← Book details Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 103

Sashe 70

Sarki Sameer Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ya dawo suka ce masa, daga nan ya É—auki wata siririyar hanya, ya nusa cikin dajin inda gidan sa yake.....,

Suma zama sukayi suna ci gaba da tattaunawa akan abun da ta faru da taya da taya tsohon da addu'ar Allah ya kawo masa É—auki yabar cikin dajin nan, ya dawo ya cigaba da rayuwa kamar kowa.......,

__________Meer cike da taƙai ci yake tafiya yana tafiya yana faman sakin tsaki ba adadi, amma kuma wani ɓangare na zuciyar sa yakasa yarda da gaske mutumin baya gurin, koma dai meye tunda yaga inda yayi, zai ƙara komawa ko kuma zaisa asaka masa ido agun, indai tana gurin dole wataran za agansa koda wucewa ne za agansa,

A haka ya ƙarasa gida koda ya shiga gida bai bari kowa ya gansa ba, inda Allah ya taimake sa loƙacin da ya shiga falon babu kowa sai kawai ya shige ɗakin sa tare da saka muƙulli ya ƙulle ƙofar.......,

Agurguje..........✍️

      *BAYAN KWANA BIYAR....*

........acikin kwana biyar ɗinnan har yau Meer da Ameesha basu ƙara haɗuwa ba, duk inda yasan zata haɗu dashi bata bari su haɗu daɗin daɗawar ma har anfara jarrabawar inda aka fara dasu yau kwana uku ma, tun safe suke fita idan kuma suka dawo anayi musu lesson agida da yamma kuma su tafi isalamiya, dan tun a washegarin ranar da suka tattauna, aka shirya komai ta koma isalamiya boko kuma tasaka kayan su Amra suka fara jarrabawar WAEC,

shima kuma haka saboda kwana biyu ko zaman gidan ma bayayi, acikin kwanakin har Gombe suka je inda sukayi bincike agidan da aka ajiye Abban Ameesha basu samu wata shaida ba, yaran kuma Ayuba suma anneme su anrasa andai ga gawar mutum É—aya, sauran kuma ba asan inda suke ba...,

Dole suka dawo suka ci gaba da binciken anan, mutumin kuma sa su Sam suka ɗauko a Abuja shima an kuma fito dashi ankarɓi number mutumin da yake kiran sa, an ƙara mayar dashi,

Sam kuma yabawa Meer sauran binciken da suka fara, harda wayar da dadda ta basu da wayar baban sumayya da suka karɓa, har wayar Ayuba da ya buƙace da su bashi, itama sun bashi duk da ta farfashe amma ya karɓa da haka...,

....A ɓangaren Ayuba kuma ya farfaɗo saidai kuma kwata kwata baya magana, da yayi yunƙurin yin maganar sai tari ya sarƙe sa, saidai suyi masa allura ya ƙara komawa bacci,

acikin kwanakin can garin nasu shima ansan komai maganar taje musu, inda har Dadyn Bossay da Hamza suka kuma shiryawa, har da Ibrahim ƙanin Papa, Papa ne yace yaje ya wakil ce sa, sunje kuma sun samu wacce Ammah ta gaya musu anje an karɓi duk wasu shaida, abun ya zo musu da sauƙi suna zuwa masarautar suka faɗi komai babu wanda ya tada husuma ko neman tada tanzoma, saboda wasun su daman duk sunsan gaskiya kawai dai babu wanda ya fito ya iya magana,

Dan haka suna faɗar abun da ya kawo su akace za asauka abasu kujerar su, Amma sai Dady yace su bari dai sai sun ƙara shiryawa, sannan zasu dawo sai aƙara yin komai a nutse, yanzun saboda abun da yafaru ne yasa suka zo sukayi musu bayani.....,

