce ta ƙoƙi ba, amma a fili bata nuna masa hakan ba sai ta sakar masa murmushi ma,

"Umma ina noori da Baba? cewar Abban Ameesha,

shiru tayi ta kasa basa amsa dan batasan ma me zata ce masa ba,

Sauran ta fara kalla ko zata samu meyi masa bayani, amma sai aka shiga Æ´ar kallon kallon, akayi tsit,

Dadda ce ta fashe da wani sabon kukan cikin kukan tace saidai kayi haƙuri malam sundaɗe da kashe shi tun loƙacin da suka ɗauke ka muna dawowa gida shima suka ɗauke shi sukaje can wani wajen suka kashe shi, Nadeeya ma ta rasu, mukaɗai muka ɗai ne muka rayu shiyasa muka baro garin Gombe muka dawo nan, gashi duk inda akace min anƙulle ka idan naje bana samunka, loƙacin da naje na sameka a prison ɗin daga nan ban ƙara sanin inda suka maida kai ba dan mutumin ma da yake taimaka min wajen ganin ka sai suka ɗauke shi daga gurin na daina ganin sa,

Shi duk wannan sauran bayanin da take ba jinta tunda tace Baba da Noori sa sun mutu, bai ƙara jin me take cewa ba...,

Cike da tashin hankali yake kallon ta so yake yayi kuka ma ko yasamu sassauci amma yakasa zuciyar sa ta bushe,

"Kayi haƙuri Babana addu'a zakayi musu, tunda kaidai kadawo lafiya shikenan abun da nake fata kenan, babu da zance sai dai inyiwa Allah da ya nuna min ranar da zaka haɗu da iyayen ka da raina da lafiya ta wannan abun yafimin komai farin ciki,

Girgiza kai ya shiga yi sai yanzu hawayen suka samu damar zubowa, "a'a Umma kidaina wannan maganar dan Allah kar ki kuma cewa su mutu ina son ganin Noori a raye dan kice min bata mutu ba, yama miƙe tsaye dan ji yayi duk wani farin cikin da yake ciki ya neman gushe mishi burin sa kawai yasa ta a idon sa dan ji yake in ba ita bazai iya rayuwa ba idan babu ita saboda tsananin son da yake mata,

Da ƙyar aka samu ya koma ya zauna aka shiga rarrashin sa da basa haƙuri kowa saida yasa baki, sannan ya daina surutan da take ya kamo Ameesha ya rungume ta yana ƙara jin ƙaunar ta aransa dan ita yake gani kamar Norri ɗin sa, duk wanda yagan sa a wannan loƙacin sai ya tausaya masa,

Cikin tsananin damuwa Abban Ameesha yace "duk wanda yakashe su bazan taɓa yafe masa ba sun cutar da rayuwata sannan kuma sunje sun cutar da wasu akan meyasa zasu kashe su bayan inma laifi ne ai ni nayi musu binne yasa basu kashe ni ba, ni da rayuwar da suka nayi ai da kashe ni sukayi, sun kaini waje guda sun ajiye ni, tunda suka fito dani daga prison ban ƙara ganin kowa ba nayi rayuwa cikin wani irin hali wallahi da rayuwar nan gwanda mutuwa gashi bansan su waye sukayi min haka ba, bansan me nayi musu ba, kuma abun ya wuce kaina ya koma kan matata da babana bawan Allahn da baiji ba bai gani ba,

Maganar yake cikin ɓacin rai da damuwa dan shi abun duk da yafi ɓata masa rai kashe sun da a'kayi inya tuna duk dan saboda dashi suka shiga wannan halin sai yaji yama tsani rayuwar gaba ɗaya,

Itama Dadda tana kuka tana basa haƙuri da nuna masa haka Allah ya tsara bashi yaja ba, daman ko dashi ko bashi Allah yayi Nadeeya da malam bama su tsawon rayuwa bane, ka manta da komai, yanzu babu abun da ka rasa, ga ƴarka ga iyayen ka babu wanda ya rasa ransa, gaka acikin dangin ka martaba kima daraja mulki duk ka haɗa, dan haka kaman ta da wata damuwa,

Saboda halin da yake ciki ma ko amsa bai bata ba dan maganar tama so tayi ta ɓata masa rai taya za'ai ta manta da matar sa, dafe kansa kawai yayi shi kaɗai yasan halin da yake ciki...

Ran Meer ba ƙaramin ɓaci yayi ba ganin halin da Uncle ɗin sa ya shiga atake a loƙacin yanayin sa yafara dayawa daga farin ciki zuwa baƙin ciki har hannun sa yake damƙewa saboda yanda zuciyar sa take tafarfasa. Sai yanzu ma abun yake ta ƙara dawo masa suka ɗauke shi tsawon loƙaci suka rabasa da komai nasa sun kashe masa mata, ya ɗauki alƙawarin koma waye yayi masa haka bazai taɓa ƙyale saba sai yayi masa hukunci me tsananin kuma yanda suka sa yayi rayuwa batare da kowa nasa ba, suma baza su ƙara rayuwa awaje sai sun ƙare rayuwar su a gidan yari, (life in prison)
Chapter 64 · 0% Book details