Sashe 65
Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida komai yaƙara lafawa dan har ana shirin atashi daga zaman, Meer yace wa Abban Ameesha zai iya sanin prison ɗin da aka kai shi, da mutanen da suke zuwa gurin sa ko kuma babu wanda yake zargin zai iya aikata masa haka, ko agurin aikin nasu babu wanda suka taɓa samun saɓani dashi,
Nan yace masa shi babu wanda wani abun yataɓa haɗasu, kawai mugun tace amma babu abun da yayiwa kowa,
Nan Meer yace to zuwa gobe zai fara bincike dan bazai bari wannan binciken ya ɗaukar masa loƙaci ba dan inbai hukunta su ba zuciyar sa baza ta taɓa samun sukuni ba,
saida suka ɗan tattauna sosai akan yanda zasu ɓullowa lamarin sannan aka sallami kowa yakama gaban sa, saboda dare yayi sosai wajen ƙarfe shaɗaya,
Dadyn Rasheeda akace akaishi part ɗin baƙi saboda yanzu dare yayi, amma sai yace gida zai tafi da haka, tare da Bossay da Khalid suka tafi, idan su ka kai shi sai su wuce,
Abuu ne yace Abban Ameesha a part É—in sa zai zauna, daman kuma in ba nan É—in ba babu inda zai zauna a part É—in Maama, Meer yace ma su zauna a É—aki É—aya akace bazai yiyu ba gwanda kawai yaje ya zauna shima ana sa É—akin,
gaba ɗayan su a part ɗin Su Papa suka ƙara taruwa saida suka ci abinci sannan suka tashi kowa ya nufi makwancin sa yau ansamu har Meer akaci abinci, ba sabun ba yau sunci darajar Abban Ameesha, kafin kuma su tashi saida aka sanar da Abban Ameesha, auren da aka ɗaura tsakanin Meer da Ameesha, yaji daɗi kuwa dan ko basu haɗa ba shi da kansa sai ya haɗa dan yaron yagama yi masa, yasan idan ya aure ta zata samu kulawa(tabb jama'a Abban Ameesha baisan ɗayar kalar Meer ba, kallon ba ruwan sa yake masa)
Ameesha ce ta nace wai sai ta bishi sun kwanta tare amma sai Maama tace mata a'a ga É—akin mijin ta ina zata ta kwanta, kunya ma bata barta tabawa Maama amsa ba, shiyasa tayi shiru, dan a yanda aka gayawa Abban ta ba agaya masa basa so ba, shiyasa bata so tayi wani abu da zaisa ya fahimci bata so tunda taga yaji daÉ—in hakan tunda aka gaya masa yake ta faman murmushin jin daÉ—i.....,
Abuu da Ummy da Abban Ameesha sun ka miƙe zasu tafi, har sunkai bakin ƙofa Ameesha ta miƙe tace bari ta rakasu, Abban ta yace to ta taho amma
kyataho ke kaɗai dawowa fa wazai dawo dake kiyi zaman ki kawai, maƙe kafaɗa tayi tana turo baki tace ai zan iya dawowa abun da ko ina da mutane,
Maama ce tayi caraf tace"A'a baga wani É—an rakiyar ba tashi kuje sai ku dawo tare tunda ta nace sai tayi rakiyar,
Ba musu Meer ya miƙe yace "muje, tare suka fita ajere gwanin sha'awa Ameesha da Meer suna gefe gefen sa, sai su Abbu da Ummy a bayan su, haka suke tafiya har suka ƙarasa part ɗin dan saboda daman ba wata tafiya zuwa canɗin,
Saida suka kai Abban Ameesha har É—akin da zai kwanta sannan sukayi masa sallama, kamar kar su rabu haka suke ji dole suka barsa suka fito yana ta tsokanar su wai su kula da junan su kar wani abun yakama su kafin suje, bayan fitar su yakasa zaune yakasa tsaye, har yanzu ganin abubuwan da suke faruwa kamar mafarki kamar ba gaske ba,