_____A ɓangaren Dadyn Rasheeda, aure babu fashi duk da halin da yake ciki ta wani fanni amma hakan baisa ya janye maganar auren ba, domin gida har yafara cika da mutane sosai ƴan biki dan kuwa gobe ma ɗaurin aure, Rasheeda ma zuwa yanzu ta haƙura zata aure sa, saboda wayon da dady yayi musu, nacewa ai baban Bossay shima ɗan sarki ne, dan haka idan ta aure sa mijin ta Bossay nan gaba shine sarki, shi kuma Meer da take cewa shi take so anriga anyi masa aure kuma koda ta shiga gidan baza taji daɗin zaman gidan ba saboda da ƴar uwar sa ce komai zaiyi sai ya fara yiwa waccen musamman ita da baya sonta,

loƙacin da taji labari kuwa tasha kuka sosai , saidaga baya ta haƙura ta yarda zata auri Bossay saboda ita bata son kishiya da ta auri wanda yake da mata gwanda ta fasa auren, amma kunya ta hanata kiran Bossay tabari kawai idan anyi auren zata basa haƙuri ta shawo kansa,

Yanzu hakama ana can cikin ƙawaye ana ta shirye shiryen tafiya dinner, duk zumuɗin bikin da cewa za'ayi sati ana shirye shiryen sai gashi ba'ayi ko ɗaya ba, Dady ya hana, itama kuma daman ta janye saboda bataso duk ayi Bossay yaƙi zuwa ƙawayen ta suyi mata dariya shiyasa tace musu duk ta fasa, dinner kaɗai za ayi sai ɗaurin aure,

_____A ɓangaren Bossay kam yana ɗaki a kwance babu lafiya saboda baya son auren hasalima babu wanda yagawa maganar auren wayoyin sa ma kuma duk ya kashe su, dan baya farin ciki da auren, Hamza ma yayi iya bakin ƙoƙarin sa wajen ganin anfasa auren amma abun yaci tura Dady ya kafe yace sai anyi, shiyasa shima Hamza ya ɗauke ƙafa ko gidan ma baya zuwa, saidai wataran su haɗu a asibitin wajen Ayuba,

Dan haka su kaɗai suke shirye shiryen su ko gidan ja shigo babu wasu mutane sosai, dan Ammi ma idan ta tashi sanar da maganar auren sai tace iya ɗaurin aure za'ayi shima kuma ba wani abu za ayiba ana ɗaurawa za akai amarya, to shiyasa ma gidan yakasan ce babu wasu mutane sosai, wasu duk sai zuwa gobe zasu ƙaraso....,

Amma dai can cikin masarauta ansan da maganar ƙarewa ma anan Papa yace ma za' a ɗaura auren a masallaci gurin,

Duk da sanin kuma sa akayi manyan ne kawai suka sani, labari bai isa kunnen Ameesha ba, shima kuma Bossay har yanzu baiji labarin auren Ameesha ba, da abun sai yafi masa illah,

yau da yamma Abban Ameesha yace Meer yazo ya kaishi yaƙara dubo jikin Ayuba,

Har sun shirya zasu sai su Ummy da Dadda Da Maama suma suka ce zasu je su dabasa, tun ranar farko basu ƙara komawa ba,

Koda sukaje yana bacci,haka suka gama zaman su, suna shirin fita kuma,
sai ga Dadyn Bossay da Dadyn Rasheeda sun shigo, komawa sukayi suka gaisa, suna cikin gaisawa kuma Ayuba ya farka,

yana farkawa idon sa ya sauka akan Dadyn Rasheeda, kamar zai faɗo haka ya yunƙura zai tashi sukayi saurin yin kansa Dady yamayar da shi ta kwantar,

Gaba É—ayan suka shiga yi masa sannu, amma baya jin na kowa idon sa da hankalin sa gaba É—aya yana kan Dadyn Rasheeda, shi kuma inbanda kallon gargarÉ—i da yake binsa dashi,

Ayuba yana so ya buɗi bakin sa amma yakasa ga maganar abakin sa amma ta maƙale,

Kawai hawaye suka ga yana saukowa daga cikin idon sa, duk babu wanda baiyi mamakin ba, sun matuƙar tausaya masa dan atunanin su wani zafin ciwon ne ya tayar masa,

