Sashe 56
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzu ma da sauri ta girgiza masa kai hawaye na shirin fara saukowa daga idon ta,
Kawar da kansa yayi yace "kika sake kika min kuka anan sai nasaki me dalili kitashi kishaga ki wanke min toilet sannan kizo ki gyara É—akin nan daga yau yazama aikin ki tunda kina tunanin ke matar aure ce, to ba daÉ—i zakiji ba wahala zaki sha uban da yace kibari a É—aura auren..,
Da sauri ta ɗaugo batasan loƙacin da tace "nima fa baso nake ba kuma bansan anɗaura ba me yasa zakayi min wannan fahimtar nuna baso nake ba kuma ai nagaya maka tun jiya kasake ka huta nima in huta dan wallahi naci gaba da zama ahaka zan iya rasa raina saboda bazan taɓa iya rayuwa da kai ba, kafi ƙarfina kalar ka daban kalata daban halin mu ba iri ɗaya bane daga jiya zuwa yau ni kaɗai nasan halin da na tsinci kaina da zaka taimaka min da ka sauwwaƙe min tun ba aje ko ina ba na roƙeka kasake ni, kuma kama daina wannan tunanin kamar yanda kace wai na rainaka saboda ina tunanin auren dake tsakanin mu, to ko ɗaya bazan taɓa ɗaukan hakan ba, shigowa ta ma gurin ka bawai dan da son raina bane dole ce tasa nashigo na ajiye maka batare da na tanka maka duk maganganun da kake kawai ina yi maka biyayya ne saboda gudun magana banason abun da zaisa kaci mutunci na ko kamin muguntar da kasaba, amma idan ban kulaka ba sai mu zauna hakan to naga kai kuma duk yanda akayi ma ba'aburgeka sai kayiwa mutum masifa da bala'i, shiru tayi tana goge hawayen da yagama wanke mata fuska,
Tana giogewa kuma ta miƙe daga gurin cikin sauri ta shige banɗakin nasa, tana shiga ta rufo ƙofar,
Yana zaune agun yana jiyo shashsheƙar kukan ta a bathroom ɗin domin da ta shiga banɗakin guri tasamu kawai ta kama kuka saboda tsabar wani ƙatoton baƙin ciki da yake taso mata daga ƙasan zuciyar ta, da ita kanta mamakin hakan take, kawai dan anɗaura mata aure sai gaba ɗaya rayuwar ta ta nemi canzawa alhalin wanda ka ɗaura mata ɗin ɗan uwanta ne, idan kuma tunanin auren Bossay ai shi Meer ɗin yace zai sauke ta taje ta auri duk wanda take so, kuma ko a yanzu bai hanata kula kowa ba, to amma batasan me yasa take jin irin wannan yanayin ba gaba ɗaya batajin ta daidai, ta wani fannin kuma so take ta haɗu da tsohon nan hakan kawai taji tana buƙatar ganin sa,
A ɓangaren Meer kam maganganun da Yahaya masa ba ƙaramin tsaya masa arai sukayi ba, karon farko da maganar wata mace macen ma yarinya kamar wannan tagaya masa magana yatsaya yana tunanin maganar ta, gashi daman tun ba yauba ya tsani yaji tace masa mugu, hakan yaji tabasa tausayi, da ace akaran kansane da tuni ya saketa kodan yaga ta dena wannan tunanin akan sa gashi tace tana son wani, da ace yana da yanda zaiyi da sakin nata zaiyi, amma ta zauna yayi tunani kwata kwata bazai taɓa sakin taba indai ba su abune suka haɗu suka ce yasake taba shine zai sake ta a yanzu dai saidai kuma idan tayi haƙuri zai saketa ne daga zaran loƙacin da ya ɗibarwa kansa zai zauna da ita loƙaci na cika zai saketan ko da yardar su ko ba yardar su, amma kuma bayaso ya ganta cikin irin wannan yanayin da yaganta yau a kwana ɗaya har ta canza, kuma tabbas zata shiga wani hali kamar yanda ta faɗa idan suka cigaba da zama a haka,
