← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 103

Sashe 13

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai taji daɗin kala mansa  ta fara jinsa aran ta, cikin kuka tashiga karkaɗa masa kai tace, dan Allah kabarni kawai ka rabu da ita nayi alƙawarin bazan ƙara zuwa inda take ba tunda har bata buƙatar gani na, Ni yanzu hakama bansan inda take ba dan haka mubar maganar kawai yanzu kakaini gidan mu zanci gaba da rayuwa ta kamar yanda nake ada nagode da taimakon ka agareni, tunda nake bantaɓa haɗuwa da wanda ya kula dani ba kamar kai uwar sa ta tsugunna ma ta haifeni ta tafi ta barni amma kai ka tsaya ka kula dani, a loƙacin da nake buƙatar hakan, Nagode Nagode Nagode....,

Hannu ya ɗaga ya dakatar da ita yace "kiyi shiru kawai ya isa haka  maƙarasa maganar anjima ni yanzu zan fita, ki kwanta zanje na dawo, yana kaiwa nan ya miƙe tsaye, itama tsanyen ta tashi tasha gabansa da sauri, tace dan Allah ka mayar dani gidan bazan iya zama anan ba ina son ganin mahaifina,

kallon ta ya tsaya yi saida ta gama sannan yace "nace miki ba yanzu ba kiyi abun da nace miki kawai ina dawowa, ja da baya tayi ƙwalla naƙara cika mata, saboda ba haka taso ba so take kawai ta ganta agidan su,

Baibi takan taba yayi gaba saboda bayaso tagane gazawar sa dan labarin ta baƙaramin dakar sa yayi ba, ya taɓa masa zuciya sosai, kuma aransa yayi alƙawarin daga rana irin tayau bazata ƙara kukan wani abun ta rasa ba, sai yazame mata gatan ta, babu inda zata ƙara zuwa batare dashi ba, duk inda take zai kasance da ita yabata kulawa fiye da tunanin me tunani...... A haka ya fice daga ɗakin cike da tunane tunane.......,

          ************************

_________MeeshMeer

  Batare da Meer ya kalli Ameesha ba  yace "gaya min me yake faruwa ke kika turon video awayata ba,

Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke jin maganar da yayi daman tarasa ta inda zata fara yi masa bayani ashe ya gani ko shiyasa yayi mata shiru duk abun da take masa bai hukun tataba,

"Magana nake miki...,

Ta ƙara jin maganar sa ta dake ta da sauri ta dawo da dubanta gare sa tare da gyara zama, saida ta tattaro nutsuwarta gaba ɗaya ta nutsu sosai sannan ta shiga basa labarin duk abun da yafaru, loƙacin da sukaje kiransa suka tarar da abun da kuma ɗaukar da sukayi har suka zo ɗakin sa suka tura masa,

Tana gama basa labarin duk wani abun da yafaru ya shiga dawo masa akai atake agun ya tuna komai,

Dafe kansa yayi yana girgiza kai sannan yana jinjina irin wannan lamarin nasu, ashe yanda yake É—aukar abun yafi haka,

"Suna dayawa kenan?
yafaɗa afili tare da ɗagowa yana kallon Ameesha, itama da shiɗin take kallo, kai ta ɗaga nasa, sannan tace yanzu ya kake ganin za ayi, maiye mafita dan nifa wallahi mutanen nan sun fara ban tsoro kodai mu sanar da su maama kar suje batare da kowa yasani ba su ƙara yi mana wani abun musamman ma idan sukaji munɗauki muryoyin su, baza su barmu ba,

Jinjina kai yayi, yace "babu abun da suka isa suyi, amma dai kar kuƙara fita daga part ɗin har sai nace ku fita daga ke har ita ɗin, yanzu ki tashi kije zan nemeku gobe, kafin wannan binciken inason inyi wani binciken ne dan wannan nagama dashi  komai yazo ƙarshe tunda aka samu hujjoji basu da wani abu da zasu iyayi,

sannan kuma koda sun nemi da ku basu memoryn ku basu har wayar ma, amma kafin nan kikawo min wayar zanyi wani abu da ita inbaku,

Cike da gamsuwa da maganar sa tace to shikenan yanzu inje in kawo maka wayar ko itama sai a'a yanzu zaki kawo min,

Tashi tayi da sauri tace "Tom bari inkaɓo ta, tana faɗa bata jira amsar sa ba ta fita daga ɗakin cikin sauri,

Bayan ta fita ba daɗewa ta dawo da wayar a hannun ta, gabanshi tazo ta miƙa masa sannan ta koma inda ta tashi ta zauna,

Daddana wayar ya shiga yi sannan yace ta dauko memoryn inda suka ɓiye nan ma dai tashi tayi ta duba inda suka ajiye ta ɗauko ta bashi, yana karɓa yasaka awayar yagama danne dannen sa sannan ya miƙa mata wayar yace zaku iya fitama duk sanda kuka ga dama sannan inaso anjima da daddare zansa wani daga cikin ƴan gidan nan zai fita daku zaku karɓo min saƙo awani waje idan kun fita zan gaya masa inda zakuje,  kuma baku biyu ba har sauran yaran nan twins kuje ku taho dashi kuma banason kowa yasan da fitarku karkigayawa kowa ma zaku fita kawai kisan yanda zakiyi kifito dasu har gurin motar cikin dabara batare da wani yaji zaku fita ba kin gane?