Suna fitowa suka yiwa su Abuu sallama sannan suka fita, da sauri Ameesha tayi gaba ta saɓa tafiyar tasu dan bataso su haɗa hanya dashi, bare kuma su haɗa kafaɗa da kafaɗa suna tafiya tare, gashi haushin abun da yayi mata ɗazu take ji har yanzu,
Yana kallon ta yanda take ta faman sauri zuba mata ido kawai yayi yana ci gaba da tafiyar sa hankalin sa kwance,
tana ƙarasawa part ɗin ta tura ƙofar ta shiga tana shiga bata tsaya ko ina ba ta nufi ɗakin su, tura ƙofar tayi sai tajita arufe ƙwanƙwasawa ta shiga yi, amma bataji an amsa ba, sai ta fara kiran Dadda, Dadda Dadda Dadda ki buɗe mundawo nan ma dai shiru,
Tana cikin haka Maama ta fito daga nasu ɗakin, tace "ya akai ne kina ta bugu wataƙil tayi bacci kinsan tagaji yau da yawa saboda fitar da tayi ɗazu ga kuma abun da yafaru kinsan ta da baccin wuri yau kuma batayi ba shiyasa bata jiki ba, ya kamata ki rabu da ita kar kitashi ta kije ɗakin sa kawai kiyi kwanciyar ki inyaso gobe sai ki dawo,
Turo baki tayi kamar zatayi kuka tana shirin yin magana, Maama tace kinga wallahi kar ki sake ki tashe ta idan kuma bazakije ba sai ki kwana anan gurin kar kiƙara damun mu da bugun ƙofa kinga tafiya ta, tana faɗa mata haka tayi tafiyar ta,
Baƙin ciki kamar ya kashe Ameesha haka take ji, babu yanda ta iya dole ta haƙura da bugun, amma ta ƙudurci bazata kwana a ɗakin sa saidai ta kwana a falo,
tana juyowa tayi karo da Meer dake tsaye agun, duk maganar da sukai da akan kunnen sa, suna haÉ—a ido da ita ya wurga mata harara ya girgiza kai, bai gama janye idon sa ba, kawai yaga ta rama hararar da yayi mata harda murguÉ—a masa baki,
Zaro ido yayi yana kallon ta da mamaki, ita kuma sai tayi saurin canza fuska zuwa kalar dan batayi tunanin zai kamata tana ba, tayi tunanin yana hararar ta zai juya,
Girgiza kai yayi shikaɗai yasan me zaiyi mata dan haka sai ya rabu da ita a loƙacin ya juya ya tafi ɗakin sa,
Hamdalah tayi a zuciyar ta harda sakin murmushi jin daÉ—in baiyi mata komai ba,
Kan kujera tazo ta zauna sai kuma taƙaici ya kuma kamata yanzu duk ɗakunan gidan nan a falo zata kwana ita kaɗai ita da bata saba kwana ma ita kaɗai ba, anya kuwa zata iya, sai wata zuciyar tace to in baki kwana ba a ina zaki kwana, a fili kuma sai tace ai wallahi da dai in kwana aɗakin sa gwanda ingwammace na kwana anan ɗin,
kwashe fulillikan tayi daga kan kujerar da zata kwanta gashi abun taƙaicin lace ne ajikin ta kuma bata iya kwana da manyan kaya ba, haka ta kwanta ta ɗan rufe fuska ta da mayafin jikin ta, shima kuma ɗan yalolo ne baida kauri, bazai tare mata sanyin da take jiba,,
HaÉ—e jikinta tayi ta kwanta ahaka bata daÉ—e ba kuma bacci ya É—auke ta,
Meer da ya shiga wanka yayo yayi Sallah sannan ya saka kayan bacci, har ya hau kan gado ya kwan ta sai kuma ya tuna da ita, saukowa yayi ya fito wajen falon yana ganin yanda ta haÉ—e guri guda da alamun sanyi take ji daman kuma yasan hakan zata faru,
