← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 103

Sashe 43

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️

    'Rasheeda tace "to meye abun jin kunaya yaya kaine fa babban yaya
na idan ban gaya maka wa kake so infaÉ—awa, tsaka nina dakai ai ba wata kunya wallahi......,

   "Hmm to naji mai babban yaya, bari inshiga mugaisa da mom sai mu ɗora daga inda muka tsaya, ina fatan dai antanadar wani abun ko?

Ɗan turo baki tayi tace "haba yaya ai kasandai bansan da dawowar ka da na tanadar maka amma yanzu ka shiga kafin ka fito na tanadar maka ɗin, bari in shiga ciki, gurin lami, tasan yanda zatayi da babban baƙo,

ÆŠan murmushi kawai yayi sannan yayi gaba zuwa wajen mom, ita kuma ta nufi kitchen cike da farin cikin ganin yayan nata,

yana zuwa ƙofar ɗakin mom yayi nocking daga ciki tace shigo,

Turawa yayi ya shiga ciki da sallama abakin sa, tana zaune gaban kayan tana duba wanda zata saka ya shigo, da sauri tajiyo jin muryar a bazata, ganin dai da gaske shine yasa ta ajiye sauran kayan ta juyo fuskar ta ɗauke da murmushi, tace "amma dai mafarki nake, dan nasan wannan ganin dai bada gaske bane saidai a mafarki, tana maganar tana ƙarasowa wajen sa,

Dariya yasaka tare da tsugunnawa a ƙasa yace "mom ba mafarki bane nine dai, suprise nayi muku shiyasa kuka ganni haka kamar na faɗo ta sama,

Itama dariyar tayi tace "gaskiya nidai bana son irin wannan zuwan haka kawai ba tarba mai kyau,

Ɗan shafa kansa yayi yana sakin murmushi yace "to mom tuba nake ayi haƙuri bazan ƙara hakan,

"gaskiya dai kar ka ƙara dan banji daɗi ba wallahi,

Haƙuri yaƙara bata sannan ta haƙura tare da samun waje ta zauna, daga kusa dashi a bakin gado, sannan ta ɗora da cewa "ya hanya ya gajiya?,

"Wallahi lafiya lau mom yana same ku, kuna lafiya?

Itama ta amsa masa da lafiya, nan suka shiga gaisawa ya daÉ—e agurin ta inda har ta É—an basa wasu abubuwan da suke faruwa a gidan, sannan daga baya suka yi sallama yace bari ya watsa ruwa yaci abinci sai suce gaba da tattaunawa,

Bayan fitar sa, itama tayi saurin shirya wa ta fita taje ta samu su Rasheeda suna ta ƙoƙarin yi masa abin da zaici, ita da lami amma lami ce ƙarfin aikin, haka itama ta shiga suka haɗa hannu suka ci gaba da shirya masa abun da zaici mai ɗan daɗi..........,

************************

_____Shettima

'Tun ranar da abun nan ya faru ya koma gida bai ƙara samun wani sukuni ba, tunda ya dawo yake kwance a ɗaki ko abinci ma baya samu yaci sa sosai shima saidai indan hajiyar sa ta takura masa yake ci, dan tayi tayi yagaya mata abun da yake damun sa, sai yace mata babu komai daga baya ma kawai sai yace mata ai Sam ne baya gida yabata labarin abun da ya faru, sannan yace sai kiran wayar sa yake taƙi shiga duk ya kashe wayoyin sa, ga kuma halin da mahaifiyar sa take ciki na ƙarin abun da ke faruwa acikin gidan su, saobada suma labari yazo musu tuntuni sun san duk abun dake faruwa tundaga A har Z shiyasa abun yake damun sa, ya rasa inda zai samu sam ya sanar dashi abun dake faruwa dan yadawo wajen mahaifiyar sa, yayi mata ƙarya da fakewa da Sam,

Dalilin hakanne yasa ta rabu dashi itama ta taya sa neman Sam ɗin amma aduk loƙacin da takawo masa abin ci yaƙi ci sai tayi masa faɗa wataran kuma tayi masa nasiha da kwantar masa da hankali da hakan yake haƙura yaci,

Yauma kamar kullum yana zaune akan kujerar yasaka abincin agaba yana kallo a zahiri zaka ce abincin yake kallo amma a baɗine hankalin sa bama ya gurin, tunanin sa kawai yake yanzu ai suna can tare, ga taƙaici ya hana sa zuwa gidan su, dan har yanzu haushin yake ji, saboda duk laifin tane mai yasa da yace kada ta shiga ta shiga, shiyasa ya rabu da ita yayi alƙawarin bazai ƙara neman ta ba, indai ba ita tane me shiba, gashi kuma abun nema yake yayi masa illa yakasa jurewa,

Yana wannan tunanin wayar sa tayi ringing da kamar bazai dauka ba, sai kawai yaja tsaki tare da miƙa hannu ya ɗauke ta batare da ya duba number dake kiran shi ba, kawai ya ɗaga tare da kara wayar a kunne, sai yayi shiru baice komai ba, kamar daga sama ko a mafarki yaji saukar murya ta a cikin dodon kunnen sa, da sauri ya zaro wayar ya duba screen ɗin wayar da ya tabbatar da wai da gaske ne abun da yaji ko kuma kunnuwan sane sukayi masa ƙarya, zubawa number ido yayi cike da tabbatar wa kansa ganin sunan da yayi saving da number ta ɓaro ɓaro yana yawo akan screen ɗin wayar, mayar da wayar yayi kan kunne sa,