"Eh tace masa, amma ina zamu baka ganin zasu iya binmu karfa su sa a kashe  mu, nidai wallahi tsoro nake ji,

Taƙasan ido yake binta da kallo sannan ya girgiza kai, yace "banason shashanci ke kaɗai ce dazasu kashe ki kuma taya ma za ayi su san da fitar ku saidai idan faɗawa wani kikayi, amma in ba hakaba babu wani abu ni banason fitane kuma saƙon yana da muhimmanci ne daga yamen aka kawo min bazai yiyu in aiki wani bare ba daban za a iya samun matsala, shiyasa na aike ku, kuje kawai kiyi addu'a babu abun da zai faru,

Itadai har ga Allah batayi na'am da fitar nan yau ba kuma yauÉ—in ma da daddare dama zai bari sai zuwa gobe da safe ido na ganin ido yanda duk ma wanda yabi bayansu zasu gansa ta cikin ido amma ya za 'ayi yanda a kasan sunsan komai É—in nan kuma yace su fita sukaÉ—ai,

A fili kuma sai tace masa to shikenan Allah ya kaimu anjiman, zan iya tafiya, ɗaga mata kai yayi kawai loƙacin wayar sa tana hannun sa yana daddan nawa,

Miƙewa tayi idon ta yana kansa, ji take kamar tace masa dan Allah yayi haƙuri basai sun fita amma tana jin tsoron kar ya fusata ya mammagare ta tasan kaɗan daga cikin aikin sa kenan,

Ganin yana shirin É—agowa yasa tayi saurin É—auke idon ta akan sa ta juya ta fice daga É—akin, bin bayanta yayi da kallo yana girgiza kai, sannan ya jawo laptop É—insa ya buÉ—eta yafara aiki......,

_____Waziri ne tsaye a cikin É—akin sa yana ya kaiwa da kawowa yayin da matar sa ke zaune kan gado itama ta zabga tagumi,

Miƙewa tsaye tayi ta taka taje gaban sa, sannan tace "Wai har yanzu ka kasa samo mana mafita, idan fa muka bari waɗannan yaran suka nuna videon nan akwai fa matsala yakamata muyi gaggawar katse su ayau ɗin nan duk wata hanya da zatasa su nuna videon nan mubi mu tosheta kafin wankin hula yakaimu rana, dankwa duk wanda yagani bamu da bakin kare kanmu tunda mune kuma muryoyin mune, amma kai yakake gani,

Shiru yayi bai bata amsaba sai daga bisani ya ɗan numfasa tare da furzar da iska mai ɗumi daga bakin sa, yace "Anzo wajen Anzo wajen dole kowa yayi ta kansa ɗan ƙaramin zaki ya girma, ko ince ƙananun zakuna sungirma, indai har abun da shu'aibu yafaɗa gaskiya ne abun da yace sunfaɗa ɗin to bamu da hanyar da zamu kuɓutar da wannan videon da suka ɗauka, tunda suka ɗauka dole sai sun fallasa sa, amma dai zamuyi ƙoƙarin karɓe wayar tasu wannan aikin kine kisaka adaren nan a ɗauko mana yaran idan muka tsorata su zasu faɗi inda yake zasu bamu,

Cike da zaro idanu tana rarrabasu tace "bangane maganar ka ba kana nufin dole sai ansan da videon nan to ya kake so inyi da rayuwa ta kuma shikenan burinmu bazai cika ba ko mai kake so kace min, ko kana ganin idan videon ya fita, za'a rabu damu baranta na har mucika burin mu na shekara da shekaru da muka ɗauka muna ɓata loƙacin mu,

Bakin gado ya samu ya zauna yace "kusan hakan amma dai da yardar Allah ma hakan bazata faruba, saidai rashin faruwar sa ne abun da kamar wuya,

Itama cike da ɓacin rai ta ƙaraso gaban sa tace mai kake nufi mai yasa kace haka, mai yasa baza ku koma gurin boka mai yi ba, ya kamata kuje a ƙara rufe bakin kowa mana ta yanda koda anga videon ba wanda zai yarda,

Miƙewa yayi yana kallon ta ido cikin ido yace kinga karfa ki nemi ki ƙara ɗaga min hankali ki barni da iya wanda nake ciki, bari in gaya miki abun da baki sani ba, a yanzu duk wani aikin mu da ƙulle ƙulle mu baza suyi aiki ba domin tun farkon aikin da aka ƙulla sa boka ya sanar damu cewa, indai har yayi aiki tabbas matar zata bar gidan zatayi nesa damu, sannan bazata ƙara dawowa hayyacin taba har abada, indai munyi yanda ake so, muka yarda akaiyi komai to amma inda matsalar take shine yace duk yanda zamuyi muyi kar musake mubar ƴaƴan ta araye adoron duniya idan kwa ba haka ba, ko ba daɗe ko bajima zata dawo cikin hayyacin ta da zarar jinin ta ya taka ƙafar sa acikin gidan nan to duk wani asiri sai ya warware kuma bazai ƙara ƙulluwa ba, kuma itama zata dawo cikin hayyacin ta sannan zata dawo cikin gidan, kuma gashi kinga komai ya faru yanda yace ɗin aranar da yarinyar nan ta shigo gidan nan tun aranar komai ya kunce,

Yanzu ba aikin boka bane zaiyi aiki saidai mu shirya mu sake ɗaure damtse gurin ganin cikar burin mu ya cika, yanzu hankalin kowa a tashe yake tun ranar da yarinyar nan ta shigo gidan komai ya fara canzawa, ƙungiya har sawa tayi a fita da yarinyar akashe ta amma sai gashi ta dawo, muddun muna son cikar burin mu saidai muyi dabarar da zamuyi mu kawar da su yaron da yarinyar domin sune kan gaba idan babu su burin mu zai iya cika idan kwa suna raye bazamu taɓa cika burin mu ba kuma asirin mu zai iya tonuwa, idan kwa nawa ya tonu wlh sai na tonawa kowa asiri dan bazanyi asara ba nikaɗai, dole kowa ya fito,
Chapter 13 · 0% Book details