Aransa yana jinjina taurin kai irin nata yanzu tana ganin da ta shiga ta kwanta gwanda ta kwanta anan ko tsoro ma bataji, rasa me zai yi mata yayi yasan inma ya tashe ta ba shiga zatayi ba kuma ma baya son raini kar taga kamar ya damu da ita dan haka sai kawai ya fasa, dan mugun ta ma sai yaje ya kunna mata fanka sannan ya ƙure Ac yakaita har ƙarshe, sannan yayi tafiyar sa, harda ɓiye remote ɗin Ac,
Yana shiga ɗakin sa ya haye gado ya kashe ƙwai yayi kwanciyar sa,
Can cikin dare Ameesha ta farka sanyin yayi mata yawa har karkarwa take zaune ta tashi tana haÉ—e jikin guri É—aya sai kawai ta fashe da kuka,
Haka taita kuka babu me jinta bare yazo wajen ta...,
Yana cikin bacci ya ringajin kamar sautin kuka tun yana jin sa abun har yafara yi masa yawa, saboda kujerar da ta kwanta akusa da É—akin sa take, buÉ—e idon sa yayi still yaci gaba da jin kukan ashedai da gaske ne kukan da yake ji ba 'a mafarki bane,
Tsaki yaja kawai ya sauko dan yasan itace, cike da zafin rai ya fito zai sauke mata masifa, amma yana taka ƙafar sa a falon yaji wani irin sanyi ya ratsa masa jiki, shi kansa falon gaba ɗaya ya ɗau sanyi,
Yanda yaga ta takure tana ta kuka da karkarwa, sai kuma yaji tabasa tausay, tsigar jikin sa ce ta miƙe gaba ɗaya loƙaci ɗaya saboda sanyi da ya ratsa sa,
Gurin ta ya ƙara sa, saboda sanyin ma da yake ji bazai iya tsayawa a falon ba yayi mata magana sai kawai yajawo hannun ya miƙar da ita tsaye ya fara janta dan yasan idan yace ma zaiyi mata magana zata iya ɓata masa loƙaci,
yana shiga É—akin ya rufo tare da sakin ta, kukan taci gaba dayi, yadaka mata tsawa yace "malama kimin shiru ko kuma ki fita idan bazaki iya yi ba,
Shiru tayi saboda ta daddara yanzu ta zaɓi nan akan can saboda zazzaɓi har yafara rufe ta,
wardrobe ya buÉ—e ya É—auko wani bargo ya wulla mata yace gashi nan ki shinfiÉ—a,
kan gadon ya wuce kan gadon ya kwanta,
Jikinta na karkarwa ta ɗauka ta koma kan capet ta kwanta tare da lullaɓa abun bargon amma ina duk da haka bata daina jin sanyin ba saboda zazzaɓin da take ji, tana cikin bargon amma tana karkarwa bakin tane yafara fidda sautin kaf kaf kaf na jin sanyi,
Yana jiyo ta yayi mata banza da yayi biyar ya share ta amma sai yaji abun nata yayi yawa, fitowa yayi daga cikin bargon sa yana kallon ta ganin yayi kamar rawa take,
"Ke!!
shiru ba amsa haka yaita kiran ta amma bata iya amsa masa ba, tashi ya kuma yi yana jan tsaki yazo gurin da take, hannu yasa ya yaye bargon nan karkarwar tata ta kuma ƙaruwa,
hannu yakai ya taɓa jikin ta rau yaji zafin zazzaɓi me ƙarfi ajikin ta, a hankali ya furta ya salam, yana mamakin yanda akai zazzaɓi ya rufeta haka loƙaci guda,
Hannu yasa duka biyun ya ɗagota zaune amma sai ta kasa zama saboda yanda jikin ta yaci gaba da ɓari,
Tausayi ta bashi baiyi zaton hakan dayayi zai cutar da ita har haka ba, da bai kunna mata ba,