← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 103

Sashe 28

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama cikin wata iriyar murya kamar zatayi kuka tace wannan ne wasa, daga yi maka magana sai ka kamani da faɗa da masifa kace nadaina takura maka kar nasake takura ma, amma yanzu shine zakace wai wasa, wasa to ni naji bansan shiba, haƙuri kuma shine kamayar dani gidan mu,

buɗar bakin sa sai cewa yayi "ai kina da ƙafa ƙofa abuɗe take kije duk inda zaki,

Tab maganar sa kam ba ƙaramin dukan  zuciyar ta yayi ba bata taɓa tunanin haka daga gare saba,saukar maganar sa adodon kunnen ta kamar saukar aradu haka tajita aranta, a take taji wata zazzafar ƙwalla tazo mata shikenan shima ya juya mata baya yanzu kuma ina zata dosa,

Shi kuma yana sane ya faÉ—a mata haka dan yaga tana son tafiyar ko bata so, yana faÉ—a mata haka kuma yasake ta,

Miƙewa tsaye tayi ta nufi ɗakin sa ya ɗauko hijabi ta saka ta fito zuciyar ta cike da rauni dan jikin ta har sanyi yayi ta dawo bata da kuzari haka ta fito daga iya sai hijabin ko kallon inda yake batayi ba, ta nufi hanyar fita yayin da idanuwan ta suka kawo ƙwalla duk son ruƙe sun datake so tayi amma hakan ya gagara saida suka shiga saukowa kan kumatun ta,

Murmushi Sam yasaki yana miƙewa tsaye tana zuwa daidai tsakiyar falon,  yayi saurin shan gabanta,

cak ta tsaya tare da jin wani irin daɗi aranta tayi tunanin bazai dakatar da ita ba amma a fili sai ta basar bazaka gane taji daɗin hakan ba, saima ƙara haɗe ran da tayi sai kuma taji kunyar zubowar da ƙwalla tayi mata akan fuska,

matsawa ta ƙarayi zata tafi yaƙara tare ta, kuma yaƙi magana, saida yagama karantar ta sannan yace "kiyi haƙuri da wasa nake miki koma ki zauna,

Ƙin yarda tayi tana ƙara yin gefe zata tafi, nan ma yatare ta, nan suka ringayi nan ta sakar masa kuka tace ni kamatsa min in tafi ko kana so kace duk maganar ka wasace yanzu ma wasanne idan na ɗazu na yarda wasane amma na yanzu bazan taɓa yarda ba babu abun da zai ƙara zaunar dani abun da kayi min nagode,

Sam gani yayi daga wasa abu yana neman zama gaskiya saboda ta tubure masa abunnata har yama fi na farko,

Tsaye yayi yana tunani kawai ta gota ta gefen sa zata fita yasa hannu ya dawo da ita gaba tare da rungume ta,

zai fara yi mata magana kenan aka turo ƙofar falon a tunanin sa Hamza ne shiyasa bai damu ba, yaci gaba da rungume ta har da mara riƙeta gam,

Ƙararar zubewar abu yaji kafin ya juyo ma ya tsinkayo muryar momma tana cewa Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un da sauri Sam yasake ta, yana juyowa a tsorace karaf idon sa ya faɗa cikin na momma daram daram yaji gabansa yafaɗi da sauri yayi ƙasa da idon sa.....,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

     
       'Ƙarar zubewar abu yaji kafin ya juyo ma ya tsinkayo muryar momma tana cewa Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un da sauri Sam yasake ta, yana juyowa a tsorace karaf idon sa ya faɗa cikin na momma daram daram yaji gabansa yafaɗi da sauri yayi ƙasa da idon sa.....,

Sumayya kam wani abu taji ya taso mata kunya da taƙaici gaba ɗaya suka haɗar mata, ji take kamar ya nutse agun, adaidai bayan sa ta tsaya ta ɓuya ta yanda momma bazata ganta ba,

Momma da jikin ta gaba ɗaya ya ɗauk kyar ma ta ɗaga hannnu cikin rarraba murya da kamar anriƙe mata ita ta ciki, tace "sa...sa meer, ina lillahi wa'inna ilaihi raji'un mai nake gani sameer mace mace mace fa nake gani kodai ido nane, wacece ita?

Shiru yayi mata ya sunkuyar da kansa saboda wata iriyar kunya da yaji ta kamasa ga baisan amsar da zai bata ba,

"Ba magana nake maka ba! ta ƙara yi masa magana cike da daka masa tsawa, da shi kansa baisan yaushe ta iya ta ba dan baitaɓa ma jin tayi ta ba,

Takowa tayi tazo har gaban sa, tace daman irin tarbiyar da nabaka kenan ko halin da kake yi ne acan ƙasar yau yadawo nan, nanɗin ma har cikin gida saboda baka da kunya baka da mutunci, shiyasa ka maida mutane ƴan iska idan anyi maka maganar aure kace kai ba yanzu ba ashe da abun da kakeyi, gwanda da Allah ya nuna min da idona da wanine yagaya min da bazan yarda ba, ashe sumumu kasum ne mai fuska biyu, waje Musa ciki fir'auna, wallahi kaban mamaki mace aɗakin ka waya san ma tun yaushe kake aikata, saboda tsabar rashin mutunci da rashin kunya duk waje baiyi maka ba sai ka shigo da ita to kayi daidai nace kayi daidai, sai ka ɗauke ta kubar cikin gidan sai ka kaita duk inda zaka kaita kaje kaci gaba daga inda ka tsaya daga yau bani bakai ka tattara inaka inaka kabar gidan nan tun muna shaida juna kafin inɗauki mummunan mataki akan ku,