Sosai ya shiga tunani samowa kansa mafita akan wannan sabon al'amarin da yake neman hanasa sukuni, baitaɓa tunani yarasa mafita irin na yau ɗin, yanke shawarar kiran Khalid yayi dan yazo su tattauna akan yaji ta bakinsa, dan yana buƙatar neman shawara dole ya kirasa,
Ya miƙa hannu zai ɗauki wayar kenan ita kuma ta fito daga bathroom ɗin bayan tagama kukan nata ta wanke banɗakin shine ta fito,
Fitowar tace tasa yafasa É—aukan wayar yana kallon ta, ta fara tattare É—akin, sai kawai yace "zo kifice min daga É—aki, anjima ki dawo ki gyara idan na fita,
Ko uffan bata ce ba kuma bata ƙara ɗaukan komai ba ta dakata da tattarar da take duk da daman ba wata tattarar arziƙi bane dan ba wani datti a ɗakin kawai dai ledojin abarsa da yasaba shane sai wata jaka da ya ajiye ta kan kujera,
zata fita yakuma cewa "wazai É—auke miki wannan tarkacen ko ance miki mayunwaci ne ni,
"hmmmm tace aranta kawai ta dawo ta É—auka ta fice abun ta bata kuma tanka masan ba,
Binta yayi da ido har tagama ficewa daga ɗakin sannan ya ɗan jinjina kai tare da dafe kansa, shi kansa yasan bazai taɓa canzawa ba kafin fa ta fito yabarwa ransa bazai kuma tanka mata ba har ta fice amma sai gashi daga fitowar ta ya koreta,
wayar ya É—auka ya kira Khalid yana É—agawa yace "ko me kake kabari kazo yanzu ina son muyi wata magana Please,yana jiyo sa zai fara tsokanar sa kawai ta kashe wayar daman yasan halin sa inbaiyi ba ai ba shi bane,
yana ajiye wayar yaƙara luluƙawa wani dogon tunanin game da sabon lamarin da yake shirin tunkaro sa......,
************************
____Su Hamza sun ƙaraso gidan su Bossay inda suka samu tarba me kyau daga ɓangaren su Ammi, a babban falo suka sauka inda aka baje musu kayayyaki masu yawa itadai Ammi taji daɗin zuwansu musamman ma Ayuba da akace shi ɗan uwansu ne,
Bayan sun gama ciye ciyen su a kwashe kwanukan akan kira duka sauran yaran gaba ɗayan su suka hallara acikin falon inda Dadyn su Bossay ya ƙara gabatar da su Ayuba da Hamza agaban sauran yaran sannan aka ɗan basu taƙaitaccen bayani game da abun da yafaru, sannan Ayuba ya ɗora musu da nasa bayanin da kuma buƙatar da yazo musu da ita akan zasu koma can gaba ɗayan su domin su gabatar da kansu acan kowa yasan su yasan dasu,
Gaba ɗayan su sunyi matuƙar farin ciki dajin asalin su,
Dadyn su Bossay yace ta amince zasuje ɗin amma za abari a ɗan ɗaga masa ƙafa saboda shirye shiryen bikin Bossay da ya riga ya gabato saura kwana shida baikama ta ace sun tafi ba gwara idan akayi ko sati ɗaya ne sai su tarkata har ita amaryar tashi su tafi amma yanzu idan sukaje hankalin su ma duk ba'a guri ɗaya ba kuma bazasu daɗe ba zasu ƙara dawowa saboda auren,
Sai Ayuba yake cemasa yayi haƙuri dai ko susu biyune su fara zuwa ko inyaso sai adawo ayi bikin ko kuma su ɗaga bikin idan komai ya daidai ta sai ayi bikin ma acan,