Stiil dai yaƙara jin muryar ta tana tayi masa sallama,

da ƙyar ta tattaro duk wata guntuwar nutsuwar sa da ta rage masa ajiki, yayi ƙoƙari ya amsa mata mata da wa'alaikissalam, a yanda yayi maganar dake awaya ne ita baza tace a cikin damuwa yake ba,

"Ina wuni, yaji ta ƙara cewa,

"Lfy qalau " shima ya amsa mata dashi tare da ƙara yin shiru,

Itama kuma sai tayi shirun ta rasa kuma me zatace masa,

Jin tayi shiru har tsawon wajen minti 2, sai kawai ya daure yace "baki da abun cewa ne inkashe kin kirani kuma, kinyi min shiru,

Azeema ma ana ta ɓangaren ma daurewar kawai take dan ko kiran ma ta gwada kiran sa yafi sau ashirin tana fasawa tun ba yauba sai dai yanzu ta rufe idon ta ta daure ta kirasa,

Tana kwance akan gadon ta jin abun da yace yasa ta runtse idon ta, kuma bata san maiyasa takasa katse kiran ba tunda ya riga ya ɗaga, da ƙyar ta buɗi baki, tace "uhmm daman akan maganar nanne daka turo min message kace in sameka a mota ni kuma da na fito bangan kaba shine yanzu na kira inji ko maiyasa kace haka, idan da wata maganar sai muyi ta nan,

jijjiga kansa yayi jin rainin hankalin da tayi masa maiyasa zatace wai bata gansa ba bayan kuma ƙarya take yana kallon ta ko inda yake ma bata kalla ba tana fitowa ta tafi gurin motar da zasu tafi amma shine yanzu zata raina masa hankali, wani haushin tane yaƙara zuwan masa wuya,

"Shikenan ai tunda baki zoba a loƙacin ai ya wuce sai kije kuci gaba daga inda kuma tsaya, ai bani yakamata ki kiraba kije ki ta kiransa ƙarewa duk inda zaki ku tafi tare har bacci ma kuringa yi tare kar ku rabu da juna ƙarewa daukan ki a mota, sannan dan Allah kar ki ƙara kirana banaso tunda bani da matsayin da zan miki magana kiji to kije na barki dashi ɗin kirabu dani da abun da yake damuna basai kin ƙara min da taki ba banaso, Allah yaba ku zaman..., yana kaiwa nan ta buɗi baki zatayi masa magana kenan yayi saurin kashe wayar tare da jefar da ita aƙasa yana jin zuciyar sa na wani irin ƙuna,

Kwantar da kansa yayi ajikin kujerar yana rufe idon sa,

kamar daga sama yajiyo muryar hajiyar sa tana cewa "daman nasan wannan damuwar ba iya ta rasa Sam bace akwai wani abun aƙasa, ashe sirika tace ta saka min yaro gaba, tana maganar tana ƙarasowa wajen sa sannan ta tsugunna ta ɗauko wayar tare da zama a kusa dashi,

BuÉ—e idanun sa yayi tare da gyara zaman sa yana mamakin ya akai tajisa shi yama manta a inda yake da yasani ya koma É—akin sa,

"Haba babana, muryar ta, ta katse masa tunanin sa, tace "haba haba sai kace bana miji ba kai waya gaya maka ana soyayya a haka, ba 'a saurin yanke hukunci cikin fushi, gaya min maiye tsakanin ku kuma mai ya haÉ—aku?

shiru yayi na wasu ƴan sakanni sannan ya numfasa da farko yaso ɓoye mata amma daga baya da ya tuna ta riga tasan komai, kuma daman tsakanin sa da ita ba wata ƴar ɓoye ɓoye baya iya ɓoye mata komai, tunda aduniyar nan ita kaɗai ta rage masa idan da wanda zai iya gayawa damuwarsa bayan ita to saidai Sam su su biyun nan su kaɗai yake gayawa damuwarsa to yanzu Sam baya nan dole ita ce wacce zai gayawa abu dake damunsa dashi akaran kansa abun mamaki yake basa baisan ya akai sonta yakamasa haka ba loƙaci ɗaya, kuma bai ƙara tabbatar wa ba sai ranar da yagan su da Hamza,

Nan ya gyara zama yafara bata labarin duk wani abu da ya faru tsakanin sa da Azeema amma yana rage wasu abubuwan kamar loƙacin da yafara ganin ta a office ɗin sa Salim baya nan har ya ɓalle mata bra, da kuma gurin da ya riƙeta a ɗaki har ta fito ta shiga kitchen ya ƙara binta, har Fulani taso ta kamasu Allah ya taimake su, komai Saida yagaya mata, har loƙacin da wannan na ƙarshen yafaru yagan su da Hamza alamun dai suna soyayya tare...,

Hajiya yana gama bata labari tasaka masa dariya sannan tace "masa ai ba haka ake soyayya ba wannan ai duk laifin sane tunda batasan yanayi ba kuma bai taɓa gaya mata ba to taya zata san yana sonta, idan sonta yake yi ai gaya mata zaiyi sannan tasan dashi amma bai gaya mata ba taya zai ringajin haushinta, nan dai Hajiya ta tsaya da kanta ta nusar dashi kuskuren sa da ɗora sa a hanya har ta fahimta sannan tace yaje har gidan su ya shawo kanta kuma yabata haƙuri in kuma ba hakaba to komai ma zai iya faruwa, yana zaune wani zai aure ta,
Chapter 43 · 0% Book details