Gabansa ne ya tsanan ta faɗuwa bama shi kaɗai ba har sumayya saida taji maganganun momma kamar alburushi jin tsatstsaursn matakin da aka ɗauka akansa alhalin ba haka yake ba kuma tasan duk itace taja masa badan itaba da duk hakan bata faruba da batayi masa gardama ba tace zata tafi da hakan bata faru ba saboda tasan da wasa yake kawai jan magana ne yasata hakan sai gashi ta jawo musu babban aiki, tana so tayi magana amma ganin yanda ran mahaifiyar tasa ya ɓaci yasa tajin tsoron yin magana,

Da sauri Sam yaƙarasa gaban ta ya tsugunna yace momma wallahi ba abun da kike tunani bane ban taɓa aikata komai ba, daman ina taso inyi miki bayani akanta kiyi haƙuri ki saurare.......,

Tsawa ta kuma daka masa tace "rufamin baki anan ko nayi maka illa anan gurin katashi ka ɓace min dagani kajata kufita daga gurin nan, yanzun nan kufita daga nan, wallahi sai kabar gidan na koreka na cireka daga cikin ƴaƴana bana son na ƙara ganin ka,

kamar zaiyi kuka ya miƙe tsaye gaban sa na wani irin bugu, ya shiga tashin hankalin da bai taɓa shiga ba dan yaga momma ta ɗau zafi da yawa,

Cikin marairai cewa yace "dan girman Allah momma ki tsaya ki saurare ni, ni bahaka nake ba ba halina bane ke kanki shaida ce da ace halina ne da tuntuni kin daɗe da sani shekarata nawa amma baki taɓa ganin da mace ba, wallahi ko hannun wata macen bantaɓa riƙewa ba bayan ita itama kuma da dalili bawai hakan nan ba ki tsaya inyi miki bayani kar kiyi saurin yanke min hukun cikin fushi, momma dan Allah yafaɗa yana ƙoƙarin riƙo hannun ta atunanin sa ko zata haƙura amma sai taƙara janye wa tana binsa da wani irin kallo da bai gane masa ba,

Duk wannan abun da yake gaya mata amma taƙi sauraron sa ta dage akan sai yabar gidan kuma yanzu da tace ya haɗa kayansa ma amma yanzu tace daga nan inda yake sai waje babu abun da zai ɗauka ya su fice,

Sam yayi iyaka bakin ƙoƙarin sa amma abun yaci tura tun yana bata haƙuri har abun yafara ƙona masa rai akan meyasa bazata tsaya ta saurare sa ba maiyasa zata koresa sai kace wanda takama yana zina, shiru yayi mata yadaina bata haƙurin kuma yaƙi fita yana tsaye ƙam yaƙi motsawa kawai ya zuba mata ido,

Sumy kanta aƙasa ƙwalla cike da idon ta, tace "dan Allah kiyi haƙuri bashi da laifi karki koreshi Wallahi taimakona yayi,

Wata tsawar momma ta buga mata tare da doka mata wata uwar harara kamar zata faɗo da idon, sannan tace "dalla malama rufe min baki ko nasaka dake, banza kawai wallahi idan baku fitaba daga ke har shi babu wanda zan ƙyale sai kinyi da na sanin zuwan ki cikin gidan nan ballagaza marar kamun kai,

Wasu zafafan hawaye ne suka taho mata dan kalmar ba ƙaramin ciwo tayi mata, tun tana iya hawaye har ta fara mai sauti, cikin kuka tace kiyi haƙuri koma mai kika faɗa daidai ne nice da laifi amma kisani ni bandace da sunan da kika kirani dashi ba ni ba ballagaza bace, kuma yanzu zan tafi bazan ƙara dawowa inda yake ba, na miki alƙawari , amma dan Allah kar ki koreshi, kitsaya ki saurare sa sam abun da kike tunani ba haka bane, idan natafi zaimiki bayani, tana gama faɗar haka tabi ta gefe zata wuce Sam yayi saurin riƙo hannun ta,

ÆŠagowa tayi ta kalle sa da idanun ta duk da suka jike da hawaye, sai taga ba ita yake kallo ba idon sa ma baya kanta,
hannunta da ya riƙe ta kalla, taga yanda ya damƙe nata hannun tayi ƙoƙarin ƙwacewa amma yaƙi saki,

Momma idanun ta kamar zasu faɗo gurin kallon hannuwansu yanda ya riƙeta, ji tayi ranta yaƙara ɓaci wato zai nuna mata abun yafi yanda take tunani,

Kallon sa tayi tana girgiza kai itama idon tane ya cika da ƙwalla amma sai tayi saurin mayar da ita, ta ɗago ta kalle sa sannan ta saki murmushin yaƙe mai ciwo tace "yayi kyau hakan ai ba komai bane awajen ka, mutumin da baya tsoron Allah wa kuma zaiji tsoro aduniyar nan,
Chapter 28 · 0% Book details