Nan shima Dady yace gaskiya aure ta matso bazaiyiyu ace an É—aga saba, yanzu dai abun da za'ayi shine kawai su kwana anan inyaso gobe da sassafe sai su shirya dashi Ayuban da Hamza su fara yin gaba inyaso shi ya biyo su daga baya,
Duk dai yanda Ayuba yaso yaja ra'ayin Dady ya amince amma yaƙi yarda dole suka tsaya akan goben zasu tafi su kaɗau ɗin,
Nandai zama ya tashi inda Bossay yaja Hamza ya sauka aɗakin sa shikuma Ayuba tunda ba sa'ansu bane dady ya ajiye sa aɗakin sa na ɓangaren baƙi, da suka shiga kuma nan suka ƙara zama Ayuba yana ta basa labarin abubuwan da yasani nagame da masarautar da labarin mahaifin su......,
Su Hamza kuma suna É—aki suma Hamza yana tambayar Bossay wai dama aure za ayi masa, nan Bossay shima yake basa labarin baya son auren yabasa labarin yarinyar gaba É—aya tun farkon haÉ—uwar su har zuwa yanzu yabasa har labarin yanda yarinyar ta kirasa tagaya masa bata sonsa amma shi baisan meyasa Dadyn sa yana ce sai anyi auren ba, duk da yaji komai, yagama basa labarin cike da É—inbun damuwa afuskar sa,
Hamza yayi mamaki sosai sai yacewa Bossay ya kwantar da hankalin sa zaisa afasa auren indai bayaso amma da sharaÉ—i sai yafara samun wacce za'aÉ—auara masa auren da ita saboda inya fahimci Dadyn sa bayaso yaji kunya ne idan aka fasa auren amma idan ya kawo wata za'a iya fasawa da wacce sai ayi da wacce yake so É—in,
Bossay yace masa "ai dady bazai taɓa yarda ba saboda yagaya masa tunfarko akwai wacce yake so yace masa saidai yabari idan akayi wannan sai yaƙara wani daga baya amma wannan ba fashi sai anyisa tunda shi yace yanaso tunfarko dan haka bai isa yace yafasa auren taba,
"Tofa Hamza yace yana kallon Bossay sundaɗe suna tattaunawa akan yanda zasu shawo kan al'amurin Dady ya yarda afasa auren, daga ƙarshe dai Hamza yace yabar masa komai ahannun fasa aure kamar anyi angama ne indai yana nan sai anfasa auren nan,
Sosai Bossay yashiga jin daɗi da murna harda rungume shi yana cewa nagode ƙaramin babana,
hararar sa Hamza yayi ya ture sa, yana cewa wallahi saima in fasa,
Dariya Bossay yayi, yana cewa yi haƙuri baba Hamza,
Nan sukai ta hirar su tare amma duk hirar nan maganar auren Ameesha bata zowa Bossay ba har yanzu, sallace kawai take tashin su daga hira, haka suka wuni har dare, bayan sunyi dinner a falo kowa da kowa aka ƙara dasa wata hira har wajen ƙarfe goma, sannan kowa ya tashi ya tafi makwancin sa,
*Washe gari*
Tun wajen ƙarfe goma suka gama shirya inda Hamza ya nemi izinin Dady akan zasu tafi da Bossay, da farko yaƙi amincewa amma sai Hamza yace gobe zai dawo ko jibi, saboda shi zai wakilci shi idan sukaje, da wanann dabarar suka shawo kansa ya amince,
Bakin Bossay har kunne Dady ya amince a tafi dashi, dan haka tare suka rangaya gaba ɗayan su wajen ƙarfe goma da rabi motar su ta ɗaga zuwa Gombe,
Basu suka sauka ba sai wajen ƙarfe shida na yamma suka sauka,
Suna shiga garin Gombe sakamakon magariba da ta kawo kai sai kawai Ayuba ya kaisu wani gidan bai kaisu cikin masarautar ba saboda wani dalili yace su bari sai zuwa gobe da safe sai su shiga,