Abban Ameesha ne ya kalli Meer da yayi zaune acan gefe yana daddana wayar sa, tace "ko zaka kirawo likita yazo ya kuma duba sa, kamar da matsala, kayi sauri yayi maganar yana ƙara matsawa kusa da Ayuba yana yi masa sannu, da basa haƙuri, dan gani yake duk kamar shi yaja masa, yana matuƙar tausayin sa, musamman ma idan ya tuna ta dalilin sa ya haɗu da iyayen sa, nadan shi ba da tuni har yanzu yana can cikin wani irin hali, shiyasa yafi kowa jin wannan rashin lafiyar da yake ciki,

Da sauri Ayuba ya shiga girgiza kai tare da ɗago hannun sa da ƙyar ya shiga nuna inda Dadyn Rasheeda yake da tunkan hankalin su ya koma kansa Dadyn Rasheeda yayi saurin matsawa daga inda yake, duk da kallo suka shiga bin inda yake kallo amma basu fahimci komai, dake Meer yana nesa dasu kaf abun da ya faru akan idon sa, yaga loƙacin da Dadyn ya matsa daga inda Ayuba ya nuna sa kuma yaga idon Ayuba a inda ya sauka,

Dadda ce tace "Allah sarki gaskiya yana jin jiki kuma kamar da abun da yake son cewa naga yana É—aga hannu,

Dadyn Bossay yace haka yake kullum muka shigo haka yake yi, daman ance ko ya tashi ba lalle kwakwalwar sa ta dawo daidai ba saboda buguwar da yayi,

Nan duk suka shiga tausaya masa suna ƙara yi masa sannu,

Ayuba yana so yayi kwana da hannun sa amma bazai iya ba, saboda dadyn Rasheeda gefe ya koma inda yasan bazai iya nuna saba,

Babu yanda ya iya haka ga haƙura sa nunasan da yake abun da yafi yimasa ciwo a zuciya kenan, kasa maganar da yayi,

sun daÉ—e sosai sannan su Maama suka ce zasu tafi, sai Abban Ameesha yace yau abarshi zai kwana dashi,

Da farko su Maama basu yarda ba, suka ce ai akwai masu kuka dashi ba a kwana a asibitin,

Dadyn Rasheeda yace Allah sarki ku rabu da shi mana yau É—aya dai kunsan shi ya taimake sa shiyasa yake son shima ya taimaka masa, asibitin duk na gida ne ai, babu komai idan ya kwana, zai taimaka masa sosai,

"To shikenan gaskiya ce maganar ka, ka zauna É—in tare dashi, tunda akayi maganar Ayuba yake faman girgiza kai nufin shi kar ya zauna ya tafi amma babu wanda ya gane hakan,

Nan suka fita suka barsu sai Dadyn Rasheeda ma yace ai daman suma tafiya zasuyi, sai gobe zasu dawo, tunda dare ya riga yayi,

ÆŠaki ya rage daga Ayuba sai Abban Ameesha,

Dadyn Rasheeda da Dadyn Bossay suna fita suma kowa ya shiga motar sa, suka tafi, amma sunayin nisa dake ba hanya É—aya zasuyi ba sai kawai Dadyn Bossay ya yanko kwana ya juyo, daman shirin shi kenan idan kowa ya tafi yadawo ya haÉ—a da Abban Ameesha da Ayuban yakawar dasu, dan ya fahimci Ayuba nason tona masa asiri, shiyasa kafin ya samu lafiya ya tona masa gwanda yayi gaggawar kawar da su gaba É—ayan su,

Tun yana kan hanya yagama shirya duk yanda zaiyi ya kashe su gaba ɗayan su ta hanya me sauƙi batare da kowa yagane,

______Gudu Meer game dasu kamar zai tashi sama da har saida Maama tayi masa magana akan lafiya yake irin wannan gudun sai yace mata bafiya ba tayi tayi kuma yagaya mata me yake faru amma yace zai gaya mata ba yanzu ba,
Chapter 70 · 0